Wednesday 25 September 2019

Hanya Mafi Sauki da Zaku yi Nasara Wajen Hana Banki Cazar Muku Kudi a duk Lokacin da Zaku Fitar da Kudi

Tura Wannan Zuwa Ga
Daga yau Laraba bisa umarnin babban bankin Ƙasa wato CBN, bankunan kasuwanci irin su First Bank da GTBank da Zanith Bank da makamantansu za su fara cazar kwastomomin su adadin wani kaso daga cikin kuɗin da za su ajiye ko kuma za su fitar daga asusunsu, matuƙar dai wannan kuɗi ya kai N500,000 (dubu 500) ga kwastoma ɗaya, ko kuma N3,000,000 (miliyan 3) ga kamfanunnuka da manyan ma'aikatu.

Sabon Tsarin CBN

Marubuci: Na 'Yar Talla

Yadda tsarin yake, idan kaje da niyyar saka N500,000 a cikin asusun ka dole ne bankin zai cajeka kaso 3 na adadin wannan kuɗin, wanda wannan kaso ukun shi ne ya kama N15,000 (dubu 15). Kenan maimakon a baka N500,000 idan kazo cira, sai dai a baka N485,000. Amma idan kana da ragowar kuɗi a asusun sai a cira a cikin su a baka kuɗinka cikakke. Idan kuma ya kasance sanyawa kazo yi a cikin asusun ka bankin zai cajeka kaso 2 na wannan kuɗin, wanda ya kama N10,000. Kenan anan ma ba N500,000 za a sanya maka ba, N490,000 za a sanya maka.

Ga kamfanunnuka da manyan ma'aikatu kuwa, a duk N3,000,000 (miliyan 3) da za su sanya a asusun su banki zai ciri kaso 5, wanda ya kama N150,000 (dubu 100 da 50). Idan kuma cirewa za suyi, bankin zai ciri kaso 3, wanda shi ma ya kama N90,000 (dubu 90).

KARANTA WANNAN: Ya Rasu Jim Kadan Bayan Ya Sanar Da Rasuwar 'Yar Uwarsa

Kuma wannan dokar za ta fara ne a Jahohi 6 kawai, kafin daga bisani zuwa watan Maris ɗin shekarar 2020 tsarin ya karaɗe dukkan jahohin Ƙasar.

Jahohin sune; Lagos da Ogun da Kano da Abia da Anambra da kuma Rivers.

Dan haka a shawarce, ga wanda ba ya son a taɓa masa kuɗi yana iya raba kuɗin gida biyu, in yaso yau ya kai rabi, gobe sai ya kai rabin. Haka ma kuma in karɓa zai yi, sai ya raba karɓar gida biyu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user