Tuesday 1 October 2019

SHIN DA GASKE NE NIGERIA TA KUBUTA DAGA MULKIN MALLAKA?

Tura Wannan Zuwa
Yau Talata 1-10-2019 Kasar mu Nigeria ta cika shekaru 59 da samun 'yancin kai a shekarar 1960 daga turawan Mulkin Mallaka.

Ranar Samun 'Yancin Kan Nigeria daga Turawan Mulkin Mallaka

MarubuciDatti Assalafy

Ina amfani da wannan damar wajen taya 'yan uwana 'yan Nigeria murna da farin ciki.

Sai dai a zahirin gaskiya har yanzu Nigeria da wasu kasashen nahiyar afirka ba su kubuta daga mulkin mallaka na turawa ba, domin kuwa turawa sun zamanantar da mulkin mallaka a wannan karnin ta hanyar kawo tsarin mulkinsu Demokaradiyyah.

Kafin samun 'yancin kan Nigeria, shekaru da dama kakanninmu suka kwashe suna neman turawa su basu 'yanci su huta daga bauta, turawan da sukaga babu yadda zasuyi shine sai suka bamu 'yanci a takarda, amma sai sukayi wani wayo da dabara cikin ilmi ta yanda zasu cigaba da yin mulkin mallaka a kasarmu Nigeria ta hanyar kawo mana tsarin mulkin Demokaradiyyah.

Shi wannan sabon tsarin salon mulkin mallaka (Demokaradiyya) wanda turawan Amurka suka bijiro dashi, sun kawoshi ne a lokacin da wasu jiga-jigan shugabanninmu irinsu jinin Shehu Usman Dan Fodio kuma jikan Mujaddadin musulunci  Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello da su Sir Abubakar Tafawa Balewa (Allah Ya jikansu) suka dinga tayar da jijiyan wuya kan cewa lallai turawa su tashi su bar mana Kasa, shine sai turawan suka amince, amma sai suka kawo sabon salo na dabara a matsayin sharadi wanda zasu zamanantar da mulkin mallaka a ilmance domin Kasarmu Nigeria da Kasashe irin namu suci gaba da tafiya a irin tafarkin da turawan suka daura kasashen namu a kai.

Turawa sukace duk 'Kasar da takeso a bata 'Yanci, to wajibi ne ta rungumi tsarin mulki na "Demokaradiyyah" wanda suke yiwa fassara da cewa tsarin mulkin jama'a ne kuma domin jama'a, a cikin wannan tsarin mulki akwai alheri amma sharrinsa yafi yawa a kasashe irin namu, a zahiri turawa sun baiwa tsarin Mulkin Demokaradiyyah suna mai ma'ana,  a gurinsu duk wani tsarin mulki idan ba na Demokaradiyyah bane koda tsarin mulkin musulunci ne to zasu masa batanci da cewa Mulkin kama-karya, mulkin zalunci, mulkin danniya da take hakkin bil'adama, koda Kuwa Shugaban ya Kasance mai adalci a shugabancinsa wanda ba na tsarin mulkin Demokaradiyyah ba.

Misali da Kasashen Libya, Sudan, Jordan, Syria, Egypt, Kasashe ne da basa tafiya bisa tsarin mulki irin na "Demokaradiyyah" suna mulki ne yadda ya dace da addini da al'adunsu da ra'ayin gwamnati, wannan ne silar da takai ga turawa suka samar da 'yan tawaye/'yan ta'adda a cikin irin wadancan kasashe da basa bin tsarin mulkin Demokaradiyyah tare da basu goyon baya, wanda shine silar ham6arar da mulkin wasu Shugabannin, kuma ya zamo ajalin wasu shugabannin, daga karshe turawa suka kakaba musu tsarin mulkin Demokaradiyyah.

Akwai matsalili masu tarin yawa wanda Kasashe irin namu ba zasu iya yin gaban kansu wajen magancewa ba idan turawa ba su yarda ba, misali da abinda ya shafi matsalar tattalij arzikin kasa da tsaro, akalar sarrafa tattalin  arziki da tsaro yana hannun turawa, hatta abubuwa da suke faruwa na rikicin 'yan tawaye da ayyukan ta'addanci sabon salo ne da turawa suka kawo don su zamanantar da mulkin Mallaka su cigaba da satar dukiya suna kaiwa kasashen su.

Turawa masu zamanantar da mulkin mallaka suna amfani da bankin duniya su karya tattalin arzikin Kasar da suka ga dama a duniya, sannan suna amfani da manyan kungiyoyin kare hakkin bil'adama na duniya su karfafi ayyukan ta'addanci, suna kera manyan jiragen yaki da manyan kayan yaki na zamani, suna sayarwa a kasashe irin namu da ke fama da ayyukan ta'addanci a matsayin babbar hanyar samun kudadensu, wannan ya sa ba zasu taba goyon bayan a magance ayyukan ta'addanci a kasashe irin namu ba.

DUBA WADANNAN:

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BIAFRA

SHEKARU 58 DA SAMUN 'YANCIN KAN NAJERIYA CI GABA KO KOMA BAYA?

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BASASAR NIGERIA

Idan Gwamnati tana bukatar kubuta daga mulkin mallakar turawa na zamani sai ta cusawa matasa kishin Kasa da hadin kai a cimin zukata, sannan a saukaka hanyar neman ilmin boko, a wajabta koyon ilmin kimiyya da kere-kere, kamar misali da tsarin da tsohon shugaban juyin juya hali na Kasar Iran Ali Al-kumaini yayi, idan ya kasance matasa sun taso da kishin kasarsu, sun kware a ilmin boko da kimiyya, duk abinda ake bukata za'a iya kerashi a cikin Kasa, to babu shakka kasar zata iya kubuta daga tsarin mulkin mallaka na turawa.

Daga karshe ina addu'ah Allah Ya daukaka darajar Nigeria, Ya magance mana dukkan matsaloli da suke addabar Kasarmu Nigeria Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user