Monday 21 October 2019

Jaruma Fati Washa ta Tayar da Kura a Shafukan Sada Zumunta Bayan Fitar Wasu Zafafan Hotunan Ta

Tura Wannan Zuwa
Na ji ana ta maganar wata yar wasan Hausa wai ita Fati Washa da hoton da ta dora a Instagram.

Jaruma Fati Washa

Marubuci: Aliyu Dahiru Aliyu

Wallahi har ga Allah sai da na kalli hoton ya kai sau 10 kuma kallon kurilla amma ban gano laifinsa ba sai da na ga wani yana jawabi ta kwament sannan na gane me ya janyo hatsaniyar. Wai ashe “yan hisbar” suna magana akan rashin sanya rigar mama da ta yi ne har wani shati na jikinta ya bayyana ta cikin rigar. Allah in dai kai irina ne sai an maka bayani za ka gane.

Abin da ya bani mamaki shi ne a yau idan ka je YouTube kana bincikawa ka dinga ganin bidiyoyin batsa na Hausawa suna samun “views” dubunnan daruruwa a kankanin lokaci sai ka rasa to daga ina ake samun masu kallon! Tabbas dai da yawan masu maganar tarbiyyar nan su ne munafukan da suke zagayawa suna kallon batsa cikin harshen Hausa. Na fi shekara nawa ina neman mu hadu a fassara Kimiyya da Falsafa cikin harshen Hausa amma ban yi nasarar masu fassara “pornography” ba.

Binciken da nake akan yadda ake amfani da Intanet a kasar Hausa ya sanya na gano al’amura masu ban mamaki. Wa’azi ko nasiha ba sa samun “views” 10k a shekara guda amma batsa na iya samun 100k a sati daya! Kuma wadanda suka kalla din nan su ne za su dawo su rufarwa da Fati Washa saboda su nuna su na Allah ne a bakin duniya ko kuma su kara bayyanawa da duniya yan fim ba su da tarbiyya. Da gyaran tarbiyyar dai za a yi sai a yi duka. Amma kana jin dadin me suke kuma ka fito tsabagen iya riya da munafunci ka ce wai sai sun canja wannan shi ne yaudarar addini.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Hotuna da Cikakken Tarihin Fati Washa

Fati Washa Ta Kona Shafin Instagram da Wasu Zafafan Hotunan ta

Kalli Sababbin Hotunan Jaruma Fati Washa Waɗanda suka fi Ɗaukar Hankulan Shafukan Sada Zumunta

Yau da za ka leka Messenger din wasu “mala’ikun social media” din da abin zai baka mamaki! Mutum ya bi yarinya su yi ta batsa da iskanci amma yau da Rahama Sadau za ta yi hoto babu dan kwali to fa har Alqunutu zai iya yi mata. Daga baya kuma ya zaga ya tafi YouTube yana ganin yan mata suna batsa yana kara musu views.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user