Friday 15 November 2019

ALLAHU AKBAR: Shin Kana da Abinda Zaka iya Saka ma Mahaifiyar Ka dashi a Duniya?

Tura Wannan Zuwa Ga
Abinda na karanta ya RATSA duk jikina.

Tun kana cikin mahaifiyarka Allah Ya kareka daga dukkan cuta, ya saka maka hanyar abincin ka ba tare ka sha wahala ba.

Mahaifiya da Yaron ta

Marubuci: Datti Assalafy

Mahaifiyar ka tayi naƙuda tana zufa, ihu, kuka da hawaye, kana fadowa duniya cikin radadin zafin haihuwa zata yi murna tana murmushi tana godiya ga Allah da Ya baka ikon fitowa lafiya.

Bayan an haifeka sai Allah ya janyo maka jijiyoyi guda biyu a kirjin mahaifiyarka da suke dauke da mafi tsaftar tatacciyar madara, mai dumi a lokacin sanyi, mai sanyi-sanyi a lokacin zafi, don ka sami hanyar yin ƙoto.

Ka shigo duniya baka da ƙwayar haƙori, daga lokacin da hakori ya fara fito maka kake fara azabtar da mahaifiyarka dashi, amma ko da yaushe tana murna tana nuna wa jama'a tana cewa yarona ya fara hakora.

Kayi mata tunbudi, kashi, fitsari ta wanke ba tare da ta taba ko yatsina fuskarta ba, ka hanata bacci ka hanata sukuni amma tana murna tana yarona akwai shi da kuzari.

Daga lokacin da ka sami kafa wata zubin da kyar ake iya sanin inda kake, mahaifiyarka bata koshi sai ta tabbatar da koshinka, bata sukuni da walwala sai ta ganka cikin walwala.

Shin Kana da abinda Zaka iya saka mata dashi?

Duk wanda mahaifiyarsa ta rasu muna roka mata rahmar Allah.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA CIKIN GAGGAWA

ALLAHU AKBAR: TAYI NASIHA MAI RATSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI JIM KADAN TA RASU

HANKALI NA YANA TASHI IDAN NA TUNA DA WANNAN

Wanda iyayensa ke raye muna fatan za'a kyautata musu fiye da kowa a duniya.

Allah Ka gafarta mana Ka bamu ikon cikawa da kyau da imani Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user