Friday 15 November 2019

KARANTA SHARHIN DATTI ASSALAFIY AKAN BAYANIN SARKIN KANO GAME DA SACE YARAN MUSULMAI

Tura Wannan Zuwa
Wannnan rubutun ba raddi bane, sharhi ne da tunatarwa ga Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II, game da batun da yayi na cewa da yana da iko da ya kama iyayen da suka bari inyamurai suka sace yaransu, saboda wai sakaci ne a fahimtar Sarki Muhammadu Sanusi .

Sunusi II

Marubuci: Datti Assalafy

A fahimtata wannan maganar da Mai martaba yayi babban kuskure ne da tuntuben harce, iyayen nan da aka sace musu yara akaje aka canza musu addini da suna aka sayar dasu don aikin bauta, a tawa fahimtar basu cancanci irin wannan kalamai daga Mai martaba ba, saboda suna fama da radadin ciwon zuci da kuma bakin ciki, don haka bai kamata a musu barazana da cewa Sarki zai kamasu ba!

Batun garkuwa da mutane a Kasarnan Nigeria; tarihi ya nuna; tarihi ya tabbatar da cewa inyamurai sune suka fara yin garkuwa da safarar mutane a Nigeria, daga baya suka koyawa 'yan Arewa, duk wani mugun aiki da mugun laifi inyamurai suka fara aikatawa a Nigeria, don haka tsohuwar sana'arsu ce wannan.

Sannan a Nigeria babu wanda yafi karfin ayi garkuwa dashi, domin har babban jami'in tsaro wanda ya taka matsayin GENERAL a gidan soji anyi garkuwa dashi aka hallakashi, an taba yin garkuwa da soja mai mukamin Kanar aka hallakashi, an taba yin garkuwa da babban jami'in 'dan sanda mai mukamin mataimakin Kwamishinan 'yan sanda kwanannan aka kubutar dashi, ko wata guda ba'a yi ba.

Ba da dadewa ba akayi garkuwa da babban basaraken gargajiya magajin garin Daura, an saceshi tun daga garin Daura aka kawoshi cikin birnin Kano, birnin Sarki Muhammadu Sanusi II aka boyeshi kusan wata biyu, daga bisani jami'an 'yan sanda suka kubutar da shi a hannun masu garkuwa da shi.

Wannan yana nuna mana cewa hatta su kansu manyan jami'an tsaro masu rike da makami na tsaron rayukan 'yan Nigeria basu fi karfin ayi garkuwa da su ba a Nigeria, haka suma manyan sarakunan gargajiya masu daraja ta farko ba su fi karfin ayi garkuwa da su ba, to balle kuma 'dan talaka wanda babu mai gadinsa sai Allah, babu fadawa da suke gewaye dashi, babu jami'an tsaro dauke da bindigogi da suke gadinsa a gida da duk inda zai je.

Masu hikimar magana sunce; duk wanda yake son kayanka ya fika dabara, masu garkuwa da mutane ko masu satar yara basa kama mutum ko satar yara lokaci guda face sai sun kiwaci mutum ko yaran da zasu sace, yaran nan suna fita daga gidan iyayensu su tafi makaranta, iyayensu suna iya aikansu waje, lokacin da za'a sace yaransu ba su sani ba, kuma haka kawai da gangan iyaye ba zasu bari a tafi musu da yara ba, ko karuwa ce da ta yadda tayi cikin shege ba zata yarda da wannan ba, balle iyayen da sukayi auren sunnah.

DUBA WANNAN: Shin dagaske Ne duk 'Yam Matan Jami'a Lalatattu Ne?

Na tabbata yaran da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi ya haifa idan zasu fita daga gida sai da rakiyar jami'an tsaro ko fadawa don su samu kariya daga miyagun mutane, yaran talakawa fa? wa yake rakasu idan zasu fita daga gida?

Allah Ya jikan Al-marhum, Al-mufassir shahid Insha Allah Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano, Malam Ja'afar yayi wasu maganganu game da Sarki Muhammadu Sanusi II akan mas'aloli irin wannan tun kafin ya zama Sarkin Kano lokacin Malam Ja'afar yana raye, to amma ni Datti Assalafiy zan iya yiwa Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II uzuri akan cewa; "Dan Adam mai iya canzawa ne a kowani lokaci", iyakarta kenan! imba haka ba da sai nace Malam Ja'afar Kano ya hutar dani game da haskaka mana waye Sarki Muhammadu Sunusi II

Allah Ya jikan Sheikh Ja'afar
Allah Ya taimaki Sarki Muhammadu Sanusi II Ya bashi ikon fadin daidai da aikata daidai Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user