Saturday 11 January 2020

Sauke Sabuwar Wakar Abba Muhammad Dan Hausa - Ina Kike

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Soyayya.


Abba Muh'd Ɗan Hausa Yayin Rera Waƙa a cikin Studio..

Abba Muhammad Ɗan Hausa , fitaccen Mawaƙi ne a arewacin Nijeriya  musamman cikin jihar Kano , duba da yadda yake fitar da waƙoƙin shi masu ɗauke da sakonni na musamman, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen bunƙasar waƙoƙin sa ciki da wajen ƙasar nan.

Taken Wakar "INA KIKE"

Daga jin taken wannan wakar munsan bakwa bukatar sharhi akai.

Abba Muhammad Dan Hausa , ya rera wannan waƙar ne domin tunatar da masoyiyar shi tasirin soyayyar ta a cikin zuciyar shi, wanda hakan ne ya sanya yake mafarke-mafarke (na Zuciya) akan ta saboda tasirin soyayyar ta a cikin ran shi.

Wannan dai sabuwar waƙa ce da mawaƙin ya rera cikin wannan sabuwar shekarar da muke ciki (2020).

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙin wanda ya baje kolin basira da hikimar sa a cikin waƙar.

Ga kaɗan daga cikin baitin waƙar:

Ina kikee?

Ina kikee?

Ina kikee?

Nemanki ni nake,
Kin shiga zuciya ga shi kin ɓace.

Gashi kin ɓace.

Ɗangon Waƙa:

Ke ce nake so ki zam cikin gidana a gefena,
Ke ce nake so ki zam uwa ta 'ya'ya, iyalina,

Ummm!

Ke ce farin-ciki da ke bayyana a rai da fuskana,
Ina kike zo mu tattauna?
Mu je gida ki gaida Ummana.

Ina kikeeee! Ina Kikee?

Ina kike?

Nemanki ni nake,
Kin shiga zuciya ga shi kin ɓace...

Kardai mu cika ku da surutu ku sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

Ku sauke waƙar anan..


Kada Ku Sake A Baku Labari...

Domin samun sababbin waƙoƙin siyasa, waƙoƙin Soyayya, waƙoƙin bege, waƙoƙin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Abba Muhammad Dan Hausa - Sako Ga 'Yan Arewa

Abba Muhammad Dan Hausa - Garkuwata

Isah Ayagi - Ni Naki Ne Abadan Da'Iman

Ku Ci gaba da kasancewa da Mu domin samun Cikakken Tarihin mawaƙi Abba Muhammad Dan Hausa nan bada daɗewa ba Insha Allah.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za'ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user