Thursday 5 March 2020

Kaso Mutum Kuma Kayi Hankali da Mutum a Duk Inda Ka Kasance

Tura Wannan Zuwa Ga
Mutum ne zai yi maka fatan alkhairi, amma idan alkhairin yazo shi zai fara nuna hassada a gareka.

Saboda Ɗan Adam babu mai iya masa sai ALLAH...

Marubuci: Bashir M. Sulaiman

Mutum ne za kayi masa alkhairi sama da sau ɗari, ranar da kai kuskure guda ɗaya dukkan shi ya rushe.

Mutum ne yake rububin ka idan yaga dama ta same ka, amma da zaran damar ta kuɓuce baka sake ganin shi.

Mutum ne za kayi masa alkhairi, daga ƙarshe ya zo yayi maka sharri.

Mutum ne yana hangen wata matsala na iya samunka, amma bazai sanar maka ba, sai bayan ta faru.

Mutum ne zaka riƙeshi amana, amma shi yaci amanar ka.

Mutum ne idan yaga samun duniya a gare ka, zai zo ya raba ka da mutanenka na asali, waɗanda suka san mutuncin ka, amma da ta gushe shi kuma sai ya gudu ya barka.

Ya ALLAH ka haɗa mu da mutane masu ƙaunar mu na gaskiya, kuma tsakani da ALLAH Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: