Friday 6 March 2020

Rayuwar Duniya Tana Tafiya Ne Akan Abubuwa Uku

Tura Wannan Zuwa Ga
Rayuwa tana murginawa ne bisa lokuta uku:

1. Lokacin da ya shuɗe (Jiya kenan)
2. Lokacin da ake ciki (Yau kenan)
3. Lokacin da ake jira (Gobe kenan)

Nazari Aikin Mai Hankali


A cikin waɗannan lokuta, Lokacin da ake ciki duk ya fi su muhimmanci, don kuwa Jiya ta wuce kuma har abada ba za ta dawo ba, Gobe kuma ba ta zo ba, kuma babu yaƙinin ganinta.

Yi ƙoƙarin ka amfani Yau ta hanyar ambaton Allah da yawaita Istigfari, ka kuma rage dogon buri (musamman ma mummuna), don ba ka san lokaci da wurin da za ka ci karo da mutuwa ba.

Allah Ta'ala Ya shiryar da mu, Ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: