Tuesday 17 March 2020

Karanta Abubuwa 6 da Mata Suke So Amma Basu Cika Furta Su Ba

Tura Wannan Zuwa Ga
1. Faɗa musu gaskiya, mata suna matuƙar son mutumin da baya ɓoye musu gaskiya yana kuma burge su sosai dan haka aboki kar kayi wa matarka ko budurwar ka  ƙarya don tana ganewa kayi mata ƙarya to kasa mata shakka zata dinga ji a ranta anya kuwa zaɓen da nai banyi zaɓe marar kyauba.

Ka Lura da Wannan a Soyayya

Marubuci: Abdulyassar Goron Dutse

Karya na matuƙar cutar da soyayya ko ga ma'aurata.

ANA IYAYIN KARYA KAƊAN A TSAKANIN MIJI DA MATA DAN KWANTAR DA HANKALIN MATA.

2. Mata suna son a fahimce su
wato mata ko da yaushe suna son wanda yake kusa dasu ko masoyan su su fahimci komai game da su kamar me take so meye bata so tana da hali kaza da kaza bata da kaza da kaza, saboda haka aboki kayi ƙoƙarin ka karanci halin budurwarka tun kafin aure ko bayan aure kana kuma faɗa mata zaka ga tana mamaki ya akai ka sani zata ji daɗi, ta yadda tana riƙe da hakan a zuciyar ta lallai wane ya san halina ya kuma fahimci abun da nake so da wanda ba na so.

3. Mace na son ka zama me nuna mata kai jarumi ne me basira, dan mata suna son jarumi me ƙwazo bawai kullum kai ta ƙasƙantar da kanka gareta ba a'a ka zama me nuna mata ƙwazo da fasaha hakan na sa suji lallai sun iya zaɓe, dan suna son wanda zai basu tsaro da kulawa koda yaushe budurwa ko matar aure tana so ace mijinta mai ƙoƙarine ko jarumi ne.

4. Ka zama me nuna mata soyayyarka koda yaushe, mata suna matuƙar jin daɗin zama da Namijin da yake nuna musu soyayya koda yaushe da kulawa domin suna buƙatar hakan tsawon rayuwar su ,ba wai kawai a jiye soyayyar azuci ba kaƙi furta ta ko da yaushe.

TABBAS SUNA MATUKAR SON NAMIJI MAI IYA SOYAYYA KUMA SUKAN KASA RABUWA DASHI.

5. Zuzutawa mata naso a zuzuta su akai su babban matsayi koda basu kai ba, misali budurwarka kana ce mata wance banga wata mace mai ƙira irin taki ba,kina da kyau sosai kina matuƙar ruɗani fiya da tunani, ke kaɗai nake so da , sarauniyar 'yan mata ,da shauransu.

6. Mata naso a Jiɓinci Al'amuran su ta hanyar Hidimta musu wato kamar tsaro da tallafin kuɗi, mata suna buƙatar koda yaushe kazama kana basu kulawa da tsaro, da biya musu buƙata dai-dai misali, ba wai tarin kuɗi me yawa ba a'a ko da rake kake sayarwa dai-dai samun ka kanai mata hidima bawai kullum soyayya ba amma ba 'yar gudunmawa ko kyauta, hakan nasa mace taji bata sonka dan in anyi auran ba zaka iya yi mata abubuwan da take buƙataba. Da sauransu su,

Allah ya zaɓa Abinda yafi Alkhairi Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user