Saturday 28 March 2020

KARANTA LABARI MAI TABA ZUCIYA NA WANI YARO DA MAHAIFIYAR SHI

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani yaro ne ya zauna yana taɗi da mahaifiyar sa sai yake nuna mata yadda yake son ta da ƙaunar ta, ita ma tana faɗa ma sa yadda take matuƙar son sa a cikin birnin zuciyarta. Daga cikin abin da take gaya masa ta ce, na sha wahala ƙwarai wajen rainon cikin ka. Allah ne kawai ya nufi zan rayu. Ga shi kuma ka tashi mai yawan ciwo a kullum ina kan hanyar asibiti.


Uwa Uwa Ce....

MarubuciIsah Ade

Da dare kuma ba na samun bacci saboda yawan kukanka. A cikin raha sai ta ce masa, yanzu idan ka girma da me za ka saka min ne? Ya ce, Mama kada ki damu, idan na girma zan samu aiki mai kyau da albashi mai ƙwari sai in riƙa sawo maki duk abin da kike so.

Ta ce, ai wannan daman mahaifinka yana yi. Kuma ka ga ma kafin ka girma tsufa ya fara kama ni, ba ni buƙatar jin daɗi fiye da wanda nake ji a yanzu. Ya ce, to Mama ba wata damuwa, zan auro Mata mai hankali da kirki wacce za ta riƙa girka maki abinci, ta share ɗakinki, takula da ke sosai. Ta ce, a’a. Wannan ai ba aikinta ba ne. Kuma ba za ka aure ta don wannan ba, don Allah bai ɗora mata yin haka ba.

Ni ma kuma ba haka nake buƙata wurin ta ba. Za ka auri Mace ne don buƙatar kanka da kula da ‘ya’yanka idan Allah ya ba ku. A nan ne fa ya yi shiru, ya nunfasa, sannan ya ce, Umma! To me zan yi in biya ki kenan? Ta ce, ALHAMDULILLAH. Ka zo ga tambayar da nake so ka yi min.

Kada ka bar ni. A kowanne hali da kuma duk in da kake ka riƙa bin labarina; ka ziyarce ni ko ka buga min waya, ka riƙa ɗebe mini kewa da jin ɗuriyarka. Idan ajalina ya zo ka runguma ni tare da jama’a ku kai ni makwancina. In kun rufe ni ka tsaya ka yi mani addu’a. Sannan ka yawaita yin sadaka a gare ni.

A duk sallah ka riƙa sa ni cikin sujudarka kana neman rahamar Allah a gare ni. Ka tuna cewa, duk aikin alheri da kake yi ina da kamasho a cikin sa. Sannan ka sani cewa, ɗaukar cikinka da na yi da rainon ka ba aiki ne da na yi shi bisa wata yarjejeniya ba.

Samun ka wata baiwar Allah ce da kyautarsa da ya sanyaya rayuwata da ita. Tare da haka kuma yana ba ni ɗinbin lada a kan ta. A nan ne fa yaron ya sunkuyar da kansa yana hawaye. Uwar ta rungume shi tana share hawayensa tare da yi masa addu’oi na samun nasara da ci gaba da samun dace a rayuwarsa.

Darussa:

Uwa uwa ce, wacce babu irin ta.

Ba mu iya biyan iyayenmu alhakin haifuwarsu amma muna iya saka musu ta hanyar zama na kirki da bin kyakkyawar tarbiyar da suka ɗora mu a kan ta.

Muna auren mata ne don buƙatar kanmu ba don su yi hidimar iyayenmu ba. Amma fa dole ne su mutunta su tare da kyautatawa a gare su. Maso uwa ya so ɗanta. Mai son miji dole ne ta so surukarta.

Haƙƙin iyaye ba ya ƙarewa har mutuwarsu. Addu’a da yi masu sadaka da kyautata namu ayyuka duk suna cikin kyautatawa a gare su.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user