Sunday 8 March 2020

Sauke Sabuwar Wakar Isah Ayagi - Mutu Ka Raba

Tura Wannan Zuwa
Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Soyayya.


Isah Ayagi - Mutu Ka Raba

ISAH AYAGI, fitaccen mawaƙi ne a masana'antar shiya fina-finan Hausa (Kannywood), duba da yadda yake fitar da waƙoƙin shi masu ɗauke da sakonni na musamman cikin faɗakarwa da Nishaɗantarwa, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen bunƙasar waƙoƙin sa ciki da wajen ƙasar nan.

Taken wakar "KIN ZAMA CIKON FARIN CIKINA NA DUNIYA, KIN SHIGA ZUCIYA BAMAI CIREWA MUTU KA RABA".

Daga jin taken wannan wakar munsan  cewa bakwa buƙatar sharhi akai.

Waƙar HIJIRA (Da Sauran Kallo) , ita ce wakar da tayi sanadiyyar shaharar sa a farfajiyar Kannywood dama Duniya baki ɗaya.

Isah Ayagi , ya rera wannan waƙar ne cikin wani salo mai ban sha'awa da tafiyar da zukatan masoya, lallai waƙar Mutu Ka Raba ta cancanci samun kyautar girmamawa.

Idan baku manta ba , a baya mawaƙin ya fitar da waƙar Mukullin Zuciya, sanin kowa ne cewa waƙar tayi fice sosai duba da yanayin kalaman da mawaƙin yayi amfani da su a cikin waƙar tun daga ɗangon waƙar (Mukullin Zuciya) zuwa baituttukan waƙar.

Mutane da dama sun fi sanin waƙar da sunan Mutu Ka Raba da Ni da ke nayi Aniyar Zama da Ke , babu mai raba mu Ni dake , kena ba Mukullin Zuciya, duk da cewa ba wannan bane sunan waƙar.

Hakan yasa mawaƙin ya kuma zama ya shirya sabuwa mai taken Mutu Ka Raba, idan baku manta ba munce muku sunan waccan waƙar Mukullin Zuciya.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

Ku Sauke wakar anan..

DOWNLOAD MUSIC HERE

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

Zaku iya sauke Sababbin wakokin Isah Ayagi harma da Tsofaffin Wakokin Isah Ayagi a kyauta idan ku shiga link ɗin dake ƙasa.

SABABBIN WAKOKIN ISAH AYAGI 

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za'ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user