Friday 20 March 2020

Sirrin Soyayya da Tausayi Tsakanin Ma'aurata

Tura Wannan Zuwa
Idan Allah ya sa soyayya da tausayi da rahama tsakanin miji da matar shi za suyi rayuwar aure cike da mutunta juna da kare haƙƙin juna ko ana tare ko ba a tare, ana cikin ƙuruciya ko an manyan ta ana cikin wadata ko ana fama da talauci da wahalhalun rayuwa, an samu arzikin haihuwa ko ba haihuwa, ana cikin lafiya ko jinya ta zo.

Soyayya Ce Sirrin Cimma duk Wasu Mafarkan Rayuwar Ma'aurata


MarubuciIbrahim Nuhu Imam Rimi

Soyayya ta gaskiya da rahama da tausayi kaɗai ke sa ma'aurata su ke wa juna afuwa idan kuskure ya faru, su ke fatan alkhairi wa juna ana raye ko  bayan mutuwar ɗayan su.

In da akwai soyayya ta gaskiya da rahama tsakanin ma'aurata da miji bai wulakanta matar shi ba, da bai sake ta ba ya bar ta da fama da yaran shi ba tare da kula da haƙƙoƙin su ba.

Haka ita matar da bata cutar da mijin ta ba ta hanyar mallake shi da raba shi da `yan uwan shi  har da iyayen shi don kawai ta more dukiyar shi ita kaɗai,  in Allah ya jarrabe shi da talauci kuma ta rabu da shi ta auri wani.

Kai miji ka sani fa akwai  namijin da ya fika komai amma matar ka ta amince da kai ka zamo mijin ta, ke ma ki sani fa cewa akwai matan da suka fiki komai amma mijin ki ya gamsu da ki zamo matar shi, don haka aure alƙawari ne.

Lallai in Allah ya tsawaita rayuwar ma'aurata lokaci zai zo wanda ba zasu ji daɗin dukiya da abun duniya ba, ba za su yi sha'awar komai ba, a wannan lokaci in akwai abunda zasu mora shine ƙauna ta gaskiya da tausayi da rahama a tsakanin su.

Allah ya sanya soyayya da ƙauna da tausayi tsakanin ma'aurata Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user