Wednesday 8 April 2020

Karanta Babban Sako Ga Masu Sha'awar Yin Aure

Tura Wannan Zuwa Ga
Yin aure, abune da ya dace da hankali da shari'a da al'ada mai kyau. Akwai hikimomi masu tarin yawa wajan yin aure, ga maza da mata, kasancewar mutane sun banbanta a halitta da halaye da yanayi, yasa malamai suka kalli ayoyi da hadisai da suka yi kira akan yin aure suka basu fassara kashi uku.

BABBAN GA MASU SHA'AWAR YIN AURE..

Marubuci: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Wasu malamai suna ganin yin aure sunna ne, abinda suke nufi, idan kayi aure zaka sami lada, amma idan ba kayi aure ba, kuma baka yi fasiƙanci ba, baka da alhakki.

Na biyu sunce yin aure sau ɗaya a rayuwa wajibi ne ga mutum, idan ya zauna bai yi aure ba yayi laifi, domin wajibi shine abinda shari'a ta nemi ayi shi dole, idan mutum yayi yadda aka umarce shi zai sami lada, idan kuma yaƙi ya zama abin zargi, kuma ana iya yi masa uƙuba akan haka.

Na uku suka ce shi aure ya kasu gwargwadon yadda mutane suka karkasu:

Na ɗaya: wanda aure ya zama wajibi a kansa. (shine wanda yake da ƙarfin sha'awa kuma yana da halin da zai iya riƙe auran ko sana'a, kuma idan bai yi auran ba zai yi lalata.)

Na biyu: wanda aure ya zama sunna akansa. (Wanda zai iya ɗaukar nauyin iyalin kuma yana yin wata sana'a ko neman ilimi, bashi da sha'awa mai ƙarfi).

Na uku: wanda aure ya zama haramun akansa. (Wanda ba zai iya ɗaukar nauyin matar ba, kuma bashi da buƙatar auran, ko idan yayi zai dinƙa cutar matar, wajan hana ta haƙƙoƙinta, ko bashi da lafiya wajan biyan buƙatar iyali).

Na huɗu: wanda aure ya zama makruhi akan sa. (ba a so yayi aure saboda ya shagala da wani abu mai mahimmanci, ko ibada ko wani ilmi, ko wani bincike wanda ya hana shi samun lokaci, ko kuma bashi da sha'awa, kuma babu tsoran yin lalata tare da shi.).

Na biyar: wanda aure ya zama halal a gareshi (idan yayi babu matsala, idan bai yi ba babu matsala).

Wannan shine fassara da malamai suka bayar ga dukkan ayoyi da hadisai masu kira da yin aure.

Kada kayi ganganci wajan zaɓin abokiyar zama, ko abokin zama ga mace, ayi istikhara, a nemi shawara, kuma abi a hankali, Kuma aje ayi gwajin lafiya, kamar ƙanjamo,  da sikla da ciwan hanta, da sauran cututtuka da ake ɗauka.

Allah ya haɗa kowa da nagari Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user