Wednesday 8 July 2020

Karanta Addu'a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi

Tura Wannan Zuwa Ga
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai yace masa;

لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .

La ba'asa tahoorun in sha'al-lah.

Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.

Addu'a Ga Mara Lafiya

أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)

Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7).

Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwai).

Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya faɗi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya".

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user