Tuesday 11 August 2020

Karanta Addu'ar Da Ake Yiwa Mara Lafiya Wanda Ya Yanke Kauna Daga Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga
أَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَأَلْحِقْنِي بِالرَّفِيقِ اْلأَعْلَى.

Allahummagh-fir lee, warhamnee wa-alhiknee birrafeekil-a'la.

Addu'ar Da Ake Yiwa Mara Lafiya Wanda Ya Yanke Kauna Daga Rayuwa..

Ya Allah! Ka gafarata mini, Ka ji ƙaina, kuma Ka riskar da ni da abokin zama mafi ɗaukaka.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayin da ajali ya zo masa, sai ya riƙa sanya hannayensa a cikin ruwa yana shafa fuskarsa da su yana cewa;

لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله، إِنَّ لِلْمَوْتِ لَسَكَرَاتٍ.

La ilaha illal-lah, inna lilmawti lasakaratin.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; haƙiƙa mutuwa tana da magagi mai ɗimautawa.

لاَ إِلَهَ إلاَّ اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ.

La ilaha illal-lah, wallahu akbar, la ilaha illal-lahu wahdah, la ilaha illal-lahu wahdah, la shareeka lah, la ilaha illal-lahu lahul-mulku walahul-hamd, la ilaha illal-lah, wala hawla wala ƙuwwata illa billah.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare Shi, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mulki da yabo nasa ne, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user