Sunday 9 August 2020

Sauke Sabuwar Wakar Sani Liya-Liya - Kishiya 1

Tura Wannan Zuwa
Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Soyayya ta Barkwanci.

Kishiya 1

Sani Abdullahi Alasan wanda aka fi sani da Sani Liya-Liya Baran , sabon mawaƙi ne kuma marubuci ne wanda tauraruwar sa take haskawa a halin yanzu tun bayan fitar waƙar Sambisa.

Taken waƙar "HAR GUDA NAWA ZAKA YI? YADDA ANNABI YA FAƊA, GASHI KU KUMA BAKU FATAN AYI MUKU KISHIYA".

Waƙar dai tazo da wani sabon salo a cikin masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), wanda bakasafai ake ganin hakan a cikin waƙoƙin masana'antar Kannywood ba.

Kishiya waƙar barkwanci ce , waƙar tana nuna irin halin matan nan waɗanda zasu iya sadaukar da komai na rayuwarsu don kar mijin su ya ƙaro musu abokiyar zama (Kishiya).

Kar ku manta ita ma waƙar Kishiya mai dogon zango ce kamar dai yadda waƙar Sambisa take, tun daga ta ɗaya zuwa ta huɗu kuma duk da haka har yanzu ba a kammala waƙar ba, kamar misalin haka waƙar Kishiya take.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

Zaku iya sauke sababbin wakokin Sani Liya-Liya harma da tsofaffin wakokin Sani Liya-Liya a kyauta idan ku latsa rariyar liƙau ɗin dake ƙasa.


SABABBIN WAKOKIN SANI LIYA-LIYA

Ku Ci gaba da kasancewa da Mu domin samun Cikakken Tarihin Sani Liya-Liya nan bada daɗewa ba Insha Allah.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user