Thursday 10 September 2020

Hanya Mafi Sauki Domin Furta Kalmar So Ga Wanda Kake So Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
TAMBAYA

"Wata yarinya na gani na kuma kamu da sonta, kuma ina zuwa gidansu, yaya zan yi na bayyana mata ina son ta?"

Furta Kalmar So

MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa

AMSA

Zata iya kasancewa babba ce ko ƙarama, to koma dai yaya take a karon farko akwai buƙatar kafin ka furta mata da baki, kake nuna mata wasu alamomi da zasu ke bayyana mata hakan a zahiri. ta hanyar fifita ta fiye da sauran 'yan gidansu.

Idan ka tashi zuwa gidan da wata tsaraba ko wata kyauta ya kasance tata ta fi ta kowa yawa. Idan salla ta zo ka ɗinka mata kayan salla da takalmi da sauran kayan kwalliya na mata dai-dai ƙarfinka ka aika ko ka kai mata su. A lokacin azumi kake aika mata da kayan shan ruwa.

Idan ka je gidansu ko da bata nan kake tambayar ina ta tafi, idan kuka haɗu ka sanar da ita ka je gidansu dan ka gan ta ku gaisa amma sai aka samu akasi baku haɗu ba, kuma baka ji daɗin rashin ganin nata ba.

Kake yawan jan ta da hira, kake bata labarai masu sanya nishaɗi da ɗebe kewa a dukkan lokacin da kuke tare.

Na tabbata ko baka furta kalmar so a gare ta ba za ta shaƙu da kai, za ka ke burge ta, za ta ke son ganin zuwanka, haka kuma 'yan gidansu za su fahimci ƙudurinka na kana sonta.

Bayan an shafe tsawan wani ɗan lokaci hakan na faruwa, sai ka ware watarana ka ziyarce ta har gida ka aika a kirawo ta ka sanar da ita batun da tuntuni take tsammanin ji daga wajenka, wato na kana son ta.

Zaka iya sanar da ita ta hanyar tura mata da saƙo ko akasin haka, amma zuwa da kai, ya fi saƙo.

Idan kuma yarinya ce zaka sanar da ita hakan ne bayan ta kai munzalin tsayawa da samari. Dama tintini 'yan gidansu sun daɗe da sanin manufarka a kanta, har ta kai suna zolayarta da kai, wataƙila ma suna yi maka magana akan hakan ko kuma sun zuba ido suna jiran ka furta hakan da kanka.

Daga nan kuma sai a shiga mataki na biyu wato fagen soyayya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user