Saturday 26 September 2020

Sauke Sabuwar Wakar Hamisu Breaker Ft Umar M Sharif - Arewa Mu Farka

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.


Arewa Mu Farka

Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne su fito su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar da al'umma halin da ƙasar Nijeriya take ciki a halin yanzu, kana kuma a ƙara tunatar da al'ummar Nijeriya musamman yankin arewacin hanyoyin da za abi domin daƙile yaɗuwar fyaɗe da sauran ayyukan ta'addanci wanda su addabi yankunan ƙasar baki ɗaya musamman arewacin Najeriya.

Taken waƙar "INA ZAMU JE! INA ZAMU KWANA! MU TASHI MU FARKA 'YAN AREWA".

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Kaɗan daga cikin mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijeriya dama Duniya baki ɗaya:

Ali Jita
Adam A. Zango
Adamu Nagudu
Ado Gwanja
El-Mu'az Birniwa
Fati Niger
Fresh Emir
Dan Musa Gombe
Hamisu Breaker
Hussaini Danko
Ibrahim Ibrahim
Nazifi Asnanic
Naziru M. Ahmad
Sadik Zazzabi
Umar M. Sharif

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda su baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Mawaƙan sun yi kira sosai ga shugabanni, kana sun taɓa fanni daban-daban wanda 'yan arewa suke ciki a gwamnatin ƙasar amma babu abinda muƙaman nasu suke tsinanawa al'ummar ƙasar musamman matasa waɗanda sune mafiya yawan al'ummar ƙasar Nijeriya.

Wato tsayawa bayyana abinda wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user