Saturday 3 October 2020

Tsakanin So Da Soyayya (04)

Tura Wannan Zuwa
Kauna fa in ta yi yawa ba abin da ba ta sawa, amma duk da haka mace tana da cikakken lokacin da za ta karɓi ƙaunar mutum ta kuma musanya masa da tata, tana kuma da zaɓi in ta ga bai yi mata ba ta watsar, don sau da dama a wannan matattarar ta mu ta Hausa-Fulani namiji ne yake fara ambata wa mace kalmar ƙauna, wani lokacin macen takan zaɓi ta yi asarar wanda take so in dai har sai ta furta masa da bakinta ne zai gane, wannan ma batu ne da za a iya tattauna shi, musamman a tsakanin malaman ilimi da mu masu kallo mu rubuta.

TSAKANIN SO DA SOYAYYA

MarubuciBaban Manar Alkasim

To sai dai, mun ga yadda namiji yake da buƙatar duba gami da kyakkyawan zaɓi kafin ya fara soyayya da mace, to ita kuma macen ya lamarin yake a wurinta? Musamman kasancewar soyayyar yau tsakanin Saurayi da Budurwa tamkar abotar mazuru ce da zakara, waɗanda iyayen gidansu suka amince wa rayuwarsu wuri guda bisa aminci, wannan kuwa ko ba yunwa wata rana akwai tsautsayi da ɓacin rana.

To bari mu waiga baya mu ga yadda soyayya take sanya mutum ya aikata abin da kallo ɗaya ba zai iya ba; Zainab (R.A) Baquraishiya ce kuma makusanciyar Annabi (S.A.W), ajinsa ce ko a wurin aure, ƙaunarsa ta ciyo ta har ta zo majalisinsa a gaban jama'a ta furta cewa ta ba shi kanta ya aura, kenan ta san komai na sa ba soyayyar rana guda ta tunkuɗo ta ba.

Khadija (R.A) Baquraishiya ce, ta ba Annabi (S.A.W) dukiyarta ya yi kasuwanci a ciki, ta ga gaskiyarsa da amanarsa, ta ji labarin mu'ujizozinsa a wurin bawanta, wato Maisara, kafin ta tura cewa tana son Annabi (S.A.W) da aure, kenan ba kallo ɗaya ba ne, ta san komai na sa kafin ta kamu da ƙaunarsa.

Gumaisa'u matar Abu Talha da ake buga misali da ita wajen rubutun soyayya a muslunci, ita ce ma ta ce wa bazawarinta in zai muslunta to shiga musluncinsa shi ne sadakinta, tabbas akwai abin kula, don kuwa maganarta da shi ita ce " Kai mutum ne da mace ba za ta ƙi karɓarka a matsayin miji ba, matsalar dai kawai kai kafuri ne in za ka muslunta to ya zama sadakina" A sawwaƙe za mu gane cewa ta san sa ko da can kafin ya zo wurinta.

Gaskiya {ƙauna} daban, {sha'awa} daban, ita {sha'awa} komai na mutum zai iya sakawa ka so shi, wannan ya tuna min haɗuwata da Ceɗiyar 'Yar-Gurasa, wato Ɗan Azumi Baba, a littafinsa na SAKAINA, ƙarya ma ta iya zama dalilin da ta sanya yarinyar mai kuɗi ta duƙar da kanta ga mai yi wa babanta wanki da guga, wannan ba laifi nake ƙoƙarin fitarwa ba, sha'awa nake ƙoƙarin faɗin yadda take sihirce matasa.

Sau da yawa zaka taras, kyawun fuska, iya magana, wadata, ilimi, shahara, mulki ko shugabanci, iya wanka da sauransu duk sukan kawo ƙaunar rana guda, irin wannan sha'awar ba ta ba mutum damar ya yi aiki da hankali wajen aunawa ko wancan ya cancanci zama masoyi ko bai cancanta ba, ko da kuwa namiji ne shi to bare mace, shi kawai ake so in ba shi ba kuma mutuwa.

Shekarun baya na sami wace irin wannan sha'awar ta jefa ta rijiya har ta kashe kanta, wata kuma ta kai iyayenta ƙara kotu a kan wani ɗan arne, a ƙarshe ta aure shi kuma ta mutu arniya, na sami labarin 'yam mata kusan ashirin da biyar duk an sauke musu inji sakamakon irin wannan sha'awar mai ɗauke da sunan ƙauna.


MAKALOLI MASU ALAKA:

In kana son mutum sabo da Allah ne, mai zai hana ka karanci kyawawan halayensa, ka so kamun kansa, mutuncinsa, rayuwa da shi ta har abada? Meye kuma na kashe kai? Ko saɓa wa iyaye a zahiri? Shi masoyin in ya ga yadda ta yi wa iyayenta don sun saɓa wa abin da take so, anya ba zai yi tunanin cewa in ya saɓa wa abin da take so wata rana shi ma zai taras da haka ba? Sannan meye na mutuwa a gudu a bar masoyi? Me ya sa ba za a yi tunanin yuwuwar abin nan gaba ba?

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user