Thursday 29 October 2020

Yanzu-Yanzu: Rarara Ya Sanya Gasar Kyautar Mota Da Naira Dubu 150 Akan Sabuwar Wakar Sa Ta Matsalar Nigeria

Tura Wannan Zuwa Ga

Wannan dai bashi bane karo na farko da mawaƙin yake sanya gasar motoci da kuɗaɗe akan waƙa, idan mai karatu bai manta ba, a baya ma, Rarara ya sanya gasar kyautar motoci ga duk wanda yayi bidiyo mai matsakaicin zango na waƙar Dogara Ya Dawo.


Dauda Kahutu Rarara

Bayan an kammala gasar waƙar DOGARA YA DAWO, sai ga shi kuma mawaƙin ya kuma bayar da dama ga duk wanda Allah ya ba wata baiwa musamman mawaƙa da masu shirya fina-finan barkwanci, da su shirya sabuwar waƙa akan Nijeriya, sannan kuma waƙar bata buƙatar nuna ƙabilanci, abinda ake buƙata ga duk wanda zai yi waƙar shine, ya waƙe ƙasar Nijeriya, domin ba a buƙatar ya sanya sunan wani acikin waƙar koda kuwa mawaƙi Rarara ne.


TSARIN KYAUTUTTUKAN GASAR


Duk wanda yazo na ɗaya, zai samu kyautar Mota


Duk wanda yazo na biyu, zai samu kyautar Adai-daita Sahu (Keke Mai Ƙafafu Uku/Keke Napep)


Duk wanda ya zo na uku, zai samu kyautar mashin


Mafi ƙarancin abinda mutum zai iya samu a gasar shine kyautar ₦150,000


Lura: Kai ne zaka yi waƙar, ba kamar yadda a baya, kowa ya sani cewa wanda ya sanya gasar shine zai bayar da waƙar da za a hau kai, amma wannan gasar ta bambanta da sauran, dole kaine zaka tsara waƙar, sannan kuma ka rera waƙar da kanka, a taƙaice dai ba waƙar Rarara bace.


DOMIN TUNTUƁAR MAWAƘI


Zaku iya samun shi a:


A Youtube Channel: Dauda Kahutu Rarara


A Instagram: Real Dauda Kahutu Rarara


A adireshin ɗin email: kahutudauda@gmail.com


Abinda ya ƙara birge mutane dangane da wannan gasar shine kowanne mawaƙi zai iya shiga cikin gasar kama daga Mawaƙan Hausa, Gargajiya, Gambara da sauransu


Allah ya ba mai rabo sa'a Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user