Tuesday 27 October 2020

Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya (01)

Tura Wannan Zuwa

Zai yi matuƙar wahala mutum ya iya tantance haƙiƙanin ma'anar soyayya, don takan canja ta ɗauki surori daban-daban da launuka mabambanta gwargwadon mutanen da suke yin ta, akwai buƙatar kallon zamani: Ba dole ba ne soyayyar da aka yi ta a shekara hamsin ta zama ita ake yi a yau,  Wuri: Irin soyayyar da ake yi a ƙasar Turai takan bambanta da wace Larabawa da mu baƙaƙe muke yi.


Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya

MarubuciBaban Manar Alkasim


Shekara: Manyan mutane da matasan da suke tasowa kowa da yadda yake nuna ƙaunarsa ga masoyinsa, dattijo ba zai sauko ya zama yaro ƙarami ba, ba ruwan soyayya da tsufa, amma akwai ƙaruwar hankali da sanin ya-kamata, Wadata da rashi: In mai wadata zai nuna ƙaunarsa ga masoyiyarsa yana da hanyoyin da yake bi, masamman wajen yin amfani da abin da yake hannunsa wajen zaɓen inda za a je, da inda za a zauna, da abin da za a ci.


Aure: Akwai cikakken 'yanci wajen yin amfani da duk wasu lafazozi, da yin aiki da duk wata gaɓa don nuna soyayya, ga cikakkiyar hidima don jin daɗin masoyi, wannan bai samuwa a samartaka zalla ba tare da aure ba, Ilimi da jahilci: Wanda ya yi karatu ya haɗu da jama'a daban-daban masu sifar rayuwa mabambanta gami da cakuɗa da fahimtar Turawa, dole tsarin soyayyarsa da mace ya bambanta da wanda bai je makaranta ba, to kafin mutum ya tantance ma'anar soyayya yana da buƙatar ya kalli ƙusurwoyi da dama, gami da nazari kan bambance-bambancen matattaran jama'a da addinansu.


Annabi (S.A.W) yana cewa: Ɗayanku ba zai yi imani ba har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa. Haka ƙauna take, duk wani mai yin magana a kan soyayya za ka ji ya ƙare kan musayar ƙauna ta kowace sifa, in mace za ta fito da zuciyarta gaba ɗaya ta danƙa wa namiji, to lallai akwai buƙatar shi ma ya yanke hannayensa ya miƙa ma ta, soyayya a taƙaice hidima ce ta zuciya da sauran gaɓoɓi ba tare da sauraron godiya ko tukwici ba, aiki take sanyawa tuƙuru na taimakawa, tausayawa, tausasawa da ba da kariya, kenan ba kamar yadda ake rayawa cewa tana hana ganin laifi ba, takan yi ƙoƙarin maganin laifin ne kafin ya auku, in ya bayyana kuma ta yi ƙoƙarin gyarawa ba lulluɓewa ba.


Ba yadda za a yi soyayya ta zama wata hanya ta biyan buƙatar wani shi kaɗai, ko ta taƙaitu da amfanuwa da abin da yake hannun wani, shi ya sa ma Annabi (S.A.W) ya ce: Ka guji abin hannun mutane sai su ma su so ka. In ƙauna ta taƙaita da zuciya sai ta koma sha'awa, wace take kamar wutar kara mai balbala da macewa a ɗan lokaci kaɗan, shi ya sa in mutum ya yi nazari mai zurfi zai fahimci shawarar da Annabi (SAW) ya bai wa masoya wajen zaɓen abokin rayuwa, sai ya lissafo abubuwan da galibi su suke ɗaukar hankalin mutum wajen zaɓen abokin rayuwa.


In mace tana da dukiya tabbas za a yi sha'awar aurenta don abin hannunta, haka in mutum yana da hali bai rasa samun wace zai zauna da ita komai muninsa, kenan zancen kuɗi ake yi, ba kuma hanyar da za a fassara kwaɗayi da soyayya, don zancen ya kasu biyu, ko dai ƙaunar mutum ko ƙaunar abin hannunsa, in dai za a yi zancen ƙaunar mutum to ko kaɗan ba za a duba cewa yana da hali ko bai da shi ba, bare a tambaye shi aikinsa da irin gidan da zai zauna, da matsayin danginsa a gwamnatance, ƙauna tana tsakanin zuciya ne da gaɓoɓi, ba ta ƙetare zuwa sutura ba bare a yi maganar aljihu.


In mutum zai nemi mace mai arziƙi, to tun farko kar ya yi zancen musayar motsin zuciya, ko ta yi masa hidimar yau da kullum, bare kuma 'yan uwansa gami da iyaye, yana iya miƙa wuyarsa in bai da buƙatar komai daga gare ta, a nan kuma ba mai iya kawo zancen soyayya, haka ko shi namiji in dai za a gwamatse shi don abin hannunsa shi kansa ya sani, zai yi wahala ya manta wahalhalun da ya yi kafin ya mallake ta, to duk wanda bai wuce ga-shi ba, to lallai bai fi ƙarfin wulaƙanci ba, da yawa wasu sai dai su turo mata abubuwan sawwaƙe rayuwa, ko su ajiye saduwar dare a matsayin hanyar nuna soyayya, tabbas waɗannan sun yi hidimar badawa, amma zuciya ba ta yi aiki ba.


Daga yanzu za mu fara tunanin ko kallo ɗaya zai iya sanyawa ka ƙaunaci mutum, ka iya kasadar miƙa masa rayuwarka har abada, ka ba shi amanar jin daɗinka na dindindin, da sakankancewa da cewa ba zai cutar da kai ba, kuma ba zai yarda da duk wani abin da zai cutar da kai ba ƙarami ne shi ko babba, ka tabbatar da cewa komai kake biɗa na duniya da shiriyar lahira za ka iya samu a hannunsa, tabbas daga Mace ta yi ado ba za a iya gane hakan zai samu ba, haka daga Namiji ya sami kuɗi ba zai yuwu a sakar masa jiki ba.


Hanyoyin da za a bi don cinma soyayya ta gaskiya, da samun abokin rayuwa na ƙwarai, da juya tunanin masoyi gami da toshe ɓarakar da take fatattakar alaƙoƙin masoya da ma'aurata su ne za su zama mana tafarki a wannan sabon shirin da yardar Allah.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user