Tuesday 20 October 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (26) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

KAI NE FARKO


In har za mu nemo hanyar cin nasara a rayuwa kai ne farko, domin kai ne za ka fara laluben inda take ka hau hanyar nemanta, wasu cikinmu suna ganin cewa in ka ji ana maganar nasara to a neman aure ne ko wasan motsa jiki, tabbas an fi samun nasara idan akwai gasa, amma wace gasa ce ta wuce mutum ya sami abinda yake so a rayuwa? Duk masu ƙoƙarin cin nasarannan da kake ji kowa haƙilonsa shi ne ya sami abinda yake so a rayuwa, na zauna da wanda bai da wani zance sai ya zama mai kuɗi, ma'aikacin gwamnati ne, ya ƙi komawa makaranta ya ƙaro karatu, arziƙin mahaifinsa ya karye bare a yi maganar gado, baida sana'a bare mu ga nau'in sana'ar da kuma gudunta wurin isa ga nasarar da yake nema.


MATAKIN FARKO

MarubuciBaban Manar Alkasim


Akwai ƙananan sana'o'i waɗanda masu kuɗin mu na yau duk sun yi su, amma sun yi sana'o'i da yawa a bayansu, na ga wani mai arziƙi aka ce wanki-da-guga ne silar arziƙinsa, da na bincika sai na ji ya yi wasu sana'o'in barkatai a tsakiya, na ga wani matashin dakta a ilimi da na tambaye shi yadda aka yi ya isa wannan matsayin, sai ya fara ba ni tarihinsa wanda na ji har ƙasashen maƙwabtammu ya zaga don neman nasara a rayuwa, ya sheda min cewa burodi yake sari yana sayarwa, ya yi wasu sana'o'in kafin ya dawo ya riƙi karatun da yake dogoro a kansa yanzu.


Kai dai ka lura wace sana'a ce za ka fara don ta zama maka gada wurin isa inda nasara take? In ka tara masu kuɗi kowa za ka ji hanyar arziƙinsa daban ce, akwai shahararrun mawaƙa da na gani suka ce daga almajirci suka zarce, ka ga dai kamata ya yi a ce sun zama malaman Qur'ani, to ba su kaɗai ba, na ma ga wasu masu abin hannunsu, arziƙi ya kankama kuma suka ce daga almajirci suka fara, kowa kuma ya san almajirci ba sana'a ba ne bare a fara tunanin yana kawo arziƙi ko bai kawowa, uwayensu kan turo su ne sai yadda hali ya yi, ko karatu ko wani abin, duk abinda yaro ya fara buɗe ido da shi to shi ne zai zama mafarin tafiyarsa da zai riƙa takawa yana hango nasara da shi.


1. Yanzu dai a matakin farko ka fara amincewa kana son ka dogara da kanka, ba wai jira kake a raba gado ka samu a sama ba, ko hakan ne ma ka sani in har aka ba ka kasonka dole ka riƙa ririta shi kana ƙara yawansa, ƙoƙarin da za ka yi wurin ba wa dukiyar kariya ta rurin ƙara yawanta ya fi wanda za ka yi a lokacin da kake neman na kanka wahala, don haka yi ƙoƙari ka kama sana'a, fitar da burin cewa za ka gaji kuɗi, ko tsammanin wani zai taimake ka, yi ƙoƙari neman na kanka ya zama maka jiki kafin ka riƙe wata dukiya da za ta shigo maka daga baya, da za ka riƙe kantinka da ka haɓɓaka shi cikin shekara goma sha bakwai, ka miƙa shi ga wanda mai san kan sana'ar ba, ka ba shi shekara ɗaya tal ka dawo ka ga inda ya kai.


Yi ƙoƙari ka gano inda ka fi rauni, in ba ka son abokanka su riƙa ganinka kana ƙananan sana'o'i to ka nemi irin sana'ar da za ka zauna wuri guda kamar tela, tsaron kanti da sauransu, kar ka ɗauki kabu-kabu ko yaron mota ko sayar da gwanjo wuri-wuri, ka amince wa kanka tabbas kana son sana'ar, kuma za ka iya yin alfahari da shi a ko'ina ne, in mace ce kake nema ka gamsar da zuciyarka cewa da sana'ar za ka ciyar da ita, daganan sai tsarin yadda za ka tafiyar da sana'ar ba tare da tsoron komai ko kowa ba.


In ka fara sana'ar za ka ga wasu matsaloli a tsakiya kar ka damu, ka sami ƙarfin gwiwa kawai, ina yaro na yi sha'awar bara yadda na ga sa'o'ina yara suna neman na kansu kuma suna iya yi wa kawunansu wasu abubuwan duk da cewa suna nesa da mahaifansu, mu kuwa muna gaban uwayen ba iya tsinana komai, ranar farko da na fita aka kama ni a gida na ji jiki, bayan wasu lukuta kuma na yanke shawarar zama yaron mota, har na sami wanda zan riƙa bi, amma da yaron gidansa ya zo haka ya ce min na sauka, daganan na karaya na koma gida, banda wannan ma na taɓa zuwa gona na siyo rake na je kasuwa, don in sayar in sami na rufin asiri, amma ni da kaina na saka rakennan a gaba na shanye kayana, wanda na sayar kuma na cinye kuɗin, shi ma dai ban ci nasara ba.


Bayan na ƙara wasu 'yan shekaru sai na fahimci da a ce na sauko da kaina ƙasa na bi ɗayan abokaina da yake ɗayan sana'o'in da na yi ɗin nan, na koyi aikin sosai, na kuma san yadda zan yi manejin rayuwa ƙila da hakan bai faru ba, amma duk da haka na gode wa Allah, domin na yi karatun rayuwa, wajen faɗii tashina na sami wurin da na maƙale har na kawo matsayin da nake ciki yanzu, akwai wani yaro da ya yi rayuwa kusan irin tawa amma ya fi ni natsuwa, ban san sana'o'in da ya yi a baya ba, amma na fara ganinsa da 'yan faya-fayen bidiyo na wasan Hausa yana yawo da shi, da yake yana samun ciniki a kasuwar unguwarmu sai ya yi wani ɗan shago ɗan mitsili wanda ko shi bai iya shiga, sai dai ya jera faya-fayen in za a saya ya ciro wa mutum ya ba shi.


MAKALOLI MASU ALAKA:


Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (23) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (24) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (25) Cikin Sauki


A hankali ya fara kawo man shafawa da 'yan turarurrukan mata yana sayarwa, maganar da muke yi, ya kama shago a ɗaya hannun ya maƙare shi da nau'ukan turare, yana kan hanyar nasara, akwai wata mata da na san ta auri wani mutum, mu a waje muna kallon soyayyar da suke sha kuma suna burge mu, amma a cikin gida auren na lilo yana ƙoƙarin ɓalgacewa, ba abinda ta rasa na ci da sha da sutura, kuɗi kuma sai dai ta ba wasu, komai take so gashinan, sai dai tana da matsalar shimfiɗa, 'yan uwanta ba su ganin wannan wani abu ne, na ce ita ce da kanta za ta fara nemo wa kanta hanyar nasara.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user