Sunday 13 September 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (24) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
AIKIN KA

Za mu iya kasa ƙananan ma'aikata zuwa gida biyu, akwai waɗanda suke aiki don neman abin sakawa a bakin salati, da kuma waɗanda suke yi don tsare dukiya ko tarata, manufar kowa game da aikin akwai bambanci, dagewa da mai da hankali wurin wanda yake aiki don neman abinci bai kai kamar mai yi don tara dukiya ba, shi ya sa ko kyauta za a yi sai ka ga bambanci a tsakaninsu, na taɓa jin wani babban mutum da na san yana da wani babban kamfani yana ta bala'i a kan Naira hamsin, ya ce in mai kayan ba zai sayar a Naira 500 ba a dawo masa da kudinsa, don me za a ƙara masa Naira 50?

Hanyoyin Samun Nasara

MarubuciBaban Manar Alkasim

Babban abinda ya kamata mutum ya tsare shi ne aiki koda ba nasa ba ne, kwanan nan nake ji wani asibiti sun ɗauki wata ɗaliba daga gwaji saboda tsabar hazaƙarta da dagewarta, na ga wasu lakcarori su ma an ɗauke su saboda hazaƙarsu a ɗakin karatu, suna gamawa aka ɗauke su aiki, a duk lokacin da kake aiki ana kallonka, kar ka ce don ba naka ba ne ba za ka wahala ba, in ma naka ɗin ne jajurcewarka wani babban jigo ce da za ta taimaka maka wurin ganin ka isa inda ake buƙata.

Ba wani ma'aikaci wanda bai sha wahala ba kafin ya kai ga gaci, bari mu dubo wasu 'yan abubuwa ko na ce sharuɗɗa waɗanda su ne ginshiƙan cin nasara musamman a rayuwarmu ta baya-bayannan, duk wani ma'aikaci yana da kyau ya sani cewa ba wani aiki a duniya wanda ake faɗo masa ta sama, komai yana da farko, in ba ka sani ba kuma kana son cin nasara to ka nemi a nuna maka a matsayinka na sabon ma'aikaci, kar ka yi girman kai, alamun ka shirya aikin kenan, in mutum na neman aiki zai jigata, in ya samu bai nufin yanzu hutu sai ya naɗe hannu ya ci arziƙi, yanzu ya kamata ya fara aiki.

Samunka da aiki yana nuna cewa aikin ma ya same ka, in kai ne mai wurin sai ka yi tsayuwar daka wurin ganin ya haɓaka, kar ka yi zaton shikenan yanzu hutu ya zo, idan kana zama wa wani a kantinsa ne sai yau ya yaye ka, ya buɗe maka wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan kanti kar ka ce "Yauwa 'yanci ya zo, na farko dai sai lokacin da na fito kuma ina da zaɓi a lokacin da zan koma gida, zan ci abinda nake so, kuɗin duk da na samu nawa ne sai yadda na yi da su, in ka yi hakan haƙiƙa ka yi gaggawa, da ɗan sauran tafiya a gabanka.

Wannan wata gada ce da ka tsallake daga dukiyar wanizuwa taka, lokacin da aka mallaka  maka kuɗin gado bayan da kana fama da talauci kar ka taɓa zaton ka haye, gada ka samu, in ka taka a hankali ka haye, in ka yi gaggawa ka auka ciki, kuɗin ko shagon da aka ba ka asali na wani ne, za ka ɗan ɗauki lokaci kafin ka maida su naka, zan ba ka misali, wani lebura da ya yi aikin wuni tun da safe har maraice kafin ya sami 2,000 a matsayin ladar wahalarsa, kai kuma ka yi rakiya ne a ka miƙo maka wannan kuɗin, cikin sauƙi za ka ce a zare maka tsire na ɗari biyar, shi kuwa ba zai sha wahala tun safe ya kashe ɗari biyar a kan tsire kacal ba, wanda ya buɗe shago ya ce ya zama naka, ku ka sami gado, ko ka zama shugaban ƙaramar hukuma ko kansila za ka ɗan ɗauki lokaci kafin ka maida kuɗin naka, in ɗan siyasa ne ƙila sai ya sauka gaba ɗaya kuɗin sun girgiza kafin ya fara jin cewa nasa ne.

Gaggawa ce ke damun mutanenmu, na san wanda ya gaji miliyoyi yanzu ya koma abin tausayi kamar ba shi ne jiya yake fantamawarsa ba, na ga wani ɗan siyasa wanda ya sami kuɗi ya yi gidaje ya mallaki kadarori da dama, yanzu ko gidan kansa bai da shi, wani ma gidan ma ya raba biyu ne ya sayar da rabi yadda zai samu ya iya ririta rayuwar, wani bawan Allah ya yi ritaya aka ba shi kuɗinsa tsibi a hannunsa, ya sami wasu bayin Allah suka ba shi shawarar cewa ya yi shago don kar kuɗin su ƙare a banza, ya karɓi shawararsu ya fasa ɗaki ɗaya daga cikin ɗakunansa ya mai da shi shago, ya maƙare shi da kaya, kusan komai kake so yana da shi, yanzu aiki ya kamata ya fara tuƙuru, don ya tabbatar da nasarar da yake ganin ya samu.

Sai ya yi kuskure, ba ya iya futowa shagon sai rana ta raba, kafin taran dare kuma ya rufe, sai mutane su zo sayen kaya ba shi, in an aika masa ya ce ba zai fito ba, aka yi ta kukan hakan har aka gaji aka fita harkarsa, da dai ya ga kamar abubuwa na ɗan ja baya sai ya ɗauki ma'aikaci, shi ma bai zaɓo ƙwararre ba, ya haɗa irin tarhon kusa ɗin nan, in an zo sayen kaya sai a buga masa ya faɗi kuɗin, shi ba zai iya zama a shagon ba ya zama babba, ba a jima shagon ya lalace aka rufe shi gaba ɗaya ya koma ɗakin kwana, na ce ya yi gaggawa ne, na san wanda ya tarairayi abinda ke hannunsa yanzu ana ganinsa a matsayin mai isasshen jari.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (21) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (22) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (23) Cikin Sauki

Idan ka sami jari a rana guda na tsabar kuɗi waɗanda ba ka zata ba, yi ƙoƙari ka zuba su a banki ka manta da su, ka dawo ka fara neman abinda ranka ya natsu da shi kuma yanayin da ake ciki ya karɓa, sannan ka zauna da waɗanda ke cikin harkar ka gani kuma ka tambayi fa'idoji da matsalolin dake cikin harkar, sannan ka ƙimanta masaniyarka da ƙoƙarin Ka in zai yuwu ka shiga, sai ka ajiye cewa yanzu ne za ka fara neman nasara ba wai da samun wannan kuɗin har ka cimmata ne ba, sai ka sanya Allah a gaba ka yi ta roƙon ya ci gaba da agaza maka kamar yada ka faro tun farko.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user