Thursday 12 November 2020

Abinda Yake Faruwa Dakai A Lokacin Daka Kwanta Bacci Da Music Batare Daka Sani Ba

Tura Wannan Zuwa

Babu wanda zai baka mamaki da tausayi fiye da wanda kafin yayi barci sai ya kunna kiɗa. 


GAYU, A DAINA YIN BARCI DA KIƊA KO WAƘA


Marubuci:- Ibrahiym A. El-Caleel


Barci yana kusanto da bawa ga mutuwa ne. In banda abinka gaye, mene ne amfanin gayyato sheɗanu a lokacin da kake kusantar mutuwa? 


Cikin Suratul Zumar, Allah (S.W.T) yace: 


اللَّهُ يَتَوَفَّى الْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَالَّتِي لَمْ تَمُتْ فِي مَنَامِهَا فَيُمْسِكُ الَّتِي قَضَى عَلَيْهَا الْمَوْتَ وَيُرْسِلُ الْأُخْرَى إِلَى أَجَلٍ مُّسَمًّى إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ


“Allah ne wanda ke karɓan rayuka a lokacin mutuwar su, da waɗanda basu mutu ba a cikin barcin su. Sai ya riƙe wanda ya hukunta mutuwa akan sa, kuma ya saki ɗayan zuwa ga ajali ambatacce. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu hankali."


Malaman Tafsiri a nan suka ce Allah ya kan zare ran ɗan Adam a lokacin da yake barci. Sai dai zarewar ba zarewa bane na gaba ɗaya kamar yadda ake yi lokacin mutuwa. Zarewa ne wanda yake za'a bar wani ɓangare na rai ɗin yana ittiṣali da jikin mutum ittiṣali wanda yake ba sosai ba. Domin haka ne mutum za ka ga yana barci yana numfashi, amman kuma fa a lokacin shi bai san halin da yake ciki ba. Don haka idan Allah ya ƙaddarawa mutum mutuwa a cikin wannan barcin, kawai sai dai a dakatar da numfashin. Shikenan labari ya canza. Mutum ya bar duniyar nan. Ɗan Adam ba a bakin komai yake ba! 


Sahabi Abu Juhaifah (RA) yace wata rana Annabi (S.A.W) yana cikin wata tafiya haka wacce sukayi barci har rana ta fito. Sai Annabi (S.A.W) yace: 


إِنَّكُمْ كُنْتُمْ أَمْوَاتًا فَرَدَّ اللَّهُ إِلَيْكُمْ أَرْوَاحَكُمْ ، فَمَنْ نَامَ عَنْ صَلاةٍ فَلْيُصَلِّهَا إِذَا اسْتَيْقَظَ ، وَمَنْ نَسِيَ صَلاةً فَلْيُصَلِّ إِذَا ذَكَرَ


"Tabbas kun kasance matattu, sai Allah ya dawo muku da rayukan ku. Don haka duk wanda ya san sallah ta kuɓuce masa saboda barci, to sai ya sallace ta idan ya farka. Wanda kuma ta kuɓuce masa saboda mantuwa, to ya sallace ta idan ya tuna". 


Ingantaccen hadisine wanda Abu-Ya'ala ya ruwaito cikin Al-Musnad


Waɗannan duk suna nuna cewa rai ya kan fita a lokacin da muka kwanta barci. Idan ajalin mu bai riga yayi ba, sai Allah ya dawo mana da ran. Idan kuwa ajali yayi, shi kenan sai shirye-shiryen jana'iza kuma. 


Amman duk da haka shi gaye babu ruwan shi. Madadin ya kwanta yana mai kusantar Ubangijin sa da addu'o'i da zikirai da tadabburin ayoyin Qur'ani waɗanda zasu tausasa mishi zuciya, a'a sai ka ga yana gayyato sheɗanu ta hanyar kunna music da sauran waƙe-waƙe da raye-raye da sauran iskanci iri-iri. 


Barci da music muguwar ɗabi'a ce ga duk mutumin da yake taka tsan-tsan da duniyar nan, yake da yaƙinin a kowani lokaci za ta iya kuɓuce mishi. Yana da kyau abokan mu gayu su gyara wannan ɗabi'a.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user