Tuesday 10 November 2020

Wasiyyar Aisha Dan Kano Kafin Ta Rasu

Tura Wannan Zuwa Ga

Kafin ta rasu ta roki duk wanda ta ɓatawaya gafarta mata saboda Annabi (S.A.W)


Yayin Karɓar Kyautar Girmamawa


Ga kaɗan daga wasiyyar AISHA DAN KANO
ga alummar manzon Allah da mu abokan
aikin ta.


1. Idan na mutu kada ku bari na kwana.


2. Dan Allah yusif Magarya kagayawa
mutanen office ɗin ka da ragowar abokanan sana'aa duk wanda na ɓatawa ya yafeni.


3. AISHA ƊAN KANO ta haɗu da wani
producer me suna NURA MANAJA bayan sun sami matsala da shi har basa magana amma ta janyo shi ta ce ni AISHA ƊAN KANO bana gaba mu yafewa juna.


ALLAHU AKBAR ranar talata da yamma ranar da munafiki baya mutuwa da yamma Allah ya karɓeta.


Abin lura game da rayuwar AISHA ƊAN KANO tana da tsananin ƙaunar Manzon Allah (S.A.W) fiye da kima duk abinda ya haɗaka da  ita in har ka  haɗa ta da shugaba ta haƙura ni shaidane kuma wallahi bata munafinci gata
da fara'a.


Yau sama da shekaru uku da rasuwar jarumar.


Allah muna roƙon Ka gafarta mata ka yafe
mata ka haɗata da Manzon Allah da duk
al'ummar Annabi (S.A.W).


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: Mujallar Mu
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user