Tuesday 10 November 2020

Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya (02)

Tura Wannan Zuwa

Soyayya ta gaskiya tana nufin saduwa ne da juna a jiki da zuciya, ta yadda masoyi zai yi ta fatan a jingina shi da masoyinsa, in a ka ce wane masoyinka ne, daɗi za ka ji ko da ma tsokanarka aka yi, sam ba za ka ji zafi ba bare kuma ka hasala, don an kai matsayin da kake jin masoyinka tamkar rabin jikinka, ba ka ƙaunar baƙin cikinsa kamar yadda ba ka fatan damuwarsa, lokacinka, kuɗinka, hidimarka, jikinka da duk wani abu da ka mallaka na ka ne matuƙar bai buƙata ba, ba ka damu ka sha maɗaci ba matuƙar shi zai ji zaƙin zuma, kuma za ka iya yin kuka don dai ka ga dariyarsa.


Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya


MarubuciBaban Manar Alkasim


Masoyi shiri ake yi masa na taimako ta kowace sifa, ta yadda za ka gyara komai na ka dominsa, sannan ka yi tattalinsa da 'ya'yansa da duk wanda ya jiɓance shi, ka ƙarfafa zumuntarsa, ka kare mutuncinsa da sunansa, ka tsaya tsakaninsa da duk abin da zai iya jefa shi cikin damuwa ko tashin hankali, ka kwaɗaitar da shi a kan duk wani abu da addini ya kwaɗaitar, ko ya wajabta a yi, ba shakka wannan abu ne mai tsada, wanda yake buƙatar kula da shiri na tsawon lokaci, ba yadda za a yi daga kallo ɗaya a sami lamunin komai, sannan yawan zama da namiji ko mace don hira, ko adon mace da abin hannun namiji ba su suke ba da wannan amincin ba, binciken ɗabi'ar mutum da tarbiyya ta ƙwarai su suke tabbatar da dauwamammiyar soyayya.


Idan mu kasa nau'o'in soyayya da ƙauna ne, haƙiƙa za mu iya kasawa har gida Bakwai, wasu sukan taru wa mutum guda, sai ka ga ya iya musayar soyayya kamar yadda ake buƙata, duk yadda aka rasa wani sai ka ga soyayyar ta ragu, kenan kowa bai rasa ƙauna da soyayya a tare da shi, sai dai kuma da fuskar da yake fassarawa ne, in abokin soyayyar ya ga bai samun damar yin musaya ta ɗaya daga cikin ɓangarorinta sai ka ga ya damu, shi ma sai ya sami rauni ta wasu ɓangarorin.


Daga cikin rabe-raben soyayya akwai:-


1. Kauna ta sha'awa: Wannan tana iya samuwa ne daga kallon fari, tsarin halitta, ko kyawun ado da iya wanka, ko shaharar namiji da abin hannunsa, ko ma iya zance da lallaɓa, galibin irin wannan ƙaunar ana ganinta a fina-finai da sauran littafan soyayya, takan yi ƙarfin da ba a taɓa zato ba, ta burge kowa da kowa, masamman ta fuskar yadda ake gudanar da ita, sai dai da zarar an kawar da sha'awar shi kenan ta tafi, sai kuma zaman haƙuri, irin wannan soyayyar ita ce iyayemmu suke tsokaci a kai da cewa: Da zarar an yi aure ta ƙare sai kuma zaman haƙuri.


2. Wata soyayyar tabbas akwaita amma tana da alaƙa ne da haihuwa da ƙaunar zama uwa ko uba, wato dai buƙatar namiji a ce masa Baba, ko mace a ce ma ta Mama, masamman in tsararraki sun sami gidajensu na kansu, an fara lissafin cewa wane 'ya'yansa kaza, ko wance 'ya'yanta kaza, in irin wannan soyayya ta maƙure mutum takan yi masa illa, domin tana da ƙarfin da za ta sanya shi ya ɗauki kowani irin mutum, koda bai dace a rayu da shi ba, ita kam ana iya jure ma ta, amma ba dole ba ne a sami musayar motsin rai da faranta wa juna.


An yi wasu bayin Allah da suka so junansu amma Allah Bai ba su haihuwa ba, ganin halin da uwargidan ta fara shiga, sai maigidan ya ba da shawarar cewa su auro wata wace za ta hayayyafa musu, amma komai za su kasance kamar yadda suke, Allah ne dai mafi sanin gaskiya, maigidan ya musuluntar da wata, ya kuma aura, har ta haifa masa 'ya'ya biyu, sai mai rabo ya raba su, uwargidar ta kwashe 'ya'yan da hujjar cewa ba za a kai musu ɗiyoyi inda babu musulunci ba, a taƙaice dai amaryar ta bar gidan na tsawon lokaci ba ta yi aure ba, kuma tsohon maigidan na ta yake ɗaukar nauyinta.


MAKALOLI MASU ALAKA:


Bambanci Tsakanin Sha'awa Da Soyayya (1)


Karanta Alamomin Gane Masoyi Na Gaskiya


Tsakanin So Da Soyayya (1)


3. Sai kuma soyayya ta gaskiya, wannan ba ta furuwa lokaci guda, wai daga zarar ka ga mutum shi kenan kuma ya zama masoyi, wai har kana iya faɗawa rijiya a dalilin raba ka da shi, ka zagi kowa ka saɓa wa iyaye a dalilinsa, soyayya ta gaskiya cike take da tsarin da matattara ta shirya, addini kuma ya tanadar, iyaye sukan ba da gagarumar gudummuwa wajen tabbatar da ita, addini kuma ya yi wa mutum seti ya nuna masa abubuwan da suka dace da waɗanda dole ya rabu da su don samun natsuwa da ɗan uwansa masoyi, wannan tarbiyar mutum take sakawa ya gwanance wajen zama tamkar masoyinsa a lokacin da yake gida ko lokacin da baya nan.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user