Friday 4 September 2020

Tsakanin So Da Soyayya (01)

Tura Wannan Zuwa Ga
Ana ta ƙoƙarin rarrabe ma'anonin kalmar (so) da ta (ƙauna), duk da cewa su biyu ɗin suna yin aiki ne iri guda, kuma ta kowa ce fuska, a kowani irin yanayi, maza da mata, yaro da babba kowa yana iya juya kalmomin yadda yake so, tamkar yadda suke a tsakanin masoya guda biyu, inda a nan ne ma suka fi shahara.

TSAKANIN SO DA SOYAYYA

MarubuciBaban Manar Alkasim

Kalmar (so) tana matsayin {suna} ne, wato kamar ka ce " In da SO da ƙauna", takan tsaya kuma a matsayin (aikatau) ma, kamar ka ce " Ai kuwa ya SO ta tsakani da Allah" ita ma {ƙauna} takan tsaya a matsayin (suna) misali: " Wato ita ƘAUNA ta gaskiya ba ruwanta da bin diddigin arziƙin mutum" sannan takan iya zama (aikatau) ma, misali " In kana ƙauna ta sabo da Allah ne, to ka zo gidammu, kuma da rana"

Kenan in muka lura da waɗannan kalmomi guda biyu, (so da ƙauna) za mu gano wata hikima a cikin maganar mai-girma Ado Ahmad, Gidan Dabino, da ya sanya wa littafinsa na farko da ya yi fice, wato "In da So da Ƙauna", kamar dai yana nufin, inda duk so yake ne ƙauna ma tana nan, haka in da duk ƙauna take so yana nan, a taƙaice dai abu guda ne, kamar ka ce "Ina son ki" ko ka ce "Ina ƙaunar ki" ko ka faɗi ta wata hanyar "Sonta yake" wato "Ƙaunarta yake" ta wannan ɓangare ba sai mun wahalar da kammu wai ala tilas sai mun rarrabe ma'anonin kalmomin biyu ba, in muka ɗauki ɗaya ma ta wadatar.

So, kamar yadda muka sani, wani motsi ne da yake tattare da halittu masu yaɗuwa ta fuskar saduwar ɗa namiji da 'ya mace, kenan za mu iya iyakance shi da wanzuwa tsakanin Mutane, Aljanu, dabbobi,  da sauran halittu irin su: Ƙururai, tsutsotsi da nau'o'in tsuntsaye da ma halittun ruwa.

Kalmar "so" kalma ce da ta ƙumshi tausayi da ruhin taimako, don haka tana iya aukuwa a ɓangaren jinsi guda, wato maza zalla ko mata zalla, kamar yadda takan kuɗaɗa tsakanin iyaye da 'ya'yayensu ko malamai da almajiransu, ko ma 'yan uwa na nesa da na kusa.

MAKALOLI MASU ALAKA:In har za a kalli kalmar so da irin idanun da ya kamata, tabbas za mu fahimci cewa, ba a iya fassara ta, sai an kalli abin da ke tsakanin mai yin ta da kuma wanda ake yi masa, akan sami musayarta, wani lokaci takan zo a ɓangare guda, sannan akwai ta gaskiya akwai kuma ta ƙarya, kowacce a tsakanin waɗannan tana da iyaka kuma ana iya gane ta. Ku biyo ni.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user