Wednesday 2 September 2020

Shin Dagaske Ne An Yiwa Su Rarara Da Ali Nuhu Ihun Bamayi A Jihar Katsina?

Tura Wannan Zuwa Ga
Tun jiya da yamma na ke samun kiraye-kirayen waya don ji gaskiyar lamari akan abun da ya faru na jifar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, da su Ali Nuhu da ake ta yaɗawa a kafafen sadarwa na zamani.


Babu Wanda Ya Jefi Rarara Ko ALI Nuhu A Katsina

MarubuciIsah Bawa Doro

Ko da yake, na samu yi wa wasu daga cikin su bayani a taƙaice, wasu kuma ban samu damar ɗaukar wayar su ba sakamakon ayyuka da suka yi min yawa.

Ni ne mai taimakawa na musamman wurin samar da wuraren da aka yi aikin bidiyon waƙoƙin da Rarara ya zo yin aikin su. Hakan ya sa babu wani wuri da ba da ni aka je ba a lokacin aikin na su, barci kawai ke raba ni da su.

Babu Wanda Ya Jefi Rarara Ko ALI Nuhu A Katsina

Na ga an yi rubuce-rubuce na ri-ga malam Masallaci, kowane mai shafin yanar gizo da irin salon kanun labarin shi. Hakan ya sa na ga ya dace da sanar da masu tambaya ta, da kuma  bibiya ta ainahin abun da ya faru.

A ranar Laraba ɗin ta gabata ne 19 ga watan nan na Agusta, mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya zo ya fara ɗaukar bidiyon waƙoƙin guda biyu da ya yi game da matsalar tsaro da ta ke addabar jihar Katsina. Waƙoƙin su ne 'Jihata-Jihata Ce, da kuma waƙar 'Masari Mai Hakuri'.

Babu Wanda Ya Jefi Rarara Ko ALI Nuhu A Katsina

Wuraren da aka ɗauki waƙoƙin sun haɗa da ɗakin taro na `Local Government Service Commission` da ke kusa da Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina. Sauran wuraren sun haɗa da Unguwar Kwado, kusa da masallacin dillali, akwai kuma Bakin ƙofar shigowa Katsina da ke Dandagoro, akwai kuma Gidan namun daji na 'Al-Dusar' da kuma bakin kasuwar `Central Market Katsina` dai-dai inda aka tada masu sayar da cefane, inda aka maida wurin ajiye motoci na masu shiga sayayya a kasuwar.

Inda ka cire ɗakin taro na `Local Government Service Commission` duk sauran wuraren da aka ɗauki waƙar ni ne na samar da su, kuma ni na yi magana da masu kula da wurin.

Babu Wanda Ya Jefi Rarara Ko ALI Nuhu A Katsina

Shi kan sa shugaban Ƙungiyar kasuwar ta Jihar Katsina, Alhaji Abbas Labaran Albaba, ni na kira shi ta waya tun da sanyin safiyar ranar Alhamis da misalin ƙarfe 8:50am na safe, na sanar da shi abun da za mu zo yi a kasuwar, kuma na yi masa cikakken bayani, daga ƙarshe ya yi mana fatan alheri.

A lokacin da ake aikin bidiyon waƙar mai suna Jihata-jihata Ce, wadda jarumi Ali Nuhu ke bada umarni, aƙalla an samu mutane sama da 500 waɗanda suka zagaye mu suna kallon aikin. Duk kusan lokacin da za a ɗan dakata, Ali Nuhu da Rarara su kan koma mota domin sararawa, inda 'yan jagaliya ke daddafe motar su suna neman a ba su kuɗi.

Babu Wanda Ya Jefi Rarara Ko ALI Nuhu A Katsina

Duk waɗanda za su zo, Rarara ya kan basu daga naira dubu biyar abin da ya yi sama. Kafin a gama aikin waƙar ya raba kuɗi sama da naira dubu ɗari. Sai ya gama da wasu, sai kuma wasu su zo, da kunnena na ji waɗanda suka koma gefe suna kiran 'yan uwan su ta waya, akan su zo su karɓi rabon su a wurin na Kahutu.

Shi kuma da ya lura lamarin na su ba mai ƙarewa ba ne, duk waɗanda su ka zo, sai yace masu ya riga ya gama bada kuɗi, sai su ce ai ba su yaba ba, su yanzu suka zo. Hakan ya sa ya daina ba kowa kuɗi.

Wannan rabon kuɗin da ya daina, shi ya fusata wasu 'yan jagaliyar waɗanda ba su samu kuɗi ba, da waɗanda suka zo daga baya, suka riƙa dabaibaye motar sa, har aka kammala aikin shi da Ali Nuhu lami-lafiya suka fita daga kasuwar suka koma masaukin su wato 'Katsina Motel' har saida masu gadin Rarara, su Tijjani Asase, Baba Ali, Scorpion, su ka ga sun fice daga wurin sannan su ka shiga mota suka tafi.

Bayan sun bar wurin, sauran ma'aikatan da aka zo da su, waɗanda suka tsaya ɗaukar `Generator` da sauran kayan aiki, 'yan jagaliyar suka zagaye su suna cewa '' An ɗauko 'yan iska da karuwai daga Kano an kwashe dukiyar jiha an ba su".

Babu Wanda Ya Jefi Rarara Ko ALI Nuhu A Katsina

Waɗanda aka tafi aka bar su, sun haɗa da Furodusan waƙar wato Abubakar Bashir Mai Shadda,  Baballe Hayatu, Abubakar G. Boy, Kabiru Adebo, da sauran su, aka riƙa ce masu ba ma yi, ƙarya ne. Har kuma mu ka bar wurin babu wanda aka fasawa gilashin mota, ko kuma danjar mota, kamar yadda wasu ke bada rahoton karya.

Daga jiya zuwa yau na ga mabambantan labarai a wasu shafukan Facebook da YouTube, kowa na rubuta abin da ran sa ke so ba tare da ya yi bincike ta kowane ɓangare ba, kamar yadda yake a tsarin aikin jarida ba. Sannan duka a cikin labaran ban ga inda aka tuntuɓi wani daga cikin masu ruwa da tsaki a aikin ba.

Abun da ya bani mamaki shi ne irin yadda na ga wasu suna tura labarin ba tare da sun samu sahihancin abun da ya faru ba. Wata tambaya da na ke da ita daga ƙarshe ita ce, ace wurin da aka tara mutum sama da 500 kuma mafi yawancin su matasa, na san ba za a rasa aƙalla mutum 50 masu babbar waya, wadda za ta iya ɗaukar bidiyo ba. Na ga mutane da dama, suna ɗaukar bidiyon waƙar, amma me ya sa ba a samu waɗanda suka ɗauki bidiyon jifar ko kuma bugun kawo wuƙar da wasu ke rubutawa ba.

Har na gama bincikena a  shafukan da su ka yi rubutun da kuma YouTube, ban ga bidiyon fasa gilasan motar su Rarara da aka ce an yi ba.

Dan Allah a jama'a a rika bincike na musamman kafin a riƙa yaɗa labari, shi aikin Jarida ba aikin gaggawa ba ne, aiki ne da duk wanda ya ke yin shi, ake ma shi kallon mutum mai hankali.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user