Wednesday 2 December 2020

Tsakanin So Da Soyayya (05)

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan muka taƙaita "SOYAYYA" da cewa faɗin magana mai daɗi ne da kuma son juna a zuciya, sai mu ce tabbas akwai soyayya ta gaskiya kafin aure, amma abin da muke gani, in mutum yana da daduro, yakan yi ta tunaninta akoda yaushe, yana kuma son ganinta da zama tare da ita har ma da son kwanciya da ita, sai dai ba ya ƙaunar a ce ta zama matarsa balle a ce ita ce uwar 'ya'yansa, don ya ɗauke ta 'yar iska ce tamkar wace ta yi auren mutu'a, to a nan a iya cewa soyayyar gaskiya ce tun da ana buƙatar jin muryar juna, ko ganin juna, ko ma kwanciya da juna?


TSAKANIN SO DA SOYAYYA

MarubuciBaban Manar Alkasim


Soyayya ta gaskiya ta wuce wannan matsayin nesa ba kusa ba, don in fahimtar da aka yi mata ita ce saurayi kullum ya je zance ƙofar gidan budurwa, ya miƙa kuɗi lokacin da ake buƙata, ko kullum a raba dare ana surutu a waya da sauran hanyoyin sadarwa, to mazinata ma kamar yadda muka faɗi a baya, a iya cewa suna yin soyayyar gaskiya, don duk abin da aka lissafa a baya suna yi, ƙari ma har da saduwa.


A lokacin da mace take jin cewa duk wata gaɓa ta jikinta ta maigidanta ne, kuma a duk lokacin da yake so ba tare da jinkiri ko jayayya ba, ado da kwalliyarta duk nasa ne, ba ta faɗin wata kalma sai wace za ta faranta masa rai, ko wace ta yi dai-dai da abin da yake so matuƙar ba ta saɓa wa shari'a ba.


Ta kasance koda yaushe fatan ta a ce ya ɗaukaka, sirrorinsa a rufe ne koda ya baƙanta mata, a shirye take ta dafa masa duk abin da ransa yake so, a lokacin da yake buƙata, matuƙar ba zai cutar da shi ba, duk wani abin da ransa yake so kai tsaye shi ne na ta in bai saɓa wa shari'a ba, zumuntarsa ita ce tata, in bai sadar ba ta matsa masa cikin lallami da dabara kamar na ta za a yi wa, ta tsaya sai ya taimaki iyayensa da 'yan uwansa, ta fito da kyawawan halinsa a gaban jama'a, ita ce shi a duk lokacin da baya nan, in ta ji an kira shi kafin ya waiga idonta ya kai wurin.


Duk abin da ransa ba ya so kafin ya yi magana an kawar da shi, abin da yake so kafin ya furta an kawo masa, in ya wuce lokacin da ya saba dawowa nan da nan ta fara neman dalili, tufafin da yake sakawa ta san su, kuma sai da ta tabbatar sun dace ya fita da su, in ya dawo ta fi kowa farin ciki, in yana waje ta yi masa addu'a, ba ta taɓa kallon dukiyarsa sai don ta adana masa, duk abin da ya ba ta sai dai godiya da addu'a.


Waɗannan ba za su taɓa haɗuwa ga budurwa ba, bare kuma ta kwatanta su ga wani saurayi, kenan duk surutan cikin duhun dare shirme ne kawai da ɓata wa juna lokaci, sai kuma sha'awar juna da kullum ake ba ta ma'anar soyayya don cutar da kai, domin duk lokacin da aka biya wa juna buƙata sau ɗaya, sau biyu, sha'awar ta tafi sai a ce soyayya ta ƙare, sai ka ce zaman kashe dakali da tsotson minti zuwa saduwa su ne soyayyar.


Shi kuwa namiji in ya fara tunanin cewa wannan yarinyar fa za ta zama rabin rayuwarsa, uwar 'ya'yansa da su riƙa musayar jini da numfashi, dole ya riƙa jin cewa shi da ita abu guda ne, tana buƙatar kulawarsa da tausayinsa, amintacciyarsa ce, rumbun asirinsa ce, mataimakiyarsa ce a cikin gida ko a waje, laifinta kuskure ne in za a haɗa da kyautatawarta, tana masa kaza da kaza don haka ta cancanci zama ɓangaren jikinsa da ba zai iya yakicewa ya yar ba, tana buƙatar tausasawar zuciyarsa da ta aljihu, don haka ba zai taɓa bari wani abu ya sha gabanta ba bare ya ga gazawarta.


MAKALOLI MASU ALAKA:

Tsakanin So Da Soyayya (04)


Don Allah in za mu kalli waɗannan abubuwa ta ɓangaren mace da namiji akwai buƙatar mu ta da jijiyar wuya wajen faɗin akwai soyayya ta gaskiya kafin aure ko babu? Sannan akwai buƙatar mu yi nazari kan cewa da gaske ne soyayya takan ƙare bayan aure sai kuma zaman haƙuri?


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user