Wednesday 13 January 2021

Karanta Amfanin Yin Kyauta Guda 8 Ga Masoyi Ko Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Dayawa daga cikin matasa basuson yin alkhairi ga budurwan su, wani zai iyayin wata biyu zuwa uku ko kyautan naira ɗari (₦100) bazai shiga tsakanin sa da budurwan sa ba.


HANNUN KA MAI SANDA


Marubuci:- Kamaluddeen Kmc


Wani ma har shekara zai iyayi batare da yamata alheri ba, kuma ahaka yakeso karta saurari kowa sai shi, a haka yakeso tasoshi so na haƙiƙa alhali baikyautata mata.


Dayawan 'yan mata suna iyayin sati ko wata ma ko sisi basu dashi.


Saboda ba wani sana'a sukeyi ba galibin su, shiyasa idan ankon su yataso hankalin su yana tashi sosai musamman ma iyayen ta marasa ƙarfi ne, shiyasa idan sunnema agida basu samu ba zasu tambayi ɗaya daga cikin samarinsu wanda suke kallon yanada fuskan rahama yabasu kuɗin anko musamman inda shaƙuwa , duk da cewa wasu matan suna wuce gona da iri.


Yanada kyau kafin kafara yiwa mace hidima ka fahimci inda ta dosa, shin tanasan ka dagaske?


Idan ka fahimci tanason Ka sosai kuma bata taɓa tambayarka ba, kuma bata taɓa nuna maka tanason abin hannun ka ba.


To anan ne yakamata kaikuma saika fara ɗan yi mata ihsani bawai sosai sosai ba, ɗan dai-dai gwargwado.


Su Mata basu raina ihsani galibinsu, ko kyautan chocolate kabata zataji daɗi sosai.


Ballan tana kabata Naira Ɗari Biyar (₦500)  kace tasa kati, zatayi farin ciki musamman ma bata saba riƙe kuɗi ba. 


Idan kuwa tasaba da riƙe kuɗi to irinsu ba kuɗin ake basu ba, kyauta ake basu, kaɗan saya mata takalmi, ko doguwar riga ko turare ko sarƙa mai kyau, hakan nan koda na dubu ɗaya (₦1,000) ne zaka ga yadda zatayi murna.


Amma abin mamaki zaka ga namiji yasan cewa tana son shi sosai, abin hannun Sa baidameta ba, amma sam-sam hannun Sa a dunƙule yake.


Babu ruwan Sa da kyautata mata ko alheri a gareta.


Amma dazaran yaga wani yafara zuwa wajen ta zai fara nuna kishinsa na banza da wofi, idan yaga wani yana Mata hidima kaga yatada hankalinsa yafara cewa aidama abin duniya takeso ba Allah ne aranta ba.


Kai ɗin wa yahanaka janyo hankalin ta ta hanyar kyauta da ihsani?


Wallahi banga laifin macen da ta juya baya ga saurayi marowaci ba, kuma rowa da imani basu zama waje ɗaya.


BARI KAJI WANI SIRRI


1. Duk namiji mai kyauta ga budurwansa yana zama azuciyarta har abada koda kuwa ta gujeshi daga baya, koda kuwa wata ƙaddara ta rabasu to wallahi komi daren daɗewa sai taji kewansa yabaibayeta.


2. A duk lokacin da taji wani ya ambaci sunanka saita tino da alkhairin daka riƙayi Mata koda kuwa tayima butulci.


3. Idan ba'ayi wasa ba ita da samun namiji irinka mai kyauta har abada wallahi, domin dama sau ɗaya take zuwa inji mutane. Duk da cewa wasu suna iya samun dama sama da ɗaya amma ba lalle tasami kamarka ba.


4. Shi mutum mai alheri daraja yake dashi koda a idon maƙiyi ne, domin maƙiyin kama yana iya zama masoyinka adalilin ihsani, hatta maƙiya musulunci a zamanin Manzon Allah (S.A.W) sun karɓi muslunci ne a dalilin ihsani da manzon Allah yayi musu.


5. Duk mutumin da baya kyautata wa budurwan Sa to haƙiƙa soyayyar sa tana cikin barazana domin akoda yaushe za'a iya ƙwace masa ita idan ta haɗu da mai kyautata mata fiye dashi , domin ita zuciya batada ƙashi kuma zuciya akullum tanason mai kyautata mata.


6. Ubangiji yanason masu kyautata wa, kyautatawan nan ya shafi kowani iri domin mahaifiyarka ce, 'yan uwan kane, iyayen kane, maƙwabtan kane dukkansu kyautata musu Allah yanason hakan.


7. Hatta a gidanku kuma a ɗakinku, wanda yafi kyautata maka yafi shiga ranka kuma kafi ganin Sa da kima da kuma daraja


8. Da yawan mutanen duniya sunfison mahaifiyarsu saboda me yasa? Saboda uwa tafi kyautatawa 'ya'yan ta fiye da mahaifi, shiyasa ake tsananin ƙaunarsu.


Da zaka sami mahaifin da yake kyautata wa 'ya'yansa  fiye da mahaifiyar su da zaka samu 'ya'yan sunfi son uban su. Amma samun irin wannan uba yana da wuya.


Don haka na barranta kaina daga cikin matasa masu kira a dunƙule hannu.


Domin lalle Allah yana son masu kyautata wa.


Allah shine mafi sani. 


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user