Saturday 9 January 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (28) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

DA WA KAKE MA'AMALLA?


Idan ka ce ba za ka yi ma'amalla da wane ba to ƙila ka yi da shi ne a baya ba ka ji daɗi ba, ma'ana dole yanzu a kiyaye, ka ƙaru da ilimi kenan, ba a cewa ba za a yi ma'amalla da mutum ba sai in an yi a baya ba a ji daɗi ba, haɗuwa da mutane mabambanta hanya ce mafi sauƙi da za ta ƙara maka ilimi wurin isa ga inda kake so, in mutum mahauci ne, yana da kyau ya san komai game da kiwon dabbobi, wannan kuma sai a wurin fulani, ta hanyarsu zai san dabbobin da suke da lafiya, da masu kitse ba naman kirki, da lokacin da ya kamata a sayi dabba ko lokacin da bai kamata a yanka nau'i kaza ba.


KA SAN MUHIMMANCIN KA


MarubuciBaban Manar Alkasim


Yana da kyau kuma ya yi mu'amalla da Majema, domin zai riƙa sayar musu da fata, tanan ne zai san irin fatun da suke buƙata, da kuɗin su, da lokacin da aka fi buƙatar fatun, zai yi mu'amalla da Yarbawa kasancewarsu ma'abota ganda, suna sayen fatu da yawa su je su gyara su riƙa sayarwa, har ila yau zai yi mu'amalla da masu sana'ar sayar da gasasshen nama, wannan a matsayin misali ne, duk wani mai sana'a za ka taras akwai mutanen dake kewaye da shi waɗanda yake amfani da su wurin aiwatar da aikinsa dai-dai, koda kuwa ma'aikatan gwamnati ne, za ka taras akwai kyakkyawar alaƙa ta aiki tsakanin ma'aika kaza da kaza.


Ba abin mamaki ba ne ka ga ma'aikatar haraji tana mu'amalla da jami'an tsaro, masamman masu fararen kaya don tabbatar da kowa ya bi doka da oda wajen biyan harajin, idan wasu suka gano cewa ma'aikata kaza ba ta ba da haraji akwai waɗanda za su yi bincike mai zurfin gaske a kansu, in an kawo su gaban ƙuliya suka yi biyayya shikenan, to haka ma mutum a ƙashin kansa da yake neman aure, yana so ya yi nasara a cikin aikin nan, wato maƙwabtan yarinyan za su taimaka, samarin dake kusa da ita, malaman dake koyar da ita a boko da islmaiyya da wurin sana'anta, in mai yi ce, duk za su iya ba ka abinda kake nema, kenan haɗuwa da wasu a gefe babban ginshiƙi ne da zai taimake ka wajen cika burin ka.


Mutumin da yake son ya gwanance kuma ya ci nasara a aikinsa na likitanci yana da buƙatar sanin injiniyoyi, kafintoci, ma'aikatan wutar lantarki, malaman makaranta, likitoci da sauransu, duk mutane nan za su amfane shi, injiniyoyin za su nuna masa irin ginin da yake buƙata da yadda zai yi ginin ya ɗauki majinyata da dama a ɗan wuri kaɗan, ƙila a rushe tsohon ginin a sake wani da tsari mai kyau, malaman makaranta za su riƙa turo ɗalibansu bisa wani alƙawari ko yarjejeniya da za a yi ta rage kuɗin, da masu shagunan gwajin jini ko ɗaukar hoton jikin mutum, ba nau'in mutanen da ma'aikaci ba zai amfana da su ba.


A duk lokacin da ka fara ma'amalla da wasu mutane dole ka koyi wasu abubuwa daga wurinsu, ko dai ka ɗauki  ilimi ko darasi, in Allah ya sa ka yi dace da abinda kake so a wurinsa ka sami ilimi kenan, sai ka natsu ka koyi abubuwa da dama a wurinsa, in kuma akasin haka ne za ka ɗauki darasi sai ka san yadda za ka guje wa irinsa, ko ya aka yi dai mu'amalla da mabambantan mutane za ta taimaka wa mutum a harkokinsa na yau da kullum.


KA SAN MAHIMMANCIN KA


Tabbas mun bambanta a rayuwarmu ɗabi'ummu da ma yadda muka ɗauki kammu, wannan ya sa wani yake jin cewa ba zai iya haɗa inuwa da wane ba don shi talaka ne, ko ba zai iya zama da wannan ba don shi mai arziƙi ne, har ka ga wani ya shigo ɗakinka yana ƙoƙarin zama a ƙasa, sai ka yi tsayuwar daka kafin ya yarda ya zauna a kan kujera, a ganinsa bai kai wannan matsayin ba, to rashin adalcinmu a yau duk matsayin da ka ba wa kanka haka wasu za su ɗauke ka, mun karanta cewa kowa a ofis ɗinsa shi ne babba don wurin aikinsa ne, in mai kuɗi ya kira ka faskare anan kai ne babba in ba ka yi masa ba ba zai iya yin abinda yake buƙata ba, amma saboda rashin tsari irin namu ba ma fahimtar hakan.


Sai mu ɗauka tunda muna da kuɗi sai yadda muke so, in mutum ya ga ba zai yi ba mu canja shi mu kawo wani, muna sane da cewa in makewayin Alhaji ya cika ba zai fito ya tuɓe riga ya kware matsuguninsa ya fara yasa ba, ba zai iya wannan aikin ba, sai dai ya nemo gwanaye a fannin, to idan su ma suna neman kuɗinka kai ma fa kana neman hidimarsu, kuma kai ka fara buƙatarsu kamata ya yi ka ba su wannan girman, anan mun sami matsala ta rashin girmama juna, in mutum ya hau motarka sai ya riƙa ji kamar ta gidansu, don zai ba ka kuɗi, ya manta cewa za ka yi masa hidima, in ya zo shagonka sai ya faɗo maka duk abinda ya ga dama don zai fidda kuɗinsa, shi ma fa zai karɓi kayanka ya tafi da shi, yanzu an kai ko ofishin 'yan sanda mutum ya shiga in dai mai kuɗi ne sai ka ɗauka ba mai laifi ba ne, hankalinsa a kwance.


MAKALOLI MASU ALAKA:


Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (25) Cikin Sauki


Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (26) Cikin Sauki


Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (27) Cikin Sauki


Tunda duniyar ta juya kai ma'aikaci ko mai sana'a ka lallaɓa kayanka, ban ce ka ƙasƙanta kanka ba, in akwai halin da za ka lallaɓa mutum kuma ka jawo hankalinsa a kaikaice zan so ka yi, shi kyakkyawan hali ko mugu yana son sa, matuƙar za ka girmama kanka wasu ma za su girmama ka, sai in ka haɗu da irin waɗancan mutanen sai ka mu'amalance su ta wata fuskar amma kar ka yarda ka yi asararsu, akwai wani mai shago in na zo siyan kayan da ba shi da shi zai bar shagonsa ya sayo min a duk inda zai samu, wani sa'in ko ba ni da kuɗi zai yi amfani da nasa ya sayo min in na samu in mayar masa, ba fa yaron gidana ba ne ba a kamfanina yake aiki ba, wannan ya sa ba zai yuwu na sayi wani abu a wurin wani ba matuƙar yana da shi.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user