Tuesday 9 February 2021

Karanta Manyan Siffofin Karuwai Da Rayuwar Su Cikin Sirri (3)

Tura Wannan Zuwa Ga

A rubutun da ya gabata kashi na biyu na shiga daku cikin ɗakin karuwa, muka kawo bayanin irin ƙazantar dake cikin ɗakin karuwa da ƙazantar dake jikin karuwa, da yadda karuwa take yaɗa cutuka a tsakanin al'ummah musamman mazinata.


Rayuwar Karuwai


Marubuci:- Datti Assalafy


Wannan rubutun zai ta'allaka ne akan yadda karuwa ko karuwai suke ɗana tarko wa attijirai, manyan sarakuna ko 'yan siyasa mazinata domin su dinga samun maƙudan kuɗin shiga masu yawa, Karuwa kaska ce raɓi mai jini, ba dama karuwa ta zauna haka nan sai inda zata samu kuɗi, shiyasa idan karuwa ta tsufa a harkan karuwanci, wato farjinta ya mutu ya gama aiki, bai kawo mata kuɗi yadda ya kamata, sai ta koma harkan Luwaɗi wanda a yanzu shine abinda yafi kawo ma karuwai kuɗi.


Yawanci haka karuwai na wannan zamanin namu suke sun zama 'yan Luwaɗi, to yanzu sun fahimci Luwaɗin ba zai kaisu ba saboda cutar da yake haifar musu, yanzu su fara ɗana tarko wa wasu manyan attajirai, 'yan siyasa da sarakuna da suke harkan Luwaɗi don neman hanyar samun maƙudan kuɗaɗen shiga, zaku gansu suna walwala suna sayen manyan gidaje da motoci masu tsadan gaske, suna kafa kungiyoyin da suke taimakon al'ummah da kuɗin karuwanci suna alfahari dashi.


Saboda cigaban zamani yanzu karuwai sun baza tarko, suna sayan na'urar sirri mai ɗaukar hoto da bidiyo, suna bin manyan 'yan siyasa da attajirai da sarakuna suna lallaɓarsu da suyi zina dasu don su samu damar da zasu ɗauki hotonsu ko bidiyonsu su mayar dasu hanyar neman kuɗi wato natural ATM, a gidajen da karuwai suke ginawa ko su kama haya su shiga; suna saka na'urar ɗaukar hoto da bidiyo ta ko'ina, daga lokacin da ka iso kofar gidan karuwa har zuwa cikin ɗakinta bidiyo ne take ɗauka.


A matsayinka na attajiri mai kuɗi ko babban ɗan siyasa ko babban basarake mazinaci ɗan Luwaɗi kaji tsoron Allah ka tuba ka dena, imba haka ba zaka faɗa tarkon karuwai, ka sani cewa wannan jakar dake hannun karuwa na'urace mai ɗaukar bidiyo baka sani ba, ɗan kunnenta na'urar ɗaukan bidiyo ne baka sani ba, biron dake hannunta, botil ɗin rigar jikinta, kayan jikinta, gashin dokin da ta ƙara a gashin kanta zai iya kasancewa akwai na'urar ɗaukar bidiyo da hoto, burinta kawai ta samu damar kwanciya da kai a hotel, daga nan  ta gama da kai.


Akwai wata shegiya riƙaƙƙiyar karuwa da na sani tana yiwa 'yan siyasa wannan ta'asa, karuwace wanda kwanaki tayi rubutu anan Facebook tace Datti Assalafiy ɗan ta'adda ne yana kira a cire kan mutane lokacin da nayi magana aka kama kafurin yaron nan Mubarak Bala bayan ya zagi Manzon Allah (S.A.W) a shafinsa na Facebook, sai karuwan ta fito ta min ɓatanci wai ni ɗan ta'adda ne, amma ban kulata ba sai na tura yarana suka aika mata da saƙo.


To waɗannan karuwai haka suke, da zaran sun mallaki bidiyon wani ɗan siyasa ko babban basarake sai su fara takama da barazana, suna ganin zasu iya sa a ɗaure kowa, suna alfahari da jiji da kai, kana taɓata sai tace wai ta san manya zatasa a ɗaure mutum igiya sai ya saura, to wannan shine gadaran karuwa, wataƙila tana da hoton gwamnan jiharku yana zina da ita, idan ka taɓata zata kirashi tasa a ɗaure ka ko a ɓatar da kai, saboda shima yana tsoronta don ta mallaki hotonsa yana zina da ita.


Jama'a wannan shine abinda yake faruwa, yau idan alfarma ko haƙƙinka kake nema a gurin waɗannan manyan mutane ba zaka samu ba sai kabi ta hannun karuwa, sai ka shekara guda kana bi amma rana ɗaya karuwan da ta mallaki hotonsa ko bidiyo yana zina da ita zata samu wannan alfarmar a cikin mintuna.


Na rantse da girman Allah na san karuwan da a yanzu haka tana da bidiyon wani babban jigo a siyasar wata jiha a Arewa tsirara haihuwar uwarsa yana zina da ita, na san karuwan da ta mallaki bidiyon wani gawurtaccen jami'in tsaro mai babban matsayi a ƙasar nan, na san karuwan da ta mallaki abubuwan sirri na 'yan siyasa da yawa tana nan tana ta sheƙe ayarta, suna bata maƙudan kuɗaɗe.


DUBA WANNANKaranta Manyan Siffofin 'Yan Luwadi Da Rayuwar Su Cikin Sirri (1)


Waɗannan karuwai annoba ne, suna daga cikin waɗanda suka jefa wasu shugabannin siyasar mu harkan satar dukiyar al'ummah ana basu, karuwa zata jure wahala da wulaƙanci ta fara kamun ƙafa da yaran 'yan siyasa kawalai suma su kwanta da ita, kafin nan su kaiwa Maigidansu, daga nan tayi ta lallaɓar ɗan siyasar har sai ta samu damar kwanciya dashi ta mallaki bidiyo da hotunansa, shikenan buƙatarta ta biya, sai ya dinga ɗaukar dukiyarku yana bata.


Don haka karuwai ta kowace fuska annoba ne, kuma illane da suke cutar da al'ummah, karuwai su dena baku sha'awa yaku bayin Allah, karuwai su dena burgeku.


Yaa Allah Ka karemu daga sharrin karuwai Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user