Monday 8 February 2021

Karata Sababbin Sakonnin Soyayya Na Barka Da Yamma

Tura Wannan Zuwa Ga

KE CE RAYUWATA


Zan kasance cikin son ki har abada. Kalaman bakina sun gaza wajen furta adadin yadda zuciya take ƙaunar ki. Kin zamo tamkar numfashin da nake shaƙa. Ke ce rayuwata, ina son ki. ban san halin da zan shiga ba a lokacin da na rasa ki. Ke ce abar bege na cikin safiya da maraice. Ki Huta Lafiya.


Sadaukarwa Ga Mata Da Maza, Samari Da Ma'aurata


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


TAURARON ZUCIYATA


Shauƙi mafi tsuma zuciya da nishaɗi mafi ƙarfin kore damuwar zuciyata basu kasance a tare da ni ba sai bayan da na haɗu da kai. Kai ne  ka zamo tauraron da hasken sa yayi sanadiyar raba zuciyata da baƙin duhun da ta daɗe a ciki. Haɗuwa da kai ya kawo canji mai yawa a cikin rayuwata. Ka huta lafiya. Ina Son Ka.


KE CE A ZAHIRI KUMA KE CE A CIKIN BACCINA


Lokutan yin baccina sun kasance daga cikin lokuta mafi soyuwa a cikin zuciyata saboda ke ce kika zamanto cikin ƙawata baccina a dukkan lokacin da na rintse idanuwana, kina bayyana cikin mafarkina a kowane dare na kan gan ki cikin shiga irin ta amare, tabbas ina fatan mafarkina ya zamo gaskiya na zama na ki kema ki zamo mallakina. Ina Son Ki.


KA ZAMO WANI ƁANGARE NA RAYUWATA


Burin idaniyata a kullum baya wuce na ganin ka. Aikin ƙwaƙwalwata cikin kowa ce daƙiƙa shi ne tinanin ka. Da son ka nake kwana da son ka nake tashi, tare da shi nake fatan mutuwa manne cikin ƙirjina. Siffar ka na yi min gizo cikin duniyar baccina a kowace rana. Ina son ka masoyina. 


A RANA IRIN TA YAU


Ina son na sanar da ke cewa dukkan wani motsinki kina yin shi ne a tare da ni domin kuwa tini ruhikan mu suka dunƙule suka zama abu ɗaya gangar jikin mu ce kawai suka banbanta da juna. Ina tare da ke zan kuma ci-gaba da kasancewa a tare da ke cikin dare har rana. Ina Son Ki.


KA AMINTA DA ZANCE NA DAGA ZUCIYA NE BA DAGA BAKI BA


Ina fatan baka daga cikin masu yin tinanin cewa mace ba zata iya bayyana wa namiji tana son shi ba? A yau nake son bayyana maka wani sirri da ya daɗe ƙunshe a cikin zuciyata, na kamu da son ka ba tun jiya ba balle yau. Kai ne saurayi na farko da a karon farko ya sace zuciyata cikin gaggawa, da tinaninka nake kwana da kuma shi nake tashi. Tabbas kai ne wanda zuciyata ta daɗe tana nema domin samun nutsuwarta. Ina son ka masoyina tare da fatan kasancewa a tare da kai har abada. Ka huta lafiya.


INA SON KI FIYE DA YADDA NAKE SON KAI NA


Ko kin jiyo abun da wasu masana SO suke cewa kuwa? abun da suka ce shi ne, SO shi ne kasantuwa cikin tinanin wani fiye da yadda kake tinanin kan ka a  koda yaushe kuma cikin kowane lokaci da kuma yanayi, tabbas wannan batu yayi dai-dai da yanayin da nake ji a kan ki. Ina son ki fiye da yadda na ke son kaina. Ki huta lafiya.


INA SON KA SABODA HALAYYARKA


Ina kwana na tashi cikin tinanin ka. A dukkan lokacin da nake cikin damuwa tuno da tsararrun kalaman ka cikin muryarka mai daɗi shi ne taimakon gaggawa da yake gusar mini da damuwa, ina son ka saboda halin ka, amma shin ni saboda me kake so na, kyau ne ko kuma mene ne ya ja ra'ayinka a kai na?


KE KYAKKYAWA CE


Kin kawo haske a cikin rayuwata, kin wadata zuciyata da farin-ciki, kin kore dikan wata damuwa daga cikin zuciyata da makami mafi kaifi wato murmushin ki, zan so na kasance cikin kallon fuskar ki a dukkan lokacin da kike yin dariya, tabbas ke kyakkyawa ce, ina godiya a bisa kulawar da kike ba ni, ina son ki saboda halin ki. Samuwar ki a cikin rayuwata hakan ya nuna ni a matsayin ɗan baiwa. Ina Son Ki karda ki manta da hakan.


NA YI FARIN CIKI DA KASANTUWA TA A TARE DA KAI


Sau da yawa zuciyoyin mutane da dama na shan wahala da shiga matsananciyar damuwa a lokacin da suke tsaka da neman soyayyar gaskiya daga wajen waɗanda suke so, ita kuma soyayya ta gaskiya ana samun ta ne a wajen wanda ya nuna maka ƙauna, a saboda haka nake godewa Allah da ya haɗa ni da kai kyakkyawan saurayi mai kamala. Ina son ka.


SAMUN KAMAR KI ZAI ZAMO ABU MAI WAHALA


Ina tafe cikin tinanin ki kunnuwana suka jiyo min abun da ya sosa raina jin cewa da akwai sauran mata masu kyawun fasali da iya ado irin na ki a cikin wannan duniya, sai dai ni na tabbata ba za a taɓa samun kamar ki ba a cikin duniyar mu ta mutane, ina fatan ki kasance cikin bani gudunmawar inganta soyayyarmu domin cimma wa muradin zuciyar mu. Na tanadi dukkan wata kulawa domin ki. Fatana a cikin dare ko rana ki kasance mai tina cewa, Ina Son Ki.


ZAN KASANCE MAI BAKA KULAWA MASOYINA


Dama a ce sauran masoya na duniya za su yi kwaikwayon salon soyayyarka tabbas da yawan samun matsaloli a soyayya sun ragu. Ka iya soyayya masoyina, zan kasance mai baka kulawa da kuma kaucewa dukkan abun da zai sanya ka a damuwa. Ina son ka ina kuma kwana cikin tinanin ka. Ka huta lafiya.


INA SON KI RIƘE CEWA


So abu ne da yake da matuƙar hatsari, saboda haka akwai buƙatar ki yi duba na tsanaki a lokacin da kike ƙoƙarin zaɓar saurayi na gaskiya wanda zai tafiyar da rayuwar ki cikin girmamawa da kulawa, amma a lokacin da kika yi zaɓen tumun dare tabbas zaki kasance cikin da na sani da yin nadama na tsawan rayuwa. Kasantuwa cikin rayuwa mai inganci cikin soyayya ta gaskiya hakan na nufin ki zaɓi mutumin da hankalin ki ya kwanta da shi. Wannan shawara ce a matsayina na masoyin ki. Fatana a kullum ki fahimci cewa, Ina Son Ki.


NI NA TABBATAR DA NA YI DACE


A dukkan dare zuciyata na raɗa min cewa, So ba kawai yana nufin samun abokin rayuwa bane ba, sannan kuma ba yana nufin ƙulla zazzafar soyayya a karon farko ne ba, a'a SO yana nufin samun ingantacciyar kulawa daga wajen saurayi kyakkyawa irin ka, SO na nufin gina katangar soyayya mai ƙwarin da zata ɗauki tsawon lokacin da ya kai a busa ƙaho a doron ƙasa. Ina Son Ka


INA FATAN SAMUN KULAWA DAGA WAJEN KI


So na iya sawa mutum ya kai kansa wajen da zuciyarsa zata gaza samun kulawar da ta dace da shi, hakan na nufin ya kasance cikin ƙunci da damuwa. Ina fatan zaki kasance cikin bawa furannin soyayyar da nake yi miki tsaftataccen ruwa domin ganin ingantuwar soyayyar mu cikin bawa juna kulawa. Ina Son Ki, farin-cikin raina.


ZAI YI WAHALA FITAR SON KA DAGA CIKIN ZUCIYATA


A lokaci ɗaya So kan iya shiga cikin zuciya har ya samu gurbin zama, amma fitar da shi daga cikin zuciya ka iya ɗaukar mutum tsawan rayuwa ba tare da ya cimma wa hakan ba, ina son ka masoyina zai yi wahala fitar son ka daga cikin zuciyata. Ina fatan zan kasance cikin zuciyarka kamar yadda ka kasance cikin tawa zuciyar a safiya da maraice?. Ina Son Ka.


KIN YI MIN SATA


Tawagar jami'an tsaro  na nan tafe a hanyar su ta zuwa kama ki a sakamakon sace min zuciya da kika yi, kika kuma yi garkuwa da farin-ciki na, kika kasance riƙe da linzamin sarrafa tinanina. A nan nake cewa mu haɗu a kotun masoya domin ki kare kan ki. Hmm! Ina Son Ki, Masoyiyata.


INA TINANIN RANAR DA ZATA ZO A CE NA RASAKA A CIKIN TA


Ina son ka masoyina, ina kwana zuciya cike da tinanin ka. Na aminta da cewar masu cewa Shi so tamkar yaƙi ne wanda fara shi yake da sauƙi amma tsayawarsa ya zamo abu mai wahala. Ina tinanin ranar da zata zo a ce na rasa ka a cikin ta, wannan rana zata kasance rana mafi duhu da ƙuntata a gare ni. Ina son Ka.


SAMUWAR FARIN CIKIN KI SHI NE BURINA


Dukkan abun da na baki masoyiyata na dangane da lokaci da kuma kulawa ba wai ina tsammanin samun kwatankwacin shi daga wajen ki bane ba domin yin hakan abu ne da ya zama dole a kaina. A kullum burina ki kasance cikin farin-ciki da annushuwa. Ina son ki abar begena. 


MU KASANCE TARE CIKIN SON JUNA SHI NE MURADI NA


Kasantuwar ka masoyi a gare ni ya wadata zuciyata da farin-ciki. Samuwar farin-ciki a gare ni cikin soyayyar mu ba abu ne da ganin ƙarshen sa zai yi sauƙi ba, saboda ita soyayya ta gaskiya aba ce da bata taɓa gogewa daga cikin zuciyoyin masoyan biyu. Ina fatan zaka ci-gaba da so na kamar yadda nake son ka har abada. Ka huta lafiya.


BURIN ZUCIYATA SHI NE KI ZAMO MATATA


Na kan shafe dare cikin yin addu'ar dacewa da samun wani kaso daga cikin kulawar ki masoyiyata, So ya kasance a cikin zuciya ne, ita kuma kulawa bayyane take a saman fuskokin mu, zan kasance cikin farin-ciki na tsawon rayuwa a dukkan lokacin da aka ce na mallake ki a matsayin matata, ina son ki, ina kuma ƙaunar ki, zan ci-gaba da son ki har abada.


BANI DA GWANIN DA YA ZARCE KA


Ina son ka kuma ba zan daina son ka ba har zuwa lokacin da zuciyata zata daina bugawa. kai ne a cikin zuciyata a dukkan inda na shiga a faɗin duniya, babu wanda zai iya maye gurbin ka a cikin ta a lokacin da na rasaka saboda haka nake fatan Allah ya bar mu tare har abada. Ka huta lafiya.


KO KIN SAN CEWA AKWAI WANI SIRRI NA MASOYA A JIKIN FURANNI?


A lokacin da kika kai ganin ki ga tarun furanni dake shinfiɗe cikin lambun masoya zaki tarar da banbanci mai yawa dake tsakanin su ta fuskar launi, amma abun mamaki a gare su shi ne duk ƙamshin su ya kasance guda ɗaya ne, wannan ba komai bane face wani sirri na daban a soyayya. Son ki ya mamaye zuciyata fiye da yadda fuskata zata iya bayyanar da hakan a zahiri. Ina Son Ki masoyiyata.


INA SON KI MATATA


A yanzu haka son ki ya motsa a cikin zuciyata. Tabbas na ƙara aminta da cewa soyayya bata tsufa, saboda shi so bawai yana samuwa ne daga duniyar tinanin mu da ta kasance cikin ƙirga shekarun mu ba, yana samuwa ne a cikin zuciyoyin mu da suka kasance cikin bijirewa irga adadin shekarun na mu a duniya. A saboda haka nake cewa ina son ki matata, ki kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan dawo gida. Ki huta lafiya.


MIJINA FARIN CIKIN ZUCIYATA


Ina fatan kana nan cikin walwala da jin daɗi mijina na kaina? Na kan shiga cikin kewarka a dukkan lokacin da ka yi nesa da ni. Tabbas son ka ya mamaye zuciyata hakan ya sanya bana yin wata walwala da sukuni face muna a tare da juna. Ina son ka hasken idaniyata. Ina yi maka Fatan nasara da dawowar ka gida lafiya.


SAKO MAI MUHIMMANCI


Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user