Saturday 13 March 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (32) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

MUTANE KALA BIYU NE


Dangane da aiki ko sana'a mutane sun kasu zuwa gida biyu:-


a) Mai jin daɗin aikinsa: Wannan kam yana son aikinsa kuma yana jin daɗin ganin abinda yake yi, kullum alla-alla yake yi gari ya waye ya kama hanya, don ko kafin ya bar aikin ya dawo gida sai da ya tabbatar ya kammala aikin yau gaba ɗaya, kuma ya shirya abin da zai taras gobe, yakan bar aikin ne cikin zaƙuwar dawowa ya taras da shi, wannan ya sa wani zai gama da na yau har ya ɗan rage na gobe ma yadda in ya zo aikin zai yi masa sauƙi.


Nasarar Aiki


MarubuciBaban Manar Alkasim


Irin waɗannan mutanen ba su da wani tunani na rabuwa da aikin don suna jin daɗinsa, koda kuwa wurin aikin nasu ne, ko na wani ne sukan yi ne a biya su, wani ma sai ka rantse da Allah wurin nasa ne saboda ƙaunar aikin da yake yi, na ga wani Basakkwace da ya riƙe wa wani Bakano shago da amana, na yi zaton yaron wancan ne, ashe bariki ce kawai ta haɗa su, har dai Bakanonnan ya yi ƙarfi ya sayi wani shagon kusa da wannan ya maƙare shi da kaya, koda ya tashi tarewa sai ya ce ya bar wa yaron nan nasa tsohon shi ya koma sabon, lamarin ya ba ni sha'awa matuƙa, bai yi haka ba sai don ganin gaskiya da amanar yaron da kuma jajurcewarsa, na ga wuraren aiki da dama amma ban ga rabuwar da ta ba ni sha'awa kamar wannan ba.


Wanda duk yake ƙaunar aikinsa za ka taras kullum neman ci-gaban aikin yake yi, yana ta nemo hikima ta kowani ɓangare yadda zai haɓɓaka aikin nasa, ko ya sauwaƙe shi, ko ya inganta shi, ko kuma ya ƙawata shi ga idon jama'a, tunaninsa a kullum shi ne ci gaba, bai damu da cewa aikin nasa ne ko na ubangidansa ba, irin wannan ne sai ka ga a ƙarshe ubangidan nasa ya kyautata masa sanadiyyar aikinsa, na san wani da ya je koyon aiki a wurin wani abokina ko shekara cikakka bai yi ba har ya fara tunani da faɗin cewa ogan nasa bai kai shi sanin kan aikin ba, wannan a ganina butulci ne da rashin sanin ya kamata, ƙila kuma zaman ba zai wani daɗe sosai ba, saboda raini ya fara shigowa tsakiya, duk inda aka fara samun irin wannan to kuwa akwai matsala.


b) Yana aikin ba don yana so ba: Wannan za ka taras don dole yake yi, irin bai sami wanda ya fi shi ba, ko an matsa masa ne a gida, ko kuma bai son zaman banza dole ya fara, ko shi ɗan na kashewa kawai yake nema bai ɗauke shi a matsayin sana'a ba, a irin wannan yana yi ba dole ne ya je aiki ba, a kullum yana neman ɗan dalili ne wanda zai maƙale da shi ya ƙi zuwa aikin, ko in ya je ɗin ya dawo gida ko ya wuce yawonsa, ko bai yi aikin komai ba za ka taras da shi a gajiye yake, in damina ta zo ko hadari ya gani ba zai fita aiki ba to bare a ce an ɗan yi yayyafi, na ga wanda ya ƙi zuwa aiki da aka tambaye shi dalili sai ya ce wai mai gadin abokinsa ne ya karye kuma abokin ya yi tafiya shi ne ya je ya ɗan zauna masa.


Shi abokin ya tafi aiki, koda shi ne ya karye bai da 'yan uwa ne da za su zauna masa bare kuma mai gadinsa? Abin gwanin ban mamaki, irin waɗannan mutanen ba yadda za a yi su yi tunanin bunƙasa aikin bare har su yi tunanin kawo ci-gabansa, za ka iya kwatanta ɗalibai biyu da suka je yi wa ƙasa hidima a wani kamfani, ɗaya daga cikinsu ya dage yana ta aiki tuƙuru, a cewarsa yana ƙoƙarin sanin madafan aiki ne, wanda tabbas haka abin yake, na biyun kuwa yana ganin shi yi wa ƙasa hidima yake, bai ga dalilin da zai riƙa ƙarar da ƙarfinsa a kan wani ƙaton banza ba, yau in ya zo aiki gobe ya ƙi, wani lokacin ma ya ce bai da lafiya ya yi tafiyarsa sai bayan mako guda ya dawo, a ƙarshe kamfanin suka ɗauki wancan aiki yana kammala hidimarsa.


Shi ma ɗayan ya so a ce an ɗauke shi don kuwa ya iya aikin kamar wancan, amma ana ƙimanta mutum ne da abinda yake aiwatarwa, wanda bai sha'awar aiki in ka je wurin za ka gan sa da wayarsa yana lallatsawa, ko wasa da yara ko kallon talabijin, bai da wani lokaci da zai ɓata don ganin ci-gaban wuri, wani ma bai damu da a kore shi ba, kamar wani mai aski da na ga yana ba yaronsa kashi, wai ya buɗe shagon ya je yana yi wa maƙwabcinsa mai nama aiki don a ba shi kuɗin da bai wuce Naira Hamsin (₦50) ba, ubangidan nasa ya zane shi ya ce "Duk tsiyar da za ka yi wallahi ba zan kore ka ba, kuma sai ka yi aikinnan" ya kwaso ashar ɗinsa ya watsa, wai ashe uwarsa ta kawo shi shi kuma ya fi son inda zai yi aiki ne a biya shi wahalarsa ba wai wurin wani koyon sana'a ba, ka ga wannan da wahala ya yi wani abin azo a gani.


Ina ganin akwai bambanci tsakanin ƙwadugo da sana'a, duka aiki ne kowa kuma da hanyar cin abincinsa, amma galibi 'yan ƙwadugo sukan fita ne ba tare da sanin ina za su ko wani irin aiki za su yi ba, kamar leburorin da na sani, ma'aikatan gini ne, amma ba ƙananan ayyuka da ba su iya ba, su ne gini, fenti, ginan rami kamar masai da rijiya, sanya wuta a ɗaki, tabbatar da masai na korawa da ruwa da sauransu, wata rana a samu da yawa wata rana a rasa gaba ɗaya, akan sami ranar da babu ma gaba ɗaya, irin wannan za ka taras hatta aikin akwai yanayin lokacin da aka fi samu, akwai lokacin da ba a samun komai ma, yadda mutum ya fita haka zai dawo hannu Rabbana.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (33) Cikin Sauki


Amma in ka koyi aiki mai wuri tabbatacce kamar fawa, ƙira, shago, kanikanci da sauransu kana da matabbata, in kai mai himma ne cikin ɗan lokaci ƙarami mutum zai yi nasa, sai ka ga ya zama wani abu, a ƙarshe sai dai shi ma ya sami yaron da zai zauna masa, in ya yi dace shi ma ya zama babba kenan, a lokacin zai ga amfanin ƙoƙarin da ya yi, in ya sami yaro mai ƙwazo tabbas zai sami cikakken lokacin da zai huta, a wannan lokacin zai fara tunanin yanzu ya za a yi ya sake samun wani wurin ya zama yana da wuri biyu tunda wannan ya sami mai riƙe masa? Amfanin dagewa kenan a aiki.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user