Wednesday 7 April 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (33) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

BABBAN ABOKIN GABA


Duk wani mahaluki da ka gani ƙoƙari yake yi ya hau kan hanyar nasara, idan kuma ya bi ta a hankali zai isa har inda take, in ya same ta kuma ya lallaɓa ta ya yi ta cin moriyarta har ya koma ga Allah, in ba ta sulluɓe ko wani ya ƙwace masa ita ba kenan, sai dai duk lokacin da zai kama hanya yana da wata muguwar abokiyar gaba guda ɗaya wace koda yaushe za ta riƙa taɗiye masa ƙafa, in ya zo da tsautsayi ya faɗi, an gama kenan, wato "Gaggawa" wannan abokiyar gabar ɗai-ɗai kun mutane ne suke iya kaiwa ga nasara matuƙar za ta saka su a gaba, kai ko ka hau kan hanyar ba ta gan ka ba in ta hango ka ba za ka ƙarisa ga nasara ba, sai dai ka sake ɗauko tafiyar.


Babban Abokin Gaba

MarubuciBaban Manar Alkasim


1) Mutum ne ya shiga aikin gwamnati, manufarsa a koda yaushe ya tara arziƙi, yana da damar da zai tara ɗin tunda yana aikin gwamnati kuma yana samun albashinsa mai tsoka, da zai yi manejin ɗan abin hannunsa ya buɗe wata sana'a ya shuka dukiyarsa a can ya jira ta yi yabanya ya girbe da ya sami tikitin zuwa ga nasara, amma sai ya sami wata shawara da aka ce ya ajiye aikin ya shiga siyasa.


Ya kuwa ajiye ɗin, ɗan abinda ya tara da sauran kayan sana'ar duk ya antaya su a cikin siyasar, a ƙarshe aka kada shi tun a zaɓen fidda gwani, gaskiya ya yi gaggawa, da ya shiga siyasar kar ya tsaya takara, ya karanci mazaɓun da mutanen dake cikinsu, da abinda suke  so, ya yi ƙoƙarin sabo da masu ruwa da tsaki na yankin, in suka yarda da shi za su amince masa su zaɓe shi tare da sakankancewar in ya samu zai dube su, amma ɗaukar tsuraitattun mutane ba tare da tabbatar da matsayar masu zaɓe ba wannan gaggawa ne.


2) Abokina yake ba ni labarin wata mata da ta sayar masa da wani takalmi a kan Naira dubu uku, alhali kuɗinsa bai wuce Naira ɗari takwas ba, tana ta jin daɗin cewa ta sami riba, sai na ce masa a kaikaice -ina ƙoƙarin sanin matakin da ya ɗauka- "Ai nan gaba kar ka yi saurin sayen kayanta sai ka ji kuɗinsa a wani wurin tukun" ya ce "Allah ya kyauta! Ai daga yanzu an gama kenan, ni da sayen kayanta har abada, kai! Wallahi in ma na ga wani zai saya sai na hana shi!" A zuciyata na ce ta yi gaggawa, da ta faɗa masa gaskiya ko ta yi haƙuri da ƙaramar riba kullum za ta ci kuɗinsa, amma ta yi gaggawa.


3) Akwai wata da ubanta ya yi niyyar yi mata auren dole, ba ta son wanda za ta aura, amma ta yi alwashin cewa ubanta na mutuwa auren nan ya ƙare, ta ƙi haihuwa kuwa, ikon Allah sai uban ya mutu, ta fita daga gidan ta auri wanda take so, ƙila ta ci nasara, don ta hayayyafa kafin ta rasu ita ma, amma wata sai ta bazama karuwanci an yi biyu babu, wata kuwa rijiya ta faɗa ta mutu shi ma haka, wata mijin ta kashe ita ma aka kashe ta, duka dai sun yi gaggawa ba su auri wanda suke so ba, na ga wace ta auri saurayinta na farko bayan shekara sittin, ta yi nasara.


4) Wani ne aka saka shi wurin samun kuɗi a wata ma'aikata, tsakani da Allah yana samun kuɗinnan ba kaɗan ba, amma sheɗan ya zuga shi ya haɗa baki da ɓarayi aka saci kuɗin nan son rai, a ƙarshe aka yi bincike aka gano ɓarayin suka tona masa asiri, aka kore shi a wurin aikin aka ƙwace wasu abubuwan da ya mallaka kuma aka tura shi gidan yari, na ce ya yi gaggawa, da ya bi a hankali ta hanyar da ta dace zai sami wannan kuɗin kuma ga mutuncinsa ga aikinsa, yanzu ba ko ɗaya, galibin Samari gaggawa ce da su.


5) Akwai wani da ya fito neman auren wata yarinya, soyayyar ta jima ana yinta, har dai ta kai ga an yi aure ashe ya ɗirka mata ciki tun tana gida, saboda tunanin haihuwa a wata uku bayan aure sai suka yi ƙoƙarin zubar da cikin, anan asirinsu ya tonu, na ce sun yi gaggawa ne, da sun yi haƙuri za su cimma burinsu, maganar ta 'yan watanni ce, an ma kusa gamawa, ai kuwa tana warkewa ya ɗauke ta suka tsere, na ce ita ma wata gaggawar ce, da in ta warke za su ci gaba da aurensu hankali a kwance don cikin shi ya yi abinsa, in ma wata mazahabar da aka ce sai an sake ɗaura aure ne sai a yi, su ci gaba da bushasharsu, amma sun yi gaggawa.


6) Wani limami ne ya yi jinkiri wajen fitowa salla, al'adar mutanen mu koda hamsu salawati ne liman ya yi jinkiri lokaci sai dai ya ji ana yi, don in ya ƙara wani lokaci 'yan oya-oya za su nemi a tada sallar don zama cikin masallaci ba za su iya ba, bare kuma sallar idi, har an tura wani sai ga ainihin limamin ya iso, ai kuwa sai ya tunkuɗe wanda aka naɗa don ya yi sallar ranar kacal, a dalilin aikin da limamin ya yi shikenan ya rasa limancin masallacin gaba ɗaya, na ce ya yi gaggawa ne, da ya haƙura ƙila da ba mu samu wannan labarin ba, amma tasarrufin da ya yi a ranar sai ya sure wa kowa, a dalilin haka kuma ya yi asarar matsayinsa.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (34) Cikin Sauki


7) Wani ɗalibi ne da ya kwashe shekara huɗu yana karatu, ma'ana dai ya kammala karatunsa gaba ɗaya, sai wani tunani na satar amsa ya zo masa a ranar ƙarshe ta jarabawar ƙarshe, ai kuwa aka kama shi, dalilin sallamarsa kenan a makarantar, duk abinda ya kwashe shekaru huɗu ɗinnan yana yi ya sayar da su a wannnan ranar, na ce ya yi gaggawa, da ya haƙura zai ci jarabawar ranar koda ba yabo ba fallasa ne, tunda yana da ƙoƙari a wasu darussan wani sai ya tada wani, in ma faɗuwa ya yi wannan darasin kacal zai maimaita a shekara mai zuwa, amma ya yi gaggawa.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user