Friday 16 April 2021

Karanta Zafafan Sakonnin Soyayya Na Barka Da Asuba

Tura Wannan Zuwa Ga

ZUWA GA MASOYIYATA


ƊANƊANO


Bayyana irin son da nake yi miki a zuciyata, tamkar tirsasa ni faɗar irin ɗanɗanon da ruwa yake da shi ne a cikin baki. Faɗar hakan abu ne mai matuƙar wuya. Ina son ki.


TSARABAR MASOYA NA BARKA DA ASUBA


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


KEWA


A duk lokacin da kike cikin kewata, ki tuna cewa, kina tare da ni a cikin zuciyata a ko yaushe. Matuƙar ina raye, ba za ki kasance cikin kaɗaici ba.


MURYA


Muryarki ce ke raba ni da damuwa a duk lokacin da rayuwa ta yi mini tsanani. Ina godiya a gare ki da kika kasance cikin kulawa da ni a ko wace rana.


MAFARKI


Zuwa ga wadda nake ƙauna fiye da wani nau'in kayan ƙyale-ƙyale na duniya. Ina yi miki fatan kasancewa cikin walwala a wannan dare, tare da yin bacci mai cike da kyawawan mafarkai akan abin so. Ki kwana lafiya masoyiyata.


BURI


Idan har ina raye a duniya, babu wani abu da za ki nema ki rasa, matuƙar damar mallaka miki shi tana hannuna. Na adana miki dukkan wani nau'in jin daɗin rayuwa a gidana. Burina ki zamo mata ta mu rayu tare har abada.


NUMFASHI


Abu mai wuya da zan iya yi a rayuwata shi ne mantawa da ke, wanda yin hakan abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba har zuwa ranar fitar numfashi. Ina son ki.


KEWA


Ina shiga cikin matsananciyar kewarki a dukkan wani taku na rayuwata da na yi ba tare da ke ba. Ina kewarki sosai fiye da adadin ɗigon ruwan da ke zuba daga saman duniya a lokacin damina. Ina fatan za ki fahimci irin damuwar da nake shiga na rashin ki a kusa da ni. Ina son ki.


RAYUWA


Na san ba ki san irin farin cikin da kasancewa tare da ke ya kawo a cikin rayuwata ba. Na yi duk wani tunani, na gano babu wani abu da zan iya biyanki da shi akan hakan, face na ce na gode, kuma zan kasance tare da ke har ƙarshen rayuwata.


SA'A


Ina cike da farin cikin samun macen da babu kamar ta a wannan duniya. A duk lokacin da na tuna da cewa ke tawa ce, sai na kalli kaina a matsayin mai sa'ar da babu kamar shi.


HAƊUWA


Ke ce mafarkina da nake yi a cikin kowane dare. Tun kafin mu haɗu, nake fatan haɗuwarmu domin gina rayuwa a tsakaninmu mai inganci. Ke ce kalar macen da na zaɓa, domin kuwa tun kafin mu haɗu, tsararriyar siffarki ta bayyana a cikin zuciyata. Ina son ki ne don halinki, ba don kyawun da kike da shi ba.


GASKIYA


A daidai lokacin da nake ganin babu wata soyayya ta gaskiya da ta rage a duniya, a lokacin kika sauya tunanina ta hanyar nuna mini ita a zahiri. Na aminta da cewa, kina yi min so ne na gaskiya ba don wani abu da na mallaka ba, hakan shi ne ya ƙara dasa sonki a cikin zuciyata, ta yadda babu wani abu da zai iya goge shi har abada. Ina son ki.


ZUWA GA MASOYINA


SO


Ina son ka irin son da ba zan taɓa yi wa wani irin shi ba, ina son ka da dukkan wani nau'in so da nake da shi, wanda zan iya ba wa wani a wannan duniyar.


TUNANI


A duk lokacin da na rufe idanuwana kai nake gani, kai ne a baccina da farkena. Babu wani abu da nake yi ba tare da tunaninka a cikinsa ba. Kai ne abin son zuciyata Yarimana.


TASIRI


Ina da ikon yin magana a duk inda nake so, amma ina cike da mamakin yadda nake kasa yin magana da wani saurayi bayan kai. Ko ka san mene ne dalili? Tasirin soyayyarka ce a cikin zuciyata, sai nake jin ka a kusa da ni, ko da ba ma tare


MURMUSHI


Ba zan taɓa daina son ka ba har abada, ba zan iya tsayar da murmushi a saman fuskata ba a duk lokacin da muke tare. Ina son ka.


TUNAWA


Masoyina abin ƙaunata, ina yi maka fatan haɗuwa da tarin alkairan da ke cikin wannan rana, da samun nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciya. Ka kasance cikin farin ciki da tunawa da ni a ko da wane lokaci. Kwana biyu ba ka nema na, anya kuwa kana tunawa da ni?


SAKO MAI MUHIMMANCI


Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user