Friday 16 April 2021

Sauke Sabuwar Wakar Nazifi Asnanic Ft Hussaini Danko - Sabunta Katin Jam'iyya

Tura Wannan Zuwa Ga

 Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.


MU SABUNTA KATIN JAM'IYYA


Gamayyar mawaƙan fina-finan Hausa ne su fito, su rera wannan waƙar domin ƙara tunatar da al'ummar Nijeriya domin su hanzarta su sabunta katin su na jam'iyyar APC.

Taken waƙar "MU SABUNTA KATIN JAM'IYYA....".

Idan baku manta ba, tun a shekarar dubu biyu da sha biyar (2015), mawaƙan fina-finan Hausa suke tare da Baba Buhari. Idan mu yi waiwaye a shekarun baya sun yi waƙoƙi da dama cikin waɗanda suka fi shahara sune: Lema Ta Yage, Sakamakon Chanji, Aikin Gama Ya Gama da sauran su.

Kaɗan daga cikin mawaƙan da suka bayar da muryoyinsu domin isar da wannan saƙon ga dubban al'ummar Hausawa dake cikin ƙasar Nijeriya dama Duniya baki ɗaya:

Adamu Nagudu
Abubakar Sani (Ɗan Hausa)
Ahmad Shanawa
Alfazazi
Ado Gwanja
Abdul Smart
Auta Waziri
Dan Musa Gombe
El-Mu'az Birniwa
Hussaini Danko
Ibrahim Ibrahim
Ikram Kano
Musa Isah Gwanja
Nazifi Asnanic

Da sauransu

Waƙar ta hau kan  tsari bisa tsarin mawaƙan waɗanda suka baje kolin basira da hikimar su a cikin waƙar.

Wannan dai sabuwar waƙa ce da Mawaƙan Sakamakon Chanji su rera cikin wannan sabuwar shekarar da muke ciki (2021), waƙar dai tazo da wani sabon salo mai tafiyar da zukatan jam'iyyar APC cikin farin ciki da walwala.

Wato tsayawa bayyana abin da wannan sabuwar waƙar ta ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin dai sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke wannan waƙar yanzu domin sauraro.

SAUKE WAKAR ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user