Thursday 2 December 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (43) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

DALILAN DA SUKA SA WASU KE NEMAN SANIN MAKAMAN SANA'A


Ƙin Zama A Ƙarƙashin Wani
Hoto: Clear Review

MarubuciBaban Manar Alkasim


1) Kawo sauyi a rayuwa: Akwai waɗanda suke aiki tuƙuru don kawo sauyi a wuri, ko da kuwa ainihin manufar masu manyan sana'o'i ba wai tausayin mai neman sana'a ne ko kyautata rayuwarsa ba sukan yi abin da zai taimake shi dai a ƙarshe, galibin abin da suke yi shi ne abinda zai bunƙasa kasuwancinsu a daidai wannan ƙoƙarin nasu za su samo hanyoyin da masu ƙaramin ƙarfi za su bi wajen gyara miyarsu, saboda a ƙarshe dai su ne ma'aikatan, manyan za su nemi a kawo musu tsarin da za a bi don su karanta su ba da damar cire kuɗi, a lokacin za a yi binciken kayayyakin da ake buƙata, kowa zai amfana, mabuƙata za su sami abinda suke so, ma'aikata ma haka bare kuma masu manyan jari da suke aikin don riba.


2) Ƙin zama ƙarƙashin wani: Wasu dalilin da ke sanya wa kenan suke aiki tuƙuru don ganin sun mallaki tasu sana'ar ta kansu, ko don kyararsu da ake yi wace ke baƙanta musu rai, ko kuma su na ganin su ma fa su na da ƙoƙarin ko jari ko ilimin da za su iya zama da gindinsu ba sai sun dogara da wani ba, wasu kuma abin da muka ambata ne a baya ke ci musu tuwo a ƙwarya, wato kura da shan duka gardi da amshe kuɗi, na zauna da wanda ya raina ƙoƙarin ogansa, ya ke ganin ya ma fi ogan sanin kan sana'ar, don haka zai ɓalle kawai ya yi nasa, ba ma zai jira sai an yaye shi ba, duka dai dalilai ne.


3) 'Yanci na lokutan aiki: Za ka sami wanda bai son fitowa aiki da sassafe, ba abin da ya ƙi jini irin wannan, wani kuma bai son kai wa dare a wurin sana'a, ko wasu ranaku da suke yin karo da wasu abubuwa da yake son yi aikin yake hana shi, yaran da ke koyon sana'a ƙarƙashin uwayensu kusan sun fi kowa ƙaunar samun 'yanci, don a tunaninsu ba a duba zaruffansu a komai, kuma ba a ɗan cuna musu maganin gardama, kusan da za a tura su koyo aiki a wurin wani za su fi ƙaunar hakan don ba zai takura su kamar yadda suke fama a gida ba.


4) Su na son yin aiki a inda suka zaɓa: Akwai wasu da ba sa son aiki a wuri ɗaya, ko kuma wani wuri na musamman, don haka alla-alla suke yi su bar wurin, kar ka yi mamaki in na ce maka akwai teloli, masu askin baba, masu sayar da magunguna, masu ƙera takalma, kanikawa waɗanda sam ba su ma da shago, komai a gida suke yi, ko in an kira su su bi mutum, irin waɗannan da za su yi shago zai fi musu don sau da yawa mutum kan tafi shagon abin da ya ke buƙata ne sai kawai ya kutsa, ba tare da tun farko yana ra'ayin shiga ɗin ba, irin waɗannan masu guje wa sana'ar da aka ɗora su a kai kan buƙaci sanin makaman wata sana'a don guje wa zama wuri guda.


5) Rashin aikin yi: Wasu in suka kammala karatu ne ga kwalin a hannu amma aiki ya yi wahala sai ka ga suna buƙatar sanin makamar wata sana'ar don dai su ƙaurace wa matsalolinsu na yau da kullum, wanda ya karanci komfuta yakan fara fafutukar neman aiki da karatunsa, wani in ya fara ba ka labarin fafutukar da ya sha kafin ya sami kansa a inda yake za ka sha mamaki matuƙa, wanda ya karanci likitanci za ka ga nan da nan ya zama likitan ƙauye kafin ma ya sami aiki a wani asibitin, galibin makarantun mu na furamare ba don sabon tsari ba wuri ne da masu neman aiki ke zuwa, sukan fara da wannan ne kafin su sami abin yi, yawancin masu makarantunsu na kansu don sana'a suka yi su.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (44) Cikin Sauki


6) Buɗaɗɗen wuri da sana'a: Da yawa wasu ba sa son a ce su na aiki a buɗaɗɗen wuri, wato ofisoshi ne kusan goma a ɗaki guda, kai ma ban da aikinka za ka yi na kowa, haka wasu za su yi naka, kana cikin wani aiki a ce ka sake ka kama ba wane wanda ba yanan, irin wannan kan sa ka ga mutum ya fara laluben wani aiki duk da cewa ga aiki a gabansa yana yi, yana buƙatar ya riƙi abu guda ne wanda shi ne yake lura da shi, bayan ƙoƙarin samun gwanancewa da fice a ciki, mutum zai iya ba wa kansa wani tsaro na musamman, yadda ba zai faɗa rigingimu ba, duk abinda yake gudun faruwansa zai iya yin nesa da shi.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user