Monday 20 June 2022

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (45) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

3) Kwatanta Gaskiya: Duk mai sana'a na da buƙatar gyara sunansa yadda idan aka ce ya yi kaza wani zai ce "Anya!" Ya faɗo kyakkyawan halinsa, kar ka yarda ka shiga cikin waɗanda mata za su riƙa zarginka da rage canji idan aka aiko ƙananan yara. Wannan zai sa mata su riƙa tura yaransu nesa don sayo musu kayan da kai ma kake sayarwa, ba wanda zai iya samun wani abu sai ya rasa wani.


Zancen Bashi....
Hoto: Edgarcpa


MarubuciBaban Manar Alkasim


Yanzu dai yi haƙuri da ƙaramin ribar da za ka samu a wurin mutum guda, yi ƙoƙari ka tara irinsa dubu ribar za ta nunka, idan wasu mutane suka gane cewa kayanka na da arha ko kana cika awo za ka ga yadda na nesa ma zai biyo baya, bare maƙwabta da za su taya ka talla, ita gaskiya kan taimaki mutum wurin bunƙasar kasuwancinsa ne, in ya ɗan rage kuɗin kayan tabbas ribar da zai samu za ta yi ƙasa, amma da kayan zai ƙare da wuri ya saro wani shi ma ya ƙare ya kuma kawo wani sai ya sayar sau uku mai labta kuɗi a kayansa bai sayar sau ɗaya ba. Wannan hikimar ce kamfani ke karanta wurin jama'a ka ji sun ce bonanza, ƙaramin ɗan kasuwa ma yakan kaɗa ƙararrawar arha ta fi bashi don ya sayar da wuri ya ƙaro wani.


Bar batun masu shaguna hatta masu sana'ar hannu za ka riƙa jin ana cewa, "Wane in ka ba shi ɗunki zai ci maka ƙyalle.". Ko ka ji wasu na cewa "A daina kiran wane in ka ba shi fiɗa zai yi maka fince.". Ko ka ji ana cewa "Wane yana tsula kuɗi in ka ba shi gyara, kuma bai gyarawa da kyau don a sake kiransa.". Ko ka ji ana cewa "Masu kwashe masai ba sa kwashewa duka.". Wani mai faskare aka ce "Manya-manya yake fasawa ya gudu ya bar maka.". Akwai masu sana'ar hannu da dama suka kasa riƙe ni, a ƙarshe barinsu na yi na kama gabana. Yana da kyau duk mai sana'a ya yi gaskiya don janyo mabuƙatansa kusa.


4) Riƙa Auna Kayanka: Ga Ɗan Kasuwa akwai nau'in kaya kala biyu da yake buƙata: Na farko dai ya sami wanda mutane ke buƙata, wato wanda ya fi shiga koda kuwa bai da riba sosai, yawan siyansa zai kawo masa abin da yake so. Na biyu wanda asali ma ba riban a ciki ko bai cika fitar da uwar kuɗi ba ma, amma kuma a dalilinsa mutane kan zo su sayi wasu kayayyakin, ko rashin canji ya sa dole sai sun yi maka ciniki, irin wannan kayan ma kana buƙatarsa, bayan waɗannan ma zai yi kyau mai sana'a ya ɗan riƙa zazzagawa yana gani, wani kaya ne ba a samunsa a shagunan da ke kewaye da shi, sai ya kawo, wani lokaci za ka ji ana cewa "In dai kana son abu kaza ne jeka shagon wane kawai.".


Zai yi kyau kuma ka lura sosai cikin mabuƙatan kayanka wa suka fi zuwa? Yara, mata ko manyan mutane? In yara ne ka yi ƙoƙarin kawo wasu abubuwan da yara ke so waɗanda maƙwabtanka masu sana'a ba su ma san da su ba, mata ma suna da wasu kayan da suke so, ba laifi idan sun shigo wurinka ka ɗan tattauna da su ka ji in za su buƙaci wani kayan da kake son zuwa musu da shi. Misali sun saba da ɗanɗanon Maggi, Royco, Knorr, ko cakwai, akwai mai daɗi da ba su san shi ba wato "Terra" tallata musu ka kawo musu kaɗan, in suka gwada za ka sami alkhairi a ciki, kai kaɗai ka fara sayar da shi, sai ka jima maƙwabtanka ba su san kana sayarwa ba, albarkacin wannan ɗanɗanon za ka sami cinikin wasu abubuwan da dama.


5) Zancen bashi kuwa ga mai sana'a wani abu ne da ba yadda zai yi, sai dai wasu dalilin karayar arziƙinsu kenan, wanda yake sana'a kusa da gida ya fi kowa fuskantar wannan matsalar, don 'yan uwa na ganin sun fi ƙarfin abin da suke son karɓa ne,  ko an manta zancen sanayya ko maƙwabtaka akwai alaƙar jini don haka za su karɓi kaya duk lokacin da Allah (S.W.T) ya hore musu sai su biya, duk wanda zai karɓi kaya cikinsu kansa kawai ya sani, bai yin tunanin cewa wasu irinsa guda 10 zuwa 20 suna da wannan tunanin, in duka za su karɓa to mai ƙaramin ƙarfi ya gama yawo.


Idan aka sami tsayayye yakan murza idonsa ne ya hana, sai dai yakan yi bayanin cewa wasu sun karɓa da yawa ba su biya ba za a karya shi, akwai wanda yakan tara sama da dubu 60 na bashi, idan aka yi karo da ƙaramin ɗan kasuwa ko tantama babu zai durƙushe, bashi dole ne amma wa za a ba? Na nawa? Yaushe zai dawo da shi? Sanin wannan yana da matuƙar mahimmanci: Ba kowa ake bai wa bashi ba, mai taurin bashi sananne ne, da ya biya gwara ku ɓata har abada, na san wanda har kirari yake wa kansa da cewa "Rijiya gaba dubu kowa ya ba ki ya ba Allah, baƙo rashin sani, ɗan gari ganganci, tsohuwa fitar rabo.". Idan mai sana'a ya san da irinsu tun farko ba zai ba su ba, in ya zama dole to lallai bashin ya zama kaɗan bisa alƙawarin ba za a kuma ba shi wani bashin ba sai ya biya na baya.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (46) Cikin Sauki


Idan bai zama dole ba to hana shi kwata-kwata shi ya fi, wanda aka san in sun karɓa sukan biya cikin lokaci waɗannan ba matsala ko na nawa ne za a iya ba su, amma lallai mai sana'a ya tabbatar bai ba da bashin sama da ⅛ a lokaci guda ba, yana kaiwa wannan ƙimar ko mai biya ne a dakata sai waɗanda suka karɓa sun biya, mai sana'a ya kyautata bayani a duk lokacin da zai hana bashi don kar ya kori mabuƙacin kayansa, na biyu duk wanda zai karbi kaya ya tabbatar zai biya a kan lokaci, wanda sai ya ga dama a lokacin da yake so zai biya shi ma a iyakance masa don kar ya karya mutum.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user