Friday 10 June 2022

Zancen Hikima

Tura Wannan Zuwa

Akwai wasu wurare da ya kamata mu yi shiru kai ka ce ba mu fahimta ba, mu yi biris da abu kai ka ce ba mu gan shi ba. 


Darasin Rayuwa
Hoto: MDI

Marubuci:- Idris M Rismawy


Hakan ba ya nuna tsoro ko raunin mu ba ne,  sai dai yanzu ba za ka fahimci darasin yin hakan ba sai nan gaba. A lokacin da rayuwa za ta nuna maka haƙiƙanin abin da ke tafiya


Kowanne abu yana da inda ake faɗinsa, kuma kowanne wuri akwai abin da ake faɗi a wurin. Ba komai ne yake da gurbin faɗinsa a ko'ina ba, kuma ba ko'ina ne ake iya faɗin komai a wurin ba. 


Allah yasa mu dace, kuma ya ƙara tsare mana imaninmu Amin.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user