1. ZUCIYAR NAMIJI: Idan har yau za ka fara yin sana’a, to ka sani cewa babu abinda zai zo maka da sauƙi. Idan kuwa da sauƙi, to kowa ma zai iya, saboda haka dole sai ka zama mai zuciyar namiji. Ka yi yaƙi da duk abinda ya shiga gabanka har sai ka samu nasara, sannan ka ɗauki darussa daga kurakurenka. Matsaloli za su kashe maka gwiwa da zuciya, su buga ka da ƙasa. KA YI TA MAZA, KA DAKI ZUCIYA, KA MIƘE, KA ƊAGA KANKA, SANNAN KA CI-GABA DA YAƘAR WAƊANNAN MATSALOLI.
Marubuci: Bello Galadanchi
Shin akwai abin da ya taɓa karya ka? To ka sake gwadawa, sannan ka ƙara gwadawa. Za ka yi nasara, saboda haka rayuwa take. Ku dubi tarihin Annabawa da mutanen da suka yi nasara a rayuwa, sai da suka fuskanci manya-manyan ƙalubale, amma zuciyarsu ba ta mutu ba, har sai da suka cimma burinsu. Idan ka yi nasara, to kar ka tsaya. Ka shuka tushen wani sabon buri, sannan ka ci-gaba da yaƙi.
2. ƘAUNAR SANA’ARKA: Ka yi sana’ar da kake ƙauna domin biyan buƙatun mutanen da ke maka sha’awar wannan sana’a. Ko kayan miya kake sayarwa, idan ka nuna matuƙar ƙaunar wannan sana’a, to za ka ga mutane suna farin cikin ganinka a yau da kullum, wato rayuwar nan ba ta da sauƙi, kuma kowa da kake gani yana da nashi ƙalubalen, shi ya sa mutane suke ƙaunar mutane masu farin ciki da walwala. Yi tunani mana, idan akwai mai sayar da lemo wanda kullum ranshi a ɓace yake, ai ba za ka rinƙa sha’awar zuwa wajenshi ba. Amma a unguwarku akwai mai shayin da kullum idan ya ganka zai ɗaga maka hannu. Duk lokacin da ka je wajenshi sai ya yi ta murmushi yana ba ka labarai. Ai kuwa babu abinda zai hana ka gayyatar abokanka zuwa wajenshi. Shi kuwa kwastomomi sun ƙaru kenan. Sai ya karɓi WeChat ko Facebook ɗin su, yana buga hotunan sana’arsa da duk wani abu da zai tunantar da mutane cewa yana nan, kuma yana ƙaunar sana’arsa. Akwai mai sayar da roba a jihar Kaduna arewacin ƙasar Najeriya mai suna Salsabil. Ina nan ƙasar Chaina, amma na san da wannan shago.
3. ZA KA IYA FAƊUWA: Wannan gaskiya ne. Duk da cewa kana da zuciyar namiji, kuma kana ƙaunar sana’arka, to za ka iya faɗuwa. Mafi yawancin lokaci, rashin kuɗi ne ko rashin haɗin kan sauran abokanka da kake wannan sana’a tare da su, su ne suke karya sana’a. Amma karka damu. Ka mayar da hankalinka sosai akan dalilan da suka karya wannan sana’a, sannan ka ɗauki darasi, kuma ka ƙirƙiro hanyoyin guje wa waɗannan matsaloli nan gaba. Kar ka yi fushi, ko ka ƙullaci wani a zuciyarka, saboda hakan zai gusar da hankalinka daga abin da ya fi muhimmanci. Ka sani cewa mutane za su yaudare ka, za su yi maka baƙin ciki, za su yi ƙoƙarin lalata maka al'amari, amma wannan yana daga cikin zaman rayuwa. Saboda haka idan har ka shawo kan waɗannan matsaloli, ka haɗa da addu’a, to babu abinda zai iya dakatar da kai sai Allah.
4. SHUGABANCI NAGARI: Kowa zai iya fara sana’a, amma nasara kuwa sai wanda ya iya shugabanci. Me hakan yake nufi? Kar ka mayar da hankali akan abunda za ka samu yau ko yanzu, ka zama mai hangen nesa. Dole sai kayi haƙuri da duka jama’a, kuma ka yi ƙoƙarin rashin nuna fushinka idan wani ya saɓa maka, ko ya ƙi cika alƙawari. Babu wata sana’a a duniya da ta yi nasara ba tare da shugabanci nagari ba.
5. KA SAUKAR DA KANKA: Kar ka dage akan cewa sai ka mallaki sana’ar baki ɗayanta, ko sai shawarwarinka za’a bi, idan ba kai kaɗai ne ka fara sana’ar ba. Kar ka ji komai. Mallakar sama da kaso hamsin cikin ɗari na sana’a mai nasara ya fi mallakar kaso ɗari cikin ɗari na sana’ar da take kan hanyar karyewa.
6. KA HAƊA KAI DA WASU: Mutum ɗaya zai iya sheƙawa da gudu, amma mutane da yawa za su daɗe suna tafiya. Abun nufi anan shi ne fara sana’a tare da haɗin kan wasu ya fi fara sana’a kai kaɗai, saboda kowa yana da nashi irin baiwa da basira, waɗanda idan kuka tsaya a waje ɗaya, ba za ku san wace shawara ce za ta kawo muku nasara ba. Ko Manzon Allah (S.A.W) yana tare da sahabbai a kusan ko da yaushe domin jin shawarwarinsu da kuma neman haɗin kansu.
7. KA ƊAUKI ALHAKIN FAƊUWA DA NASARA: Idan aka samu akasi, to shi Ɗan Adam ajizi ne. Ka fito, ka ɗauki alhaki, ka gaya wa duniya cewa laifinka ne, kuma ga inda ka yi ba daidai ba. Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. Mutane za su girmama ka, kuma su ƙara amicewa da kai. Matsalar da tsohon Shugaba Jonathan ya samu kenan, ba ya taɓa fitowa ya ɗauki alhakin kuskure, shi yasa duniya ta juya masa baya. Idan ka ƙi ɗaukar laifi, to jama’a za su guje ka. Idan kuma ka yi nasara, to ka nuna farin cikinka, ka bada tukwici, ka gayyaci kwastomominka ku yi ɗan ƙaramin shagali tare. Ka gaya wa ‘yan uwa da abokan arziki. Za su ji daɗi.
8. MUTUNCI DA AMANA: Ka zama mai mutunci a kowane hali. Jama’a za su ba ka amanar kuɗaɗen su da kadarorinsu. Ɗan ƙaramin abu zai iya ɓata maka suna, har ya kai ga ruguza maka sana’arka. Ka ji tsoron Allah, ka zama mai riƙon amana da mutunta mutane.