Friday 23 September 2022

Shin Ko Ka San Hakikanin Yaudara?

Tura Wannan Zuwa Ga

Dalilan da ke sa yaudara suna da yawa, sai dai a ɗan ambaci kaɗan daga cikinsu:


1. Rashin sanin sirrin da ke cikin zuciya, wanda ake yaudarar bai san yaudararsa ake yi ba. Wannan shi ne mataki na farko cikin dalilan da ke sa yaudara, domin inda mutum ya san abin da ke ɓoye, to da ya kuɓuta daga yaudarar mayaudari ko mayaudariya.


Abin da ke jawo yaudara
Hoto: Shutter Stock

Marubuci: Abdullahi Nuhu Adam


2. Son zuciya: Mafi yawan mayaudara son zuciya ke sa su aikata wannan ɗabi'a ta yaudara inda za ka ga mace ko namiji na aikata yaudara don cim ma wata ɓoyayyar buƙata tasu.


3. Akwai wanda ke shiga yaudara a sakamakon kaɗaici da ke damunsa ko damunta, irin waɗannan idan suka samu kwanciyar hankali a inda suka je yaudarar, to a ƙarshe sai ka ga soyayya ta bayyana har ma ka ga anyi aure.


Mecece ita kanta yaudarar?


Yaudara ita ce ɓoye haƙiƙanin gaskiya da bayyana abin da yake akasin haka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user