Saturday 24 September 2022

Sirrikan Yadda Za Ka Fara Yin Sana'ar Saye Da Sayarwa Cikin Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Saye da sayarwa shi ne shiga tsakanin masu buƙata, da waɗanda ke da shi. Za ka iya gudanar da wannan sana’a a unguwarku, ko jiharku, ko ƙasar ku, ko kuma tsakanin ƙasa da ƙasa. Ribar da za ka samu shi ne bambancin adadin da ka kashe wajen saye, da sayarwa. To saboda rashin buƙatar babban jari, mutane da yawa na rububin fara wannan sana’a, sai dai nasarar ka ta dogara ne akan dabarunka da yadda kake amfani da su domin tafiyar da sana’ar. 


Saye da sayarwa
Hoto: Energy Resourcing

MarubuciBello Galadanchi


Me ya kamata ka yi? Ka fara da binciken tsarin sana’ar saye da sayarwa. Ka laƙanci hikimomin da kake buƙata domin tuƙa jirgin wannan sana’a. Yi hanzari ka nazarci kishiyoyinka da ke kusa, sannan ka yi ƙoƙarin yin fashin baƙin yadda suke tafiyar da ta su sana’ar. Idan akwai hali, ka yi aiki a ƙarƙashin ɗaya daga cikinsu, hakan zai ƙara maka haske akan yadda wannan sana’a take. Wannan hikima za ta ba ka damar zaƙulo sababbin dabarun tafiyar da sana’ar da kuma warware matsaloli. 


Ka samu biro da takarda, ka rubuta ire-iren kayan da kake son saye-da-sayarwa. Akwai kayan da ake samun riba mai yawa, akwai kuma waɗanda ribar ‘yar kaɗan ce amma kuma ana sayar da su sosai. Za kuma ka iya yin la’akari da abin da kake matuƙar sha’awa da ƙauna, yadda hakan zai ba ka damar zaɓen kayan da ka fi marmarin saye-da-sayarwa. Saboda sana’ar saye-da-sayarwa na buƙatar aiki tuƙuru da sadaukarwa da kuma laƙantar kayan yadda ya kamata, to gwamma ka yi sana’ar da kake sha’awa kuma kake da ilimi akai. Hakan zai ba ka damar ƙiyasta ire-iren ƙalubalen da za ka fuskanta, da shiryawa taƙalarsu yadda ya kamata. Gwamma ka fara da nau’in kaya iri ɗaya, sai a hankali ka bunƙasa su a dai-dai lokacin da ribar ka ke ƙaruwa


Ka yi ƙoƙarin tattaro ilimi akan kasuwar wannan kaya naka. Ka rubuta ire-iren canje-canjen da ka iya faruwa dangane da wannan sana’a, da kuma abubuwan da ake yayi. Za kuma ka iya rubuta adadin kuɗaɗen shigar abokanka waɗanda suke wannan sana’ar da ire-iren ƙalubalan da suke fuskanta. 


Yanzu kuma lokaci ne da za ka rubuta duka kamfanoni ko dilolin da ke sarar da waɗannan kaya da kake muradin sayarwa, sannan ka jera su daga ɗaya zuwa na ƙarshe bisa ingancin kayansu, da farashi, da kamfani, da ƙwarewa da kuma adadin lokacin da suke ɗauka kafin su kawo kaya kasuwa. A haka, za ka fi tantance kamfani ko dilan da ya fi dacewa da kai. Ka zaɓi ‘yan kaɗan, sannan ka tuntuɓe su domin ku zauna, da kuma ƙulla yarjejeniya. 


A ɗaya ɓangaren kuwa, ka nemi mutanen da ka iya zama kwastomominka ka yi musu tambayoyi. Ka tattauna da su ɗaya bayan ɗaya, domin fahimtar ƙalubalen da suke fuskanta dangane da waɗannan kaya, da irin yadda suke so a ringa hulɗa da su, da ma wasu abubuwan da suke tsammani. Ka rubuta waɗannan bayanai, sannan ka daidaita su da bayanan da ka samu daga kamfanoni da diloli. Yin haka zai fahimtar da kai irin alherin da za ka samu domin fara wannan sana’a.


Kar ka manta, sirrin nasarar sana’ar ka ya dogara ne akan samo sabuwar hanyar warware wa jama’a matsaloli, yayin da ka rage musu ɓata lokaci da kuma gabatar musu da rahusa. Ta yaya sana’arka za ta kawo wani sabon abu da jama’a ke buƙata? Allah Ya ɗaukaka mana ƙasar mu ta gado Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user