Monday 3 October 2022

Muhimman Abubuwa 14 Ga Dukkan Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ashe dai kamar yadda manomi yake cin ribar abin da ya shuka haka masoya ma suke cin ribar soyayyar su.


RIBAR SOYAYYA
Hoto: Getty Image

MarubuciNura Nakowa


Duk wani manomi burinsa ya ci ribar abin da ya shuka. Ba za a ci ribar noma ba har sai an tabbatar da cewa gona ta yi kyau, wanda hakan ne zai sa a girbi kayan gona me kyawun gaske.


Haka abin yake ga masoya. Abin da suka shuka shi za su girba, kuma burin duk wani masoyi shi ne ya girbi alkhairi.


Mafi girman daraja a ribar soyayyar shi ne AURE. Duk ribar da masoya za su ci muddin ba su yi aure ba, to ba su samu mafificin darajar soyayya ba. Ana iya ribatar wasu abubuwan a soyayya tsakanin masoya kamar faranta ran juna da kyaututtuka da ɗebe kewa da makamantan su, amma dukkanin waɗannan ba kamar a yi aure ba.


Tazarar da ke tsakanin aure da soyayya zalla wacce ba ta kai ga an yi aure ba, tanada yawa sosai.


Ana iya shafe lokaci me tsawo dakuma nisan gaske ana soyewa da soyayya amma kwana ɗaya a gidan aure, ya shafe dukkanin shekarun da aka yi ba tare da aure ba.


Yadda ake ƙirga ribar so ko ribar soyayya;


1. Idan aka aminta da kai a soyayya, ka ci ribar so.


2. Idan ka sa ayi za ayi, idan kuma ka ce kada ayi ba za ayi ba, ka ci ribar so.


3. Ida ana yi maka biyayya sau da ƙafa, ka ci ribar so.


4. Idan ana maka fara'a da jan hankalin ka, ka ci ribar so.


5. Idan ana kwantar maka da hankali da ɗebe maka kewa, ka ci ribar so.


6. Idan ana gudun ɓacin ranka kuma ba a aikata abin da zai ɓata maka rai, ka ci ribar so.


7. Idan ana haba-haba dakai ana mararin ka, ka ci ribar so.


8. Idan ba a son a yi nesa da kai saboda ana jin daɗin zama dakai, ka ci ribar so.


9. Idan ana furta maka kalaman soyayya cikin tattausan lafazi me daɗi, ka ci ribar so.


10. Idan ka ji kullum ka ƙara jin son masoyin ka a ranka, ka ci ribar so.


11. Idan ana yi maka godiya da yabawa, ka ci ribar so.


12. Idan aka ce ba wani sai kai kuma ka tabbatar da hakan, ka ci ribar so.


13. Idan aka zaɓe ka a matsayin wanda za ayi rayuwa da shi, ka ci ribar so.


14. Idan aka aure ka, ka ci babbar ribar so, wanda shi ne burin kowanne masoyi.


Sunada yawa idan za a ƙirga su.


Duk wani abu wanda za ka iya bada shaidar sa na alkhairi game da masoyin ka, riba ce a soyayya.


Na san kai ma da kake karatun nan a yanzu, da akwai wasu abubuwan da kake samu daga masoyiyar ka ko kike samu daga masoyin ki masu burgewa waɗanda ban ambace su ba, to ka haɗasu da waɗanda na kawo, ka tattara su guri guda domin sanin adadin ribar da ka ci.


Alhamdu lillah.


Allah yasa mu yi soyayya don Allah don mu ci riba me tarin yawa Amin.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litinin, laraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user