Monday 3 October 2022

Nagartattun Nasihohi 30 Ga 'Yar Uwata Musulma

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Ki daina kula kowanne irin saurayi, ke koda wani ya zo ya ce yana son ki, ki duba riƙonsa da addini, kada ki ce sai mai kuɗi. 


Har wani lissafi wasu matan suke yi ga mazajen da suke zuwa neman aurensu, idan suka ce "A" suna nufin Accounter, "C" Chairman, "T" Teacher, mafi yawan masu wannan lissafin ba sa son mai "T" ya je wajensu, saboda wai malamin makaranta ne, babu abin da za su samu a wajensa. Amma wasu matan babu ruwansu da wannan lissafin, lissafinsu kaɗai shi ne su samu ma'abocin addini.


Nagartattun Nasihohi Ga 'Yar Uwa Musulma
Hoto: Wakil Kohsar/AFP


MarubuciAbbati Mai Shago Flg


2. Kada ki riƙa roƙon saurayinki kuɗi ko wani abu na daban, koda za ki nemi wani abin a wajensa kada ki yawaita neman, roƙon da za ki yi wa saurayinki zai kai ki ga buɗe kafar ɓarna ne kawai, har ta kai shi ga fara tunanin hanyar da zai bi ya fanshe ababen da ya ke ba ki. Kin ga kuwa wannan roƙon ya zamar miki matsala.


3. Idan Allah ya kawo miki saurayi mai tarbiyya ki riƙe abin ki gam, kada ki tsaya wasa har ki rasa shi, kuma ɗora buri ga saurayin da kike son aura ba abin yi ba ne gare ki a matsayinki na ƴa musulma.


4. Ban da wulaƙanta mutumin da ya zo ya bayyana soyayyarsa gare ki. Idan kina da wanda ki ke so ko bai yi miki ba ki faɗa masa zance mai daɗi; ki ba shi haƙuri, lallai hakan zai sanya shi tafiya cikin farin ciki, kuma ba zai taɓa bari a zage ki ko a jefe ki da mummunan zance ba a duk inda ya kasance.


5. Ki yi haƙuri da abin da yake faruwa da ke na idan saurayi ya zo gare ki soyayya ta yi ƙarfi daga ƙarshe ya tafi ya bar ki. Ki ci gaba da roƙon Allah ya ba ki miji nagari.


6. Ki daina yin dare a wajen hira. Me zai hana ki yi hira da safiya, yamma ko wani lokaci na daban wanda ba yankin dare ba? Ko dai kina ganin hirar safe da maraice ƙauyanci ce?


Shin me ya kai wannan ƙauyanci; saurayi da budurwa su zauna zaman hira da daddare har sama da ƙarfe goma su kaɗai alhalin ga shaiɗan ya turo musu jakadunsa, ai hakan ba abin da zai ba su sai damar taɓa sassan jikinsu.


7. Samarin banza na ƴan matan banza ne; babu yadda za ayi saurayin banza ya zo wajenki ba tare da kin gane shi ta wata hanyar ba, saboda zai nuna miki munanan halayensa da manufar da ta kawo shi gare ki a bayyane ko a ɓoye, bayan soyayyarku ta yi ƙarfi.


8. Allah ne kaɗai ya san iskancin da samarin banzar nan suke aikatawa da yaran mutane a lokacin da suke yin hirar dare, da kuma wani sashe na safiya da yamma; ba wai sai da daddare ne kaɗai samarin banza ke samun damar lalata yaran mutane ba, amma mafi yawan lalatar ta su ta fi kasancewa ne da daddaren. Wannan ne ya sa ake son duk wani uba mai kishin ƴarsa ya yi ƙoƙarin hana ta hirar dare, haka ita ma yarinyar idan tana da hankali ba za ta taɓa yarda ta yi hirar dare ba. Idan saurayi ya zo gare ta za ta ce a faɗa masa ya bari sai gobe da safe ko da yamma.


Na samu wani mummunan labari game da ababen da ke faruwa da wasu mata a lokacin da suke yin hirar dare, wata take cewa "Malam Abbati! Wallahi saurayin wata ƙawata babu inda ba ya iya taɓawa a jikin ƙawata idan suna hira da daddare, abu mafi muni game da hirar tasu har yatsarsa yake sanyawa a farjinta ya biya mata buƙata" yanzu me ya kai wannan abin ban haushi? Na san da a ce da safiya ne ko yamma sannan a cikin gidansu ba zai taɓa aikata hakan ba.


9. Kada ki yarda son abin duniya ya rufe miki ido ki auri mai kuɗi marar tarbiyya, lallai idan kika aikata hakan kin yi asara, za ki yi nadama a gaba kaɗan, nadamar da ba za ta amfana miki da komai ba.


10. Babu mai azurtawa sai Allah, shi kaɗai ne ke sanya wani ya zama mai kuɗi wani ya zama talaka. Abin nufi a nan wanda ya zo gare ki da niyyar neman aurenki idan ya kasance talaka ba shi ya talauta kansa ba, kuma ba shi da wata dabara ko wayon da zai iya azurta kansa.


11. Idan za ki fita daga cikin gida zuwa wani waje na daban kada ki saka matsattsun tufafi, ki sanya kayan da shari'a ta yarda da su, sannan kada ki fesa turare mai ƙamshi in ba wanda yake kashe warin jiki ba.


12. Macen da ta sanya hijabi ta fi wace ƴan sanda suke gadinta samun tsaro.


13. Sanya tufafin da shari'a ta yarda da shi yana ƙarawa mace girma da karamci a idon bayin Allah mai rahama. Bari na buga miki wani misali: Da a ce wani zai ga ɗan iskan gari ya kama hijabin macen da ta yi shigar da shari'a ta yarda da ita, idan ya zo zai ce "sake ta ko na...." ba zai tsaya neman dalilin da ya sa ya aikata hakan ba, duba da ta sanya kayan mutumci, da kuwa wace ta sanya ɗamammun kaya ce, ba lallai ba ne ya kula su, ƙarshe ma zai iya cewa "me ya sa za ku tsare mana hanya? ku matsa gefe guda ku aikata abin da kuka so tun da kun wulaƙantar da kanku a idon duniya" dama ɗan iska a haɗa shi da ƴar iska amsar ita ce ƴan iskas.


14. Ki suturta muryarki, kada ki bari wani ya ji daɗinta idan ba mijinki ba, ban da ɗaga wa iyayenki da mijinki murya. Ke mace ce, ki kula da ababen da za ki furta da bakinki; kada ki furta komai sai alheri.


15. Ki san irin hirar da za ki yi da kowanne mutum; ƙannai, ƴan uwa da ƙawaye.


16. Ban da zagi da cin mutumcin mutane, ki yi haƙuri idan aka zage ki ko aka jefe ki da mummunar magana, ki girmama na gaba da ke, ki kyautata wa ƴan tsararki, sannan ki tausayawa na ƙasa da ke.


17. Ki bi umurnin iyayenki, sannan ki hanu daga abin da suka hane ki, ban da yin ƙunƙuni ko ƙin yi musu biyayya. Lallai duk wanda yake saɓa wa iyayensa ba zai shiga aljannah ba, ayoyi da yawan gaske sun yi nuni da a yi wa iyaye biyayya, babu abin da mai saɓa musu zai gani sai bala'i tun a nan duniya.


18. Idan kika fahimci ƙawarki ta banza ce ki taimake ta ta dawo ta gari, ki riƙa yi mata kyakkyawan wa'azi da nasiha cikin hikima, idan ta ƙi bin ababen da ki ke kiran ta gare su na nagarta ki ƙaurace mata.


19. Abotar mace da namiji tana kai wa ga saɓon Allah, da wannan nake ba ki shawarar ki tsaya ki natsu, kada ki yi abota da namiji idan ba cikin neman ilmi ba, sannan ki kula da kanki a duk lokacin da ki ke tare da shi komai ustazancinsa. Idan kyawawan halayen abokin karatunki suka birge ki har kika ji kina son sa, ki bi duk wata hanyar da kika ga zai fahimci yadda ki ke ji a ranki, muddin ba ta saɓa wa Allah ba, idan kuma za ki iya bayyana masa hakan abu ne mai kyau. 


20. Ki yi wa mijinki biyayya, ki yi haƙuri da shi, kada ki yarda a ji kanku, ki tsaya ki karanci abin da yake so da wanda ba ya so don zamanku ya yi daɗi har ya riƙa birge wasu su rinƙa burin ina ma a ce su ne ku.


21. Ki kula da shafukan sada zumunta; Facebook, WhatsApp, Telegram, Twitter da sauransu. Kada ki bari su zama silar rabuwarki da mijinki ko saurayinki. Ya halatta mace ta ziyarci shafukan sada zumunta amma ta kula da kanta sosai, kada ta yarda hirar batsa ta shiga tsakaninta da wani mutum, ta taƙaita wajen bibiyar darussan ilimummuka da malamai nagari suke gabatarwa a kowace rana. Bugu da ƙari, ya halatta ta tura tambayarta ga wani malami a kan wata mas'ala da ta bijiro mata.


22. Ki kula da sallah, azumi, sannan ki kiyaye farjinki za ki sami aljannah. Aikin da za a fara duba wa mutum ranar Lahira shi ne sallarsa, idan ta yi kyau dukkan ayyuka sun yi kyau, idan kuma ta ɓaci dukkan ayyuka sun ɓaci.


23. Ban da yin munanan hirarraki da jifar mutane da ababen da ba su ji ba, ba su gani ba. Kada ki yi shaida sai a kan abin da kika sani.


24. Idan aka kawo miki labarin mijinki ko saurayinki kada ki yanke hukunci har sai kin tabbatar da ingancin labarin, haƙuri ma shi ya fi alheri gare ki a wannan lokaci da kawar da kai daga abin da aka kawo miki koda kuwa ya kasance gaskiya ne.


25. Ki ji tsoron Allah ki kame bakinki daga bayyana wa ƙawayenki ababen da ke faruwa a shimfiɗarki, haramun ne mutum ya riƙa bayyana hakan, idan kina yi ki daina sannan ki tuna.


26. Ki koyi karatun Alkur'ani, sannan ki koyar da shi ga ƴan uwanki musulmai sai ki zama mafi alherin al'ummar Manzon Allah (S.A.W).


27. Ki ƙara mayar da hankali wajen sanin tsarki, sallah, azumi da ilimin zamantakewar aure, lallai idan kika san waɗannan ababen kafin ki yi aure za ki yi rayuwa mai daɗi a ɗakin mijinki.


28. Ki riƙa yin Azkar na safiya da maraice a kowace rana, hakan zai zamar miki garkuwa daga duk wanda yake neman ki da sharri musamman ma mugayen samari masu sihirce ƴan matan da suka ce ba sa son su, sai su aikata hakan kowa ma ya rasa, lallai Allah baya barin azzalumi. Kuma ki riƙa yi wa Annabi Muhammad (S.A.W) salati, mafi ƙaranci goma da safiya, goma da yamma.


29. Ki yawaita yin Istighfari; yana maganin damuwa, baƙin ciki, rashin haihuwa, kuma yana sanya Ubangiji son bawanSa, ya ƙara masa kusanci da shi. Idan ya roƙe shi ya amsa masa, idan ya nemi kariyarSa ya kare sa.


DUBA WANNAN YANZU: Kyawawan Nasihohi 42 Ga Dan Uwana Musulmi


30. Ki taimaki ƴan uwanki mata ta hanyar koyar da su sana'o'in hannu don su ma su samu dogaro da kansu; za ki iya aikata hakan kyauta ko ki sanya wani abu da za su riƙa biyan ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user