Monday 10 January 2022

Kyawawan Nasihohi 42 Ga Dan Uwana Musulmi

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Idan za ka nemi aure, ka nemi mace mai addini, kada ka biye wa kyau, dukiya. Haƙiƙa kyawu da dukiya za su ƙare, amma idan ka auri mai addini za ka yi rayuwa mai daɗi da ita, kuma abar birgewa ga mai kallo.


KYAWAWAN NASIHOHI 42 GA ƊAN UWANA MUSULMI
Hoto: Quran Academy


MarubuciAbbati Mai Shago Flg


2. Ina gargaɗin ka a kan auren kyakkyawar mace wace ta fito daga mummunan gida.


3. Duniya jin daɗi ce, mafi alherin jin daɗinta mace ta gari. Wannan ya sa idan Allah ya ba wa mutum mace ta gari ya yi bankwana da rigima, damuwa, ƙunci da yawan mantuwa, domin kuwa idan mutum ya auri mace ƴar bala'i za ta rikitar da shi ta riƙa sanya shi yin ƙabali da ba'adi a cikin sallarsa. Kuma koda yaushe zai kasance cikin tunani da jin tsoron abin da zai biyo baya a duk lokacin da ya shiga gidansa.


4. Kada ka kula yarinyar mutane inba aurar ta za ka yi ba. Ka ji tsoron Allah ka daina hure wa  ƴaƴan mutane kunne kana aikata alfasha da su. Shin za ka so a yi wa ƴarka ko wata ƴar uwarka irin abin da kake yi wa ƴaƴan wasu na rashin ɗa'a, ko dai ƴaƴanka da ƴan uwanka sun fi na kowa ne?


5. Ya fi maka alheri a ɗauki abu mafi tsini a riƙa kafa maka shi a tsakiyar kanka har ya ƙule a kan ka sami yaran mutane (mata) kana shafa su, abin nufi a nan haramun ne ka taɓa jikin macen da ba taka ba. Yi ƙoƙari ka yi aure domin ka samu abin da kake so wanda shari'a ta halatta maka shi daga ƴa mace.


6. Idan ka je hira kada ka taɓa jikin budurwarka, baiko ko sanya ranar aure ba aure ba ne kuma ba su ba ne suke ba wa saurayi da budurwa damar taɓa sashen jikinsu. Matasa da yawa sun hurewa ƴan matansu kunne da wasu ƙarairayi na banza har suka yarda suka amintar musu da jikkunansu suna yin lalata da su. Don Allah ka nisanta kanka daga wannan ɗanyen aikin da ire-irensa, kai koda mace ta amintar maka da kanta kada ka biye mata, ka yi ma ta nasiha tare da nuna mata munin abin da take kiran ka gare shi.


7. Kada a haɗa kai da kai cikin aikata zina da sauran manyan laifuka. Ya kai ɗan uwana mai albarka! Ka nisanci ƴaƴan banza, akwai macen da kwata-kwata bai kamata ka je wajenta da sunan neman aure ba, saboda ana ganin ka da ita za a kira ka da sunan fasiƙi, duba da shahararta a cikin fasiƙai.


8. Idan ka biye wa kyau ko dukiya ka jefar da mai addini za ka yi nadama mai yawa wacce ba za ta amfane ka da komai ba a rayuwarka.


9. Ka zaɓarwa yaranka uwa ta gari, ba maslaharka kanka kaɗai za ka duba cikin neman aurenka ba, zabar mace ta gari zai taimaka wa yaranka da sauran al'umma.


10. Kada ka keɓe da kowace mace idan ba muharramarka ba, idan kuma ka ƙi ji shaiɗan ne zai zama na ukunku. Shin ko ka taɓa ganin shaiɗan ya bar mace da namiji masu fama da sha'awa sun keɓe su kaɗai ba tare da ya tura jakadunsa ko ma shi ya je da kansa ba?


11. Ya kai ɗan uwana mai albarka! Ka girmama manyanka, ka kyautata musu kuma ka riƙa yi musu kyaututtuka daidai gwargwado. Da zarar ka ga wanda yake gaba da kai (babban mutum ko dattijo) ya taho da kaya ka karɓa ka kai masa gidansa. Idan kuma a kan abin hawansa zai ɗora ka karɓa ka ɗora masa.


12. Ka tausaya wa na ƙasa da kai, ban da hantarar sa da zagin sa don ya yi maka abin da ya ɓata maka rai.


13. Ka mu'amalanci mutane da mu'amala mai kyau. Kada ka yarda a yi kuka da kai a duk lokacin da wata mu'amala ta haɗa ka da wasu mutane. Yanzu za ka tsaya kana zagi da cin mutuncin mutane a bayan idanunsu da lokacin da suke nan bayan ka san hakan haramun ne ko kuwa ka fi son su yi murna da mutuwarka in aka labarta musu ita? A'a, to ka nisanci ɓatawa mutane suna, kuma kada ka yi wa waninka abin da kai kanka ba za ka so a yi maka shi ba.


14. Ka nemi sana'a ka bar dabar shan-inuwa. Ya fi maka alheri ka ɗauki igiya ka tafi daji ka yo itace ka sayar ka ci abinci a kan ka roƙi mutane koda za su ba ka ko su hana ka. Kai madalla da mai neman na kansa, shi ne wanda ba ya raina abin da zai samu a sana'a komai ƙasƙancinta kamar yadda wasu suke faɗi, ai ƙasƙantacciyar sana'a ita ce maula da roƙo. Duk wanda ya sha wahala ya nemi kuɗi ya sayi abinci ya ci ko ya ciyar da iyalinsa sadaka ne gare shi, ribar ƙafa ke nan, ga sauke nauyi ga kuma lada daga Ubangijinsa.


15. Kada ka raina sana'a komai ƙankantarta, abin da ba ka sani ba da yawa daga cikin manyan ƴan kasuwa sun fara ne daga kan ƙananan sana'o'i har Allah ya sa suka mallaki manyan masana'antu da kamfanonin da kake gani kana sha'awar zama kamarsu, kai ma ta shi ka nemi naka, Allah ne mai bayarwa, shi kaɗai ne zai iya ba ka ba wani mutum irinka ba.


16. Kada ka riƙa zagi ko kuka da mai gidanka a bayan idonsa, kai ko da baya sallamarka da abu mai tsoka ka yi haƙuri ka koyi abin da yake koya maka na yadda za ka iya sana'a iri kaza da kaza, watarana sai labari.


17. Gwara ka yi tallar ruwa a cikin kasuwanni, tura baro, ɗaukar kaya aka da tallar muruci a kan ka zama gwani a dabar shan-inuwa. Zaman banza bala'i ne, shi ke sanya ma'abotansa sanya idanu a kan abin da Allah ya ba wa wasunsu har su riƙa ganin kamar Allah ba ya son su ne shi ya sa ya hana su.


18. Kada ka zagi ɗan uwanka musulmi; musulmi ɗan uwan musulmi ne, ba zai zage shi ba haka kuma ba zai yi abin da zai cutar da shi ba. Kada ka rama zagin da wani mutum ya yi maka. Mai zagin iyayensa ba zai shiga Aljannah ba, to ta yaya mutum zai zagi iyayensa? Ta hanyar rama irin zagin da ɗan uwansa ya yi masa, abin nufi anan zage-zage da jifar juna ba tarbiyyar musulunci  ba ce.


19. Ka riƙa cika alkawari: Cika alƙawari ɗaya ne daga cikin siffofin mutane nagari, tauye shi kuma ɗaya ne daga cikin siffofin munafukai. Shin kana so ka siffantu da siffar munafukai? A'a. Ba ka so ko? E, to ka riƙa cika alƙawari.


20. Ka zama mutum mai taimakawa al'umma a duk halin da kake ciki na akwai ko babu. Kada ka ce sai ka zama mai kuɗi kamar wane sannan za ka riƙa taimakawa. Taimako ba ya kaɗan, ka bayar da abin da Allah ya hore maka a duk lokacin da aka nemi taimakonka.


21. Idan ka bayar da biyar Allah zai ba ka gomanta, idan kuma kana tantama a kan haka sai ka gwada ka gani. Duk wani mai bayar da abin da Allah ya ba shi na dukiya ci-gaba ne ke ƙara zuwa masa daga wajen Ubangijinsa, haka kuma hanyoyin samunsa ƙaruwa suke yi a kowane lokaci.


22. Idan wani ya bijiro maka da buƙatarsa ka biya masa ita ko ka taya shi biyan ta. Kada ka gaya masa maganar da za ta ɓata masa rai. Magana mai daɗi sadaka ce. Yayin da wani ya zo maka da buƙatar ₦10 a lokacin ₦15 ce a aljihunka, ka biya masa buƙatarsa sai Allah ya biya maka taka.


23. Ka riƙa biyan bashin da ake bin ka a kan lokaci, kada ka yarda mutane su riƙa kuka da kai a kan ƙin biyan su bashi da wuri. Bashi bala'i ne, yana hana kwanciyar kabari, yanzu mutane sun mayar da cinye kuɗin mutane ba abakin komai ba, malamai da ɗaliban ilmi ma sun faɗa cikin wannan bala'in sai wanda Allah ya tsare.


24. Ka yi wa masu aikata laifi kyakkyawan wa'azi da gargaɗi cikin hikima da fasaha ko Allah zai sa su gane munin abin da suke yi su tuba su zama mutane nagari. Ka kyautata harshenka a duk lokacin da kake yi wa mutane nasiha ko kake yi musu gargaɗi a kan wasu halaye nasu marasa kyawu. Fir'auna ma Allah ya ce a faɗa masa zance mai taushi ballantana ɗan uwanka musulmi.


25. Ka zaɓi mutane nagari su zama abokanka. Kada ka yarda ka yi abota da mutanen banza.  Duk wani aboki yana kiran abokinsa ne zuwa ga abin da yake kansa, in na banza ne sai shi ma ya zama na banza, idan kuma nagari ne sai shi ma ya zama nagari.


26. Kada ka riƙa yin askin nan da ake ɗebe wani sashe ana barin waninsa, abin da nake nufi anan askin banza da gayun nan marasa tarbiyya suke yi, idan ka yi za a kalle ka kamar su ne komai kyawun ɗabi'unka da halayenka.


27. Kada ka riƙa yin yawon banza ko yin wasanni na gaira ba dalili alhanin ga abubuwa nan masu muhimmanci da suka dace da kai, kamar neman ilimi da koyar da shi, aikata abin da al'umma za su amfana da shi da taya iyaye ayyuka.


28. Ka riƙa yin salloli guda biyar a cikin jam'i. Kada ka yarda a yi sallah a masallacinku ba tare da kai ba, da yawa daga cikin  malamai sun tafi a kan cewa sallar jam'i wajibi ce.


29. Kada ka biye wa shafukan sada zumunta idan kuma ba haka ba za ta kautar da kai ga barin bautawa Allah da ambatonsa. Idan ka hau yanar gizo ka yi abin da zai amfane ka, ya kuma amfanar da ƴan uwanka musulmai, idan kuma ka sauka ka yi abin da zai amfane ka da sauran ƴan uwanka musulmai. Kada ka yarda ka yi asara koda daidai da minti ɗaya ne a banza.


30. Ka bar duk abin da kake yi idan ka ji kiran sallah, sannan ka faɗi kwatankwacin abin da mai kiran sallar yake faɗa, idan ya ce "Hayya alas sallah da Hayya alal falah" ka ce "Lahaula wa laƙuwwata illa billa".


31. Idan za ka yi zance ka yi adalci, ka kiyayi yin ƙarya da shaidar zur, wato yin shaida a kan abin da ba ka ji ba, ba ka gani ba.


32. Ka koyi karatun Alƙur'ani da sanin saƙonnin da yake ɗauke da su a wajen ma'abotansa, sannan kai ma ka koyar da ƴan uwanka abin da ka koya na alƙur'anin.


33. Ka sabarwa kanka da karanta Alƙur'ani, kuma idan damuwa, ƙunci da baƙin ciki suka dabaibaye ka ka ɗauki Alƙur'ani ka karanta ko ka yi tilawar abin da Allah ya hore maka. Duk lokacin da ka karanta Alƙur'ani za ka ji daɗi, nutsuwa, farin ciki da nishadi sun dabaibaye ka, ƙarshe ma sai ka rasa abin da yake damunka na damuwa gabanin karanta shi.


34. Ka nemi ilimi ba don jayayya da ce-ce-ku-ce da mutane ba, sannan ka koyar da shi.


35. Kada ka riƙa ganin kowanne irin mutum bai san abin da yake yi ba ko a matsayin jahili saboda kai ka yi karatun da bai yi ba.


36. Ka riƙa yi wa Annabi (S.A.W) salati a kowace rana. Ga salati nan wanda Manzon Allah (S.A.W) ya koyar a cikin littafan musulunci, idan ba ka iya ba ka dage ka koya ka riƙa yi. Mafi ƙaranci adadin salatin da za ka yi wa Annabi (S.A.W) goma da safiya, goma da yamma a kowace rana.


37. Son samu ka riƙa karanta shafi biyu na Alkur'ani a duk bayan sallar farilla guda biyar, idan ka saba yin haka za ka sauke Alƙur'ani a cikin wata ɗaya.


38. Ka riƙa ciyar da marayu kana shafa kansu, da ɗaukar nauyin ababen more rayuwarsu har su manta ma da cewa su marayun ne, sannan ka sanya su a makarantu irin waɗanda ka sanya ƴaƴanka ko makamantansu.


39. Ka riƙa ragewa ɗalibai hanya ko biya musu kuɗin babur, mota ko a daidaita sahu a lokacin da za su tafi makaranta.


40. Ka riƙa biya wa ɗalibai kuɗin littafai da na makaranta idan Allah ya ba ka iko. Idan ɗalibi ya nemi taimakonka ka taimaka masa. Wani lokacin kuɗin handout ma gagarar wasu ɗaliban yake yi, ya kamata ka sanya hannun jarinka cikin taimakawa ire-iren waɗannan ɗaliban.


41. Mai saɓa wa iyayensa ba zai shiga Aljannah ba. Da wannan nake ba ka shawarar tsayawa ka yi wa iyayenka biyayya a kan duk abin da suka umurce ka matuƙar ba na saɓon Allah ba ne da barin abin da suka hane ka inba na bin umarnin Allah ba ne. Dama iyaye nagari ba za su sanya ɗansu ya aikata saɓon Allah ba, haka kuma ba za su hana shi yi wa Allah biyayya ba.


DUBA WANNAN YANZU: Nagartattun Nasihohi 30 Ga 'Yar Uwata Musulma


42. Ka riƙa bibiyar littafanka waɗanda kake zuwa ana karanta maka a zaure, majalissa da waɗanda ake koyar da kai a makarantun zamani.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user