Friday 7 January 2022

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (44) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

KA FARA SANA'A NE?


Idan ka fara me ya sa kake son canja wa? Ko kuwa kana son farawa ɗin ne amma kana ta tantamar sana'ar da za ka yi ka samu abinda kake so? Duk wani da kake ganin kamar ya ci nasara a rayuwarsa da haka ya fara har ya kai inda yake a yau, amma ga wasu 'yan shawarwari da zan ba ka tabbas za su taimaka sosai, koda kuwa mata ne masu sana'a a cikin gida. Akwai waɗanda sukan fara da ƙaramin abu har su ƙasaita su zama manya. Akwai ƙananan yara da ba su wuce zuwa makaranta ba, wasu sukan saki karatun aji su koma na sana'a kuma Allah ya haskaka musu ka ga sun zama masu ruwa-da-tsaki a harkar kasuwanci, yana da kyau a haɗa biyun dai.


Shin ka fara yin sana'a ko kuwa...
Hoto: Getty Images


MarubuciBaban Manar Alkasim


1) Kafin ka fara tunanin me kake so ka sayar fara tantance wa tukun, wani irin mutum kake so ka zama, babban ɗan kasuwa mai kuɗi da dama? Idan haka ne zaɓo nau'in sana'ar da za ta iya kaika inda kake son zuwa? Kusanci masu yinta fara neman sanin makaman yadda ake gudanar da ita, tsaya wurin sanin komai nata, ka ɗauke ta kamar taka, idan kana da wurin da ba ka son bari kuma anan za ka gudanar da sana'arka to dole ka zaɓi abinda ya dace da mutanen wurin, idan kuwa sana'ar da kake so ta fi maka komai to ka koyo ta. Idan ya so, daga baya ka karanci inda za ta dace a gudanar da ita.


1) Janyo mabuƙata jiki ta kowace fuska kuwa: Ka san ba a san ka ba, ba zai yuwu a san ka ba kuma sai ka ɗan bambanta da saura, yanzu ta wani fanni za ka ɓullo, kana da abinda sauran ba su da shi ne na janyo hankalin mabuƙata? Za ka ɗan rage kuɗin naka ne kaɗan ko za ka ɗan ƙara yawan kayan ne? In kuma sana'ar hannu ce to duba, za ka riƙa yin aiki cikin gaggawa ne ko za ka ɗan sauƙaƙa kuɗin da za a biya ne? Ka nemi duk abinda zai matso da mabuƙata kusa, abinda za ka guje wa shi ne kar ka taɓa yarda da abinda zai haɗa ka faɗa da su, in kaya ya lalace kar ka sayar musu, in har sun na ce za su saya to ka gaya musu aibin da ke cikin kayan.


Idan ba haka ba 'yar ribar da za ka samu ko jin daɗin rabuwan da za ka yi da kayan na rana guda ne, amma wannan mabuƙacin ka rabu da shi kenan har abada, don ba zai komo ba. Wani ya taɓa gaya min cewa mahaucin da yake sayen nama a wurinsa ya sayar masa da ruɓaɓɓen nama da saninsa, tun ranar ya rabu da shi. Wani kuma ya ce mai sayar masa da gwanjo ta sayar masa na ₦800 akan dubu ɗaya da ɗari biyar guda 10, tun ranar ya rabu da ita har lokacin da yake ba ni labarin, na ce da sun yi haƙuri tabbas da sun riƙe mabuƙatansu. Wani ya rabu da telansa a dalilin ɓata lokacin da ya yi masa a ɗunki. Wata ta ce kafinta da ta ba shi aiki har yanzu ya ƙi yi kuma ya cinye kuɗin, kuma aikin ƙarami ne matuƙa, duk waɗannan sun kori mabuƙatansu kai-tsaye.


Me ƙaramar sana'a kar ya yarda ya yi abinda zai kori mabuƙacinsa da shi, ya yi masa yadda kullum zai dawo. Misali wanda nake sayayya a shagosa ya ce a kan sari zai riƙa ba ni kaya, abin ₦350 yana sayar min akan ₦325, gaskiya ina jin daɗi, wani kuma ko ban da kuɗi zan iya ɗaukar kaya a shagonsa, don ina biya a kan kari ya san ni. 


Akwai wanda in dai na kawo masa kayana nan take zai yi min abinda nake so ya ba ni koda kuwa akwai jama'a a gabansa, kwanaki na sayi buredi mai shagon da kansa ya ce kar na ɗauki wannan, ni mabuƙacin kayansa ne ba zai bari ƙaramin abu ya haɗa mu ba, duk waɗannan ba zan iya rabuwa da su ba, bare mai sayar min da kayan wuta, ko baida shi ba zai bari na saya a wurin wani ba sai dai ya je ya kawo min da kansa.


2) Talla: Akwai wanda yakan fara talla tun bai fara sayar da kayan ba ma, ba laifi ka koɗa kayanka, amma ka tabbatar abida ka faɗa game da kayannan akwai shi, in ba haka ba duk lokacin da mabuƙaci ya saya zai yi zaton ka cuce shi ne ba zai dawo ba, akwai nau'o'in sana'ar da wasu ƙalilan a cikinsu ba su damu da ƙarya ba a wurin tallan, kamar dai masu sayar da magungunan gargajiya, wani zai ce maka sha-yanzu-magani-yanzu, wani ya lissafa maka cututtuka ɗari ba ɗaya ya ce maganinsa ɗaya ne a wurinsa, kuma a 'yan kuɗi ƙalilan, in mutum ya saya kuma bai ga abinda ka faɗa ba to shi ma ba zai bari wani mutum ɗin ya saya ba, dole mabuƙatanka su guje ka, duk wanda zai fara sana'a ya tabbatar duk abinda ya faɗa game da kayansa haka yake, musamman irin ci-gaban da aka samu yanzu na talla a wayar salula. Sau da yawa mutum kan sayi abu ya ga wani abin daban.


Yana da kyau ka fito da duk abinda mutane ba su sani ba na kyawun kayanka amma kar ka ƙara da ƙarya, ban ce ka faɗi aibin kayanka in za a saya ba, amma in mutum  ya san me zai saya ko ya sami matsala a cikinsa ya san ba ka cuce shi ba gobe zai dawo, kamar ƙananan 'yan kasuwa zuwa manya suna da hanyoyi masu yawa na tallata kayansu kamar kafofin sada zumunci, yanar gizo da ake saka liƙau, kafofin sadarwa na zamani, yanzu har a fina-finai ana tallan kaya, wasu hanyoyin da ba a gama ganewa ba sun haɗa da tallafi wanda yake ɗauke da tambarin kasuwanci ko wasu kyaututtuka, akwai su amma kamfanoni ke yi.


Kamar mata masu kayan ƙamshin girki da su turaren wuta ko na Humra da dilka in dai sun gyara kayan sana'arsu to su yi ƙoƙari su yi liƙau wanda za a riƙa mannawa a jikin kayan, kamar a ce 'Husna spices' ko 'Husna beauty' da dai sauransu, ga lambar wayanan yadda za a sami sauƙin samunki, in dai a karon farko an yi haƙuri da ƙaramar riba tabbas za a samu da yawa anan gaba. 


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (45) Cikin Sauki


Yanzu dai matakin farawa ne, tunaninmu ba me za mu samu ba ne, ya za a san mu a ko'ina ne kuma a zo neman kayanmu??


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user