Monday 10 October 2022

Ire-iren Mutanen Da Suke Da Matsala A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa

Ka guji nau'in mutanen nan, suna da hatsari a rayuwarka;


1. Mutum na farko masoyi a idonka, amma a bayan idonka maƙiyi ne, fuskar da ba ka san shi da ita ba ita ce asalin fuskar shi, fuskar da yake nuna maka makami ne da yake yaƙarka da shi.


Mutane masu hatsari
Hoto: Forbes

Marubuci: Yahaya S. Kaya


2. Ka guji wanda komai ka yi yake ɗauka kuskure ne, ko da ka yi daidai ba ya faɗa, shi kullum ba ka iya ba ne a wajen shi. Irin waɗannan mutanen suna da hatsari a yi mu'amala da su, saboda suna kashe burin mutum, saboda su ba za su ƙarfafa ma mutum akan burikanshi masu muhimmanci, tabbas illarsu tafi ta guba, saboda ita guba lokaci ɗaya take yin kisa, su kuma tsawon lokaci suke ɗauka domin su rusa ma mutum rayuwa.


3. Duk wanda zai dinga haɗaka faɗa da 'yan uwanka na jini, ko idan kun yi faɗa da su ya dinga zugaka akan ka yi rashin mutumci, lallai wannan yana son duniya ta  zage ka, su ce 'yan uwanka ma ba ka ƙyale ba wa zaka ƙyale. Ka guji irin waɗannan mutanen bom suke so su tayar a rayuwarka, wanda zai rusa martabarka.


4.  Duk wanda ba zai girmama ka ba, ba zai girmama ra'ayinka ba, ba zai tausasa maka murya ba, yana kallonka a wulaƙance, a tunanin shi ya fi ka matsayi ko kuɗi ko sarauta, ka nisanta da shi, idan ba haka ba zai mayar da kai bawa kuma ƙasƙantacce.


5. Ka guji mutanen da za su yaɗa sharrinka bisa ƙaramin saɓani, sannan za su tuna da kuskuren da ka taɓa musu ko da a baya sun yafe, za su ɓataka a wajen mutanen da suke ganinka da kima, su nuna musu kai ba nagari ba ne, su maka ƙage, su saka kokwanto a zuciyar waɗanda suka amince maka.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user