Thursday 3 November 2022

Manyan Dalilai 7 Da Suke Hana Mutane Masu Aiki Tukuru Samun Nasarori A Rayuwar Su

Tura Wannan Zuwa

Na tsawon lokaci, na yi tunanin cewa idan mutane masu ilimi suka yi aiki tuƙuru, sannan suka girma a wajen da zai ba su damarmaki, to nasarar rayuwa za ta zo ta riske su. Sai na kalli mutum na ce “wancen zai zama wani abu a rayuwa.”


DALILAN DA SUKA SANYA MUTANE MASU AIKI TUƘURU BA SA SAMUN NASARORI A RAYUWA
Hoto: Medical News Today


MarubuciBello Galadanchi


Amma yanzu da nake ƙara girma, na gane cewa hakan ba lallai gaskiya ba ne. Akwai mutane da na sani waɗanda suna da ilimi da basira, kuma suna aiki tuƙuru sannan sun taka rawar gani sosai, sannan kuma akwai waɗanda ga su nan ne kawai. Abin takaici kuma shi ne, akwai wasu waɗanda sai a hankali, ba su san me za su yi a rayuwar su ba. 


Daga nan na fahimci cewa akwai abubuwa da yawa da ake buƙata domin samun nasara a rayuwa, kamar bunƙasa a wajen aiki, ko zaman aure, ko zama cikin ƙoshin lafiya. Ilimi na daga ciki da aiki tuƙuru.


Bello Galadanchi yayin gaisawa da wani Ɗan ƙasar Sin
Hoto: Bello Galadanchi


Amma akwai wasu abubuwa da dama waɗanda muke tsallakewa. 


Ga dalilai bakwai da suka sa wata ƙila ka gaza samun nasara a rayuwa duk da cewa kana da basira kuma kana aiki tuƙuru.


1. BA KA ƘULLA DANGANTAKA DA SABABBIN MUTANE


Akwai sauƙi sosai wajen liƙewa da mutanen da ka sani na lokaci mai tsawo. Kun san tarihin juna, za ku iya yin dariya da barkwanci da juna. Matsalar tsofaffin abokai shi ne, akwai shawarwarin da za ku yi ta juyawa kullum, hakan zai sa ba za ku ringa samun sababbin shawarwari ba daga wasu mutanen waɗanda ba ku sani ba. 


BELLO GALADANCHI
Hoto: Bello Galadanchi


Yunƙurin sanin sababbin mutane zai iya yin wahala, amma za a iya farawa a hankali. Yi ƙoƙarin sanin koda mutum ɗaya ne a mako ɗaya. 


2. KANA ADAWA DA SAUYI


Zama waje ɗaya tsautsayi inji kifi, kuma akwai wahala sosai wajen sabawa da sabon abu idan ka daɗe a waje ɗaya kana abu ɗaya. Amma abin albishir a nan shi ne sauyi na kawo damarmaki da ƙirƙire-ƙirƙire. 


A maimakon yin adawa da sauyi, yi nazarin yadda za ka yi aiki da wannan sauyi. Wata ƙila ka ƙirƙiri sabuwar sana’a ganin irin sababbin buƙatun jama’a da wannan sauyi ya kawo. 


Bello Galadanchi cikin kyakkyawar shiga
Hoto: Bello Galadanchi


Ka buɗe zuciyar ka ga sababbin dabaru kuma ka zama mai ƙoƙarin sanin duniyar dake zagaye da kai. 


3. KANA TSORON ƊAUKAR KASADA


Yawancin mutane masu basira sun fi son gujewa kasada, da tsayawa akan turbar da ta fi kwanciyar hankali. Za su iya kwaikwayar abokan su, ko su zaɓi aiki ko sana’ar abokansu saboda shi ne suke ganin jama’ar da ke kewaye da su za su amince. 


Duk da cewa wannan tsari na tabbatar da kwanciyar hankali, zai iya gundurar mutum. Sau da yawa nakan ji labarin cewa mutane masu basira na ƙorafin cewa aikin su ba ya gamsar da su, kuma suna so su yi wani abun na daban, amma suna tsoro. 


Bello Galadanchi cikin shigar Hausawa
Hoto: Bello Galadanchi


Idan kana tunanin hawa wata sabuwar alƙibla da ba ka sani ba, yi tunanin ko ya rayuwar ka za ta kasance a shekaru goma ko ashirin daga yanzu idan har ka yanke shawarar cewa ba za ka gwada sabon abu ba. Shin za ka yi nadama, ko kuma za ka yi farin ciki da wannan shawara da ka yanke?


4. KA YI IMANIN CEWA YA KAMATA KA YI NASARA SABODA TAKARDUNKA


Mutanen da suka yi aiki tuƙuru a makaranta yawanci su ne a saman aji, kuma ana gaya musu yadda ake musu kyakkyawan zato na samun nasara a rayuwa. Wannan abu ne mai kyau, amma yana da na shi koma bayan. 


Na ji mutane suna cewa ya kamata su samu wani abu saboda basirar su, ko saboda makarantar da suka je. Suna zaton cewa komai zai zo ya same su saboda takardunsu na makaranta. Abin takaicin shi ne, ba haka rayuwa take ba. 


A wannan duniyar, ba ka samun nasara saboda aikin da ka yi. Kana samun nasara ne saboda abubuwa da dama kamar aiki tuƙuru, tunani a dabarance, da kuma sa’a. 


5. KANA YAWAN BIYE WA ABIN DA KE ƘAYATARWA A WANNAN LOKACI


Ɗaya daga cikin abubuwan da nake ji daga bakin mutanen da suka yi nasara shi ne sun tsani ɓata lokaci. Mutane masu basira sun san darajar lokacin su, saboda idan suka sa lokacin su da tunanin su a waje ɗaya, hakan na nufin akwai wata dama can daban da take wuce su. 


Bello Galadanchi tare da ɗaliban makarantarsa
Hoto: Bello Galadanchi


To wannan abu ne mai kyau, amma kuma hakan na nufin ko yaushe kana bin abin da ake yayi, ko yake tashe. Fara kowanne irin abu a kowani ɓangare na rayuwa na da wahala, sannan wuce ƙalubalen farko na buƙatar haƙuri. 


Mayar da hankalin ka da ƙwazon ka akan buri guda ɗaya ya fi kawo sakamako mai kyau a lokaci mai tsawo, idan aka kwatanta da yau kana nan, gobe kana can, kullum kana bin wani sabon abu. 


6. BA ZA KA IYA YANKE SHAWARA BA


Kasancewa mutum mai basira da aiki tuƙuru zai iya buɗe maka damarmaki masu yawa. Amma abin takaicin shi ne, damarmaki masu yawa na iya zama takunkumi kamar damarmaki ‘yan kaɗan. 


Samun damarmaki da yawa na kawo ƙalubale wajen yanke shawarar abin da mutum yake so ya yi. Saboda haka, sai ka ga mutum na sha’awar ya yi tsalle ya je nan, ya dawo ya gwada wancan domin ganin ko mene ne ya fi dacewa da shi. Na san wanda ya yi digiri na biyu har guda huɗu, ga shi yanzu shekaru goma amma bai san me yake so ya yi ba. 


A maimakon ka yi ta ruwan ido kana kallon damarmaki da yawa da ke gaban ka, ina bada shawarar ka gwada abubuwa tukunna. Yi magana da wasu mutanen sannan ka yi bincike kafin ka yanke babbar shawara, ta yadda za ka sani ko abin da ka zaɓa ya fi dacewa da kai, da tunanin ka, da tsarin tafiyar da rayuwar ka. 


7. BA KA YARDA DA KANKA BA


Abin mamaki shi ne akwai mutane masu basira da suka raina baiwar da Allah Ya ba su. Sun fi kowa sukar kawunan su da adawa da kansu, lamarin da yake saka su suke gani kamar ba za su iya cim ma burin da za su iya cimma wa ba. 


Mutane masu basira na so su ga abu ya yi sosai musamman a aikin su. Duk lokacin da suka yi aiki, suna sukar aikin sosai kuma har ma su ringa kokwanto


Wannan kamar abu ne mai kyau, amma illarsa ta fi yawa. Don haka, a ga abu ya yi kyau zuwa ƙarshe na iya ƙalubalantar mutane wajen samun ci gaba a rayuwa, ko ma su fara abu daga farko. 


Saboda haka a maimakon ƙyale fargabar “idan na yi kaza fa” ko kuma “gaskiya wannan ya fi ƙarfi na” ya hana ka gwada wani sabon abu, yi tunanin yadda rayuwar ka za ta kasance a shekaru masu zuwa. 


Farawa ya fi zaman jiran abu ya zo ya riske ka. 


Me za ka yi domin ƙara kusantar samun nasara a rayuwa? Waɗanne irin abubuwa ne suke riƙe ka, suke hana ka cim ma burin ka? Rubuta.


Game da Bello Galadanchi


Bello Galadanchi yayin kammala karatun jami'a
Hoto: Bello Galadanchi


Dr. Bello Galadanchi  ƙwararre ne a koyar da kasuwanci da harshen Chinese. Ya yi karatun Firamari a Al-Iman School Jos, da Sakandari a Ulul Albab Science Secondary School Katsina, da kuma digrin farko a Jami’ar Pennsylvania dake Amurka. Ya yi karatun MBA da PhD a China, sannan ya ƙirƙiri Kasuwar Bello. Bello Galadanchi ya yi aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), kuma yanzu haka yana binciken kimiyyar ilimi a ƙasar Sin.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user