Saturday 20 May 2023

Hanyoyi 7 Domin Samun Nasara A Kasuwanci

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan ka yi ƙoƙarin binciken hallayar ‘yan kasuwa masu nasara akan shafukan yanar gizo, sau da yawa za ka ga sunayen mutane kamar shahararrun mutanen da suka ƙirƙiri na’ura mai ƙwaƙwalwa kamar Steve Jobs ko Bill Gates.


Nasara A Kasuwanci
Hoto: Big Stock


MarubuciBello Galadanchi


Sau da yawa mutane suka ambaci sunayen waɗannan mutane a duk lokacin da aka yi maganar ƙwararrun ‘yan Kasuwa waɗanda suka girgiza duniya da basirar kasuwancin su. 


Suna matuƙar harzuƙawa, wani lokacin har da saka jama’a fargaba. To idan Allah bai ba ka fasahar Steve Jobs ba ko jajircewar Bill Gates ba, kar ka tayar da hankalin ka. Ina da albishir. Za’a iya nunawa ‘yan kasuwa hanyoyin samun nasara ta horar da su akan ɗabi’u masu muhimmanci. 


Manazarta, da ƙwararru a harkokin kasuwanci sun bayyana cewa shahararrun ‘yan kasuwa za su iya ɓullowa daga duka ɓangarorin rayuwa a kowani lokaci, kuma Allah Ya yi su da halayya iri-iri kuma ba sai suna da ilimin boko ba. 


Saɓanin hikima, ba dole sai ka zama mai nasara a komai na rayuwa ba, ko kana da nutsuwa ta musamman, ko ka kasance mai aiki babu dare babu rana sannan za ka iya samun nasara a kasuwanci. Maganar gaskiya, irin waɗannan mutanen ba sa iya ɗaukar kasadar da shahararrun ‘yan kasuwa ke ɗauka, kuma masu nazari sun bayyana cewa mafi yawancin lokuta, ɗaliban da ke samun C a jarrabawa su ne suke zama shahararrun ‘Yan Kasuwa. 


Sai dai kuma ƙwararrun ‘yan kasuwa suna da ɗabi’u kusan iri ɗaya, daga jajircewa zuwa kasada waɗanda suna daga cikin gimshiƙin samun nasara a kasuwanci.


Nazarin da masu bincike suka yi ya nuna cewa shahararrun ‘yan kasuwa suna da ɗabi’u daban daga manajojin kamfani, ta inda suka yi musu fintinkau a ɓangarori kamar sauraron ra’ayoyi domin ƙarin ilimi da ƙirkire-ƙirƙire, da kuma iya horar da kawunan su, da ma ƙarfafa wa kawunan su gwiwa, sannan suna da sauƙin kai wanda hakan yana taimaka musu wajen jure wahala. 


Ga ɗabi’un guda bakwai, da bayanan su a taƙaice:


1. JURIYA: Juriya ne na farko, saboda mafi yawancin kasuwanci na samun ƙalubale wajen karyewa. Hakan yana faruwa sau da yawa a kowani mako.


2. ƘAUNAR KASUWANCI: Duka shahararrun ‘yan kasuwar da na sani sun yi imanin cewa za su bada nasu gudunmuwa ga jama’a. Wannan abu yana ƙayatar da su, shi yasa suke iya jurar duk wani ƙalubale da ke addabar su.


3. HANGEN NESA: Sau da yawa shahararrun ‘yan kasuwa na fuskantar jama’ar da ke yunƙurin kashe musu gwiwa saboda suna da hangen nesa, lamarin da ragowar jama’a ba su iyawa.


4. SAURARON RA’AYOYIN JAMA’A: Wannan yana nufin samun nasara wajen jurewa fargaba. Fargabar jin kunya, da rashin samun albashi, da karyewa da ma sauran batutuwa.


5. IMANI: Dolen dole sai ka yi imani da burin ka da niyyar ka. Dolen dole sai kana sha’awar yin ganganci amma kuma a dabarance.


6. IYA KWANA: Dolen dole sai kana da zuciyar gaya wa kanka cewa “gaskiya wannan abu da nake yi ba ya aiki, bari na canza alƙibla”.


7. KARYA DOKA: Shahararrun ‘yan kasuwa mutane ne dake ƙalubalantar hikimomin da aka gada tun iyaye da kakanni. Binciken manazarta ya nuna cewa shahararrun 'yan kasuwa sun ƙunshi “ilimi, zafin nama, ganganci da saɓawa yadda lamura ke gudana.”


Idan bacci kake ka tashi, idan a zaune kake ka miƙe, idan a tsaye kake, to ka fara tafiya, idan tafiya kake to ka ruga da gudu, idan gudu kake to ka tashi sama. Allah Ya bamu nasarar duniya da lahira Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user